Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba kan zargin almundahanr naira biliyan 27

    .

    Asalin hoton, DARIUS ISHAKU

    Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama tare da tsare tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku bisa zargin almundahanar kuɗi da yawansu ya kai naira biliyan 27.

    Jaridun Najeriya sun ruwiato cewa tsohon gwamnan zai fuskanci tuhume-tuhume 15 da suka haɗa da cin amana, ɓarnatar da kuɗi da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar da na ƙananan hukumomi.

    Laifukan da ake zargin tsohon gwamnan, an aikata su ne tsakanin 2015 zuwa 2021 lokacin da yake riƙe da matsayin gwamnan jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.

  2. Amurka ta nuna damuwa kan goyon bayan da China ke bai wa Rasha

    Shugabanni

    Asalin hoton, REUTERS/EPA

    Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya ce ya bayyana damuwar Amurka game da goyon bayan da Beijing ke bai wa Rasha a tattaunawar da ya yi da takwaransa Wang Yi na ƙasar China a gefen taron Majalisar Dinkin Duniya.

    Ya ce China tana ƙara rura wutar yaƙin ta ɓangare Rasha, inda ya yi barazanar ƙara ƙaƙaba mata takunkumai.

    Mista Blinken da Mista Wang sun kuma tattauna kan hanyoyin daƙile kwararar miyagun ƙwayoyi cikin Amurka, da haɗuran da ke tattare da ƙirƙirariyar basira ta AI da kuma abin da ya kira ayyukan da Beijing ke yi masu hatsari da tayar-da-zaune-tsaye a tekun kudancin ƙasar China.

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiya.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kawo muku irin wainar da ake toyawa a faɗin duniya.

    Kuna iya tafka muhawara kan labaran da muke wallafa wa a shafukanmu na sada zumunta.