Jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji 65 ya nutse a Indonesia

Asalin hoton, Bali Search and Rescue
Wani jirgin ruwa ɗauke da fasinjoji sittin da biyar ya nutse a kusa da tsibirin Bali na kasar Indonesiya.
Aƙalla mutane ashirin da uku ne aka ceto yayin da aka gano gawarwakin mutum hudu.
Jirgin na hanyar zuwa Bali ne daga Ketapang a Gabashin Java lokacin da ya nutse.
Jami'an tawagar aikin ceto sun bayyana cewa jirgin ya fuskanci matsalar inji gabannin nutsewarsa.
Rashin kyakyawan yanayi dai na kawo cikas a aikin ceton da ake gudanarwa


