Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 28/09/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. Hotuna: Martanin jama'a kan rasuwar Hassan Nasrallah

    Kisan da aka yi wa jagoran ƙungiyar Hezbollah ta kaɗa mutane da dama, musamman ma a yankin Gabas Ta Tsakiya.

    Ga wasu hotuna na irin martani da mutane suka yi.

  3. Martani daga ƙasashen duniya kan kisan Nasrallah

    Ba ya ga shugaba Biden, mun kuma samu martani daban-daban daga ƙasashen duniya kan mutuwar Hassan Nasrallah:

    • Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya ce ya damu matuka game da "barazanar yaɗuwar rikicin"
    • Sakataren harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya sake yin kira da a tsagaita wuta nan take
    • Shugaban Cuba Miguel Diaz-Canel ya yi Allah-wadai da kisan da aka yi wa Nasrallah.
    • Jagoran addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ayyana zaman makoki na kwanaki biyar, inda ya ɗau alwashin cewa mutuwar Nasrallah ba za ta tafi a banza ba
    • na zaman makoki na jama'a, yana mai shan alwashin cewa mutuwar Nasrallah ba za ta kai ga gaci ba
    • Ƙungiyar Tarayyar Turai ta shawarci kamfanonin jiragen sama da su dakatar da zirga-zirga a sararin samaniyar Lebanon da Isra'ila
  4. Palmer ya ci kwallo huɗu rigis a wasan da Chelsea ta doke Brighton

    Cole Palmer ya zama na farko da ya ci ƙwallo huɗu a Premier kan hutu, bayan da Chelsea ta doke Brighton 4-2 ranar Asabar a Stamford Bridge.

    Sun kara a wasan mako na shida, inda Palmer mai shekara 22 ya buga ƙwallo ya bugi turki, da wanda ya zura a raga aka ce an yi satar gida.

    Brighton ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Georginio Rutter a minti na bakwai da fara tamaula a babbar gasar tamaula ta Ingila.

    Daga baya Chelsea ta farke ta hannun Palmer, sannan ya kara na biyu a minti na bakwai tsakani, sannan ya ci na uku a bugun fenariti

    Haka kuma Palmer ya kara na huɗu a raga, bayan da Brighton ta zare na biyu ta hannun Carlos Baleba, wasan ya koma Chelsea 4-2 tun kan hutu.

  5. Jinin Nasrallah ba zai tafi a banza ba, Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta - Khamenei

    Jagoran addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya ce jinin jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah da Isra'ila ta kashe ba zai tafi a banza ba.

    Ya ce an ayyana zaman makoki na kwanaki biyar a faɗin ƙasar.

    Ya miƙa sakon ta'aziyyarsa ga iyalan jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah da aka kashe.

    Khamenei ya kuma jajantawa sauran ƙasashen Musulmi kan kisan na shugaban ƙungiyar.

    Ya ce an kashe Nasrallah ne a lokacin da ya ke shirin kare marasa galihu na yankunan kudancin birnin Beirut da kuma gidajensu da aka lalata, da kuma rayuka masu daraja da aka rasa.

    "Ba za mu gajiya ba, za mu mayar da martani mai zafi. Isra'ila za ta ɗanɗana kuɗarta," in ji Ayatollah.

    Jagoran addinin na Iran ya ce duk da cewa an yi rashin “fitaccen mutum mai iko” kuma Lebanon ta rasa “shugaba mara misaltuwa”, amma Hezbollah za ta ƙara karfi.

  6. An sake kashe wani babban jami'in Hezbollah - rahotanni

    An kashe wani babban jami'in sirrin ƙungiyar Hezbollah a wani hari da sojojin Isra'ila suka kai, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Sojojin Isra'ila sun ce sun kashe Hassan Khalil Yassin ranar Asabar a kudancin Beirut.

  7. Labarai da dumi-dumi, Kisan Nasrallah yana a matsayin ma'auni na adalci - Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya bayyana kisan Hassan Nasrallah a matsayin "ma'auni na adalci ga ɗimbin waɗanda aka kashe ta dalilinsa".

    Ya ce waɗannan mutane sun haɗa da "dubban Amurkawa da Isra'ilawa da kuma farar hula a Lebanon".

    Biden ya jaddada cewa Amurka tana goyon bayan Isra'ila ɗari bisa ɗari wajen kare kanta daga Hezbollah da Hamas da Houthis da kuma duk wata ƙungiyar ta'addanci da ke samun goyon bayan Iran.

    Shugaban na Amurka ya kuma ce ya umurci ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da ta ƙara karfin tsaron sojojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya domin daƙile ta'addanci.

  8. Kasurgumin ɗan Boko Haram ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya

    Rundunar dakarun ƙasashen da ke yaƙi da ƙungiyar Boko Haram ta MNJTF, ta ce wani kasurgumin ɗan Boko Haram, mai suna Bochu Abacha, ya miƙa wuya ga sojojin Najeriya da ke aiki a karamar hukumar Kukawa na jihar Borno.

    Jami'in yaɗa labarai na rundunar a Ndjamena, Laftanar Kanar Olaniyi Osaba ne ya bayyana haka ga manema labarai a Maidguri ranar Asabar.

    Osaba ya ce Abacha, wanda ya kasance yana da hannu a kai hare-hare da dama, ya amsa shiga gaba wajen kai hare-hare a kan hanyar Mongunu zuwa Baga.

    "Abacha ya miƙa wuya ne sakamakon zafafan farmaki da MNJTF ke kai wa da kuma buƙatarsa ta son ganin an samu zaman lafiya," in ji Osaba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

    Ya ce ɗan Boko Haram ɗin ya kuma miƙa bindiga AK 47 ɗaya cike da harsasai da wayar salula da layin wayar kamfanin Airtel da kuma kuɗi N32,500.

    Jami'in ya ce wanda ake zargin na bai wa hukumomi bayan sirri da zai taimaka musu a aiki.

    A ɗaya gefen, rundunar MNJTF tare da haɗin gwiwar wasu jami'ai sun yi wasu mayakan Boko Haram kwantan ɓauna tare da kashe ɗaya daga cikinsu.

    Dakarun sun yi artabu da mayakan, inda daga bisani wasu suka samu damar tserewa har da barin makamansu.

    Osaba ya ce sun gano motoci uku ɗauke da kayan abinci da sauransu.

  9. 'Da mu suka kashe, suka bar Nasrallah'

    BBC ta samu tattaunawa da mutanen da suka ɗaiɗaita sakamakon hare-haren Isra'ila a Beirut, inda da dama daga garin Ain al-Mraysseh mai makwabtaka da babban birnin, suka nuna kaɗuwa bayan jin labarin kisan jagoran Hezbollah Hassan Nasrallah.

    Wasu da dama sun ƙasa jure jin mummunar labarin.

    Wasu sun yanke jiki sun faɗi ƙasa, wasu na ta ihu, yayin da wasu kuma ke guduwa da kuma yin kuka ko ta ina.

    Wata mata ta faɗa cewa: "Ta yaya zan koma birnin Dahieh bayan na san cewa (Hassan Nasrallah) ba ya raye a yanzu".

    Kaɗuwar da mutane suka shiga ta kai girman gaske. Nasrallah ba jagora ne kaɗai ga ɗimbin magoya bayansa ba - ya kuma zama abin koyi.

    Ba kowane mutum ne ke goyon bayan Hezbollah a Beirut ba - amma a wasu tituna, mutane sun yi ta harbi a sama domin nuna ɓacin rai da kuma fushi.

  10. Hotuna: Yadda dubban mutane ke neman mafaka a Beirut bayan hare-haren Isra'ila

    Bayan hare-hare da Isra'ila ke kai wa birnin Beirut, dubban mutane ne ke tserewa domin neman mafaka.

    Hotuna da muke samu yanzu, na nuna mutane da dama na neman mafaka a wani dandali da ke cikin birnin, bayan tserewa daga kudancin Lebanon.

  11. Lebanon ta ce mutum 11 sun mutu a Beirut sakamakon hare-haren Isra'ila

    Bayani da muke samu daga ma'aikatar lafiya a Lebanon, ta ce aƙalla mutum 11 ne aka kashe ranar Juma'a sakamakon hare-hare ta sama da Isra'ila ta kai kudancin birnin Beirut.

    Jami'ai sun ƙara da cewa an kuma jikkata mutum 108.

    A ɗaya gefen, ma'akatar ta bayyana a ranar yau cewa ta samar da wani wuri domin lura da masu lalurar kansa - inda ta ce za a sauya musu wurin ne zuwa wasu sashe-sashe don lura da su yadda ya kamata.

  12. Hamas ta 'taya' Hezbollah alhinin mutuwar Nasrallah

    Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa, wadda ita da Hezbollah ke samun goyon bayan Iran, ta jajanta wa Hezbollah rasuwar jagoranta, Hassan Nasarallah.

    Cikin wata sanarwa da ƙungiyar da ke Gaza ta fitar, ta ce tana alhinin rasuwar shugaban na Hezbollah, sannan ta ce tana tare da 'yan ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon.

    Yayin da aka kwashe tsawon gomman shekaru ana yaƙi tsakanin Isra'ila da Hezbollah, na baya-bayan na ya faru ne bayan harin da Hamas ta ƙaddamar cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban bara, tare da kisan kusan mutum 1,200.

    Faɗa tsakanin Hezbollah da Isra'ila ya fara ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2023, kwana guda bayan harin na Hamas.

    Hezbollah ta riƙa harba rokoki zuwa cikin Isra'ila domin nuna goyon bayanta ga Falasɗinawa, kuma ta alƙawarta ci gaba da hakan, har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.

  13. Da Hezbollah muke yaƙi ba da mutanen Lebanon ba - Sojojin Isra'ila

    Kakakin rundunar sojin Isra'ila (IDF) Daniel hagari ya ce ƙasarsa da ƙungiyar take yaƙi ba da al'ummar Lebanon ba.

    Yayin da yake jawabi ta gidan talbijin na ƙasar, jim kaɗan bayan da ƙungiyar Hezbolla ta tabbatar da mutuwar jagoranta Hassan Nasarallah.

    Ga wasu daga cikin batutuwan da ya taɓo a lokacin jawabin nasa.

    • Hagari ya bayyana Nasrallah da cewa "yana cikin manyan maƙiyan Isra'ila"
    • Ya ce an kashe Nasrallah a wani "shiryayyen" hari da sojojin saman Isra'ila suka ƙaddamar a birnin Beirut ranar Juma'a.
    • Yanzu haka sojojin Isra'ila na kai hare-hare kan gine-ginen Hezbollah a Lebanon, in ji Hagari
    • Ya ƙara da cewa sojojin ƙasarsa na cikin shirin ko-ta-kwana a kowane lokaci.
    • Mun kuma haramta taruwar jama'a da ya wuce mutum 1,000 a tsakiyar Isra'ila.
  14. 'Yansanda sun musanta zargin shirya garkuwa da mutane a Abuja

    'Yansandan Najeriya sun musanta raɗe-raɗin zargin shirya garkuwa da mutane a jami'ar Abuja.

    Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke shirin gudanar da bukukuwan cikar ƙasar shekara 64 da samun 'yancin kai cikin mako mai zuwa.

    A 'yan ƙwanakin nan ne dai zargin shirya garkuwa da mutane a jami'ar ya karaɗe shafukan sada zumunta.

    To sai dai cikin wata sanarwa da kakakin 'yansandan birnin Abuja, Josephine Adeh ta fitar ta ce rahotonnin shirya harin ba gaskiya ba ne.

    “Rundunar 'yansandan Abuja, na son fayyace wa al'umma cewa waɗannan rahotonni ba gaskiya ba ne, labarai ne irin na ƙanzon kurege, kuma marasa tushe, da aka ƙirƙira da nufin haifar da fargaba da tsoro a tsakanin mazauna Abuja da na jami'ar”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

    Josephine Adeh ta ƙasa da cewa tuni rundunar ta ƙara girke jami'an 'yansandan da kayan aiki a faɗin birnin da kewaye.

    A baya-bayan nan birnin na Abuja ya fuskanci karuwar matsalar garkuwa da mutane. Inda mazaune unguwannin da ke wajen birnin ke cewa masu garkuwar na addabarsu a wasu lokuta ba tare da ɗaukin jami'an tsaro ba.

  15. EU ta gargaɗi jiragen samanta su kauce wa samaniyar Lebanon da na Isra'ila

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ga gargaɗi jiragen samanta su kauce wa bi ta sararin samaniyar ƙasashen Isra'ila da Lebanon zuwa wata mai zuwa.

    Hukumar kula da kariyar sufurin jiragen sama na ƙungiyar Tarayyar Turan (EASA), ne ya fitar da gargaɗin ga duka jiragen saman ƙasashen mambobin ƙungiyar, har sai ''nan da 31 ga watan Octoba''.

    "EASA za ta ci gaba da lura da yanayin, domin duba yiwuwar ƙara ko rage wa'adin, la'akari da ƙari ko ragin barazanar hatsari'', kamar yadda sanarwar ta yi ƙarin haske.

  16. Labarai da dumi-dumi, Hezbollah ta tabbatar da kisan Hassan Nasarallah

    Ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon ta tabbatar da kisan jagoranta Hassan Nasarallah.

    Cikin wani saƙo da ƙungiyar ta fitar a shafinta na Telegram, ta ce ''za ta ci gaba da yaƙi da Isra'ila da goyon bayan Gaza da Falasɗinawa tare da kare Lebanon da mutanenta''.

    Tun ɗazu ne dai Isra'ila ta fitar da sanarwar kisan jagoran ƙungiyar, a wani hari da jirgin yaƙinta ya kai tsakiyar shalkwatar Hezbollah, da ta ce yana ƙarƙashin ƙasa a ƙasan wani gida da ke unguwar Dahieh a birnin Beirut.

  17. Harbi kan mai tsautsayi ya kashe mutum 17 a Afirka ta Kudu

    An kashe mutum 17 a wani harbin kan mai tsautsayi da ya auku a lardin gabashin Cape na ƙasar Afirka ta Kudu.

    Kawo yanzu 'yansanda ba su iya gano maharan da kuma dalilinsu na kai harin ba.

    'Yansanda sun ce harbe-harben sun yi sanadin kisan mata 15 da wasu maza biyu a wani gidan gona a Lusikisiki ranar Juma'a da daddare.

    'Yansandan sun ƙara da cewa mutanen da ake kashen 'yan'uwan juna da makwabta ne da suka taru don gudanar da wani bikin al'ada na ƙarshen makokin mutuwar wata uwa da 'yarta da suka mutu a shekarar da ta gabata.

    Mutanen sun taru ne domin shirya kujerun da za a yi amfani da su a lokacin bikin, lokacin da aka fara harbin.

    Jami'ai sun bayyana lamarin da rashin imani da tsautsayi, yayin da ake sa ran ministan 'yansandan ƙasar, Senzo Mchunu zai ziyarci yankin.

  18. Tinubu ya naɗa majalisar gudanarwar hukumar raya yankin arewa maso yamma

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu aike da sunayen shugabannin majalisar gudanarwar sabuwar hukumar raya yankin arewa maso yammacin ƙasa zuwa ga majalisar dattawan ƙasar domin amince wa naɗinsu.

    Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ya ce matakin na zuwa ne bayan sanya hannu kan dokar da ta amince da ƙirƙiro sabuwar hukumar.

    A ranar 24 ga watan Yuli ne dai Shugaba Tinubu ya sanya hannu kan sabuwar dokar.

    Mutanen da Shugaba Tinubun ya aike da sunayensu don jagorantar sabuwar hukumar sun haɗa da:

    Ambassada Haruna Ginsau (Jigawa) a matsayin shugaban majalisar gudanarwar hukumar.

    Farfesa Abdullahi Shehu Ma’aji (Kano) a matsayin shugaban hukumar.

    Sauran mambobin hukumar sun haɗa da :

    • Dakta Yahaya Umar Namahe (Sokoto)
    • Hon. Aminu Suleiman (Kebbi)
    • Sen. Tijani Yahaya Kaura (Zamfara)
    • Hon. Abdulkadir S. Usman (Kaduna)
    • Hon. Engr. Muhammad Ali Wudil (Kano)
    • Shamsu Sule (Katsina)
    • Nasidi Ali (Jigawa)

    Sanarwar ta ci gaba da cewa ana sa ran sabbin shugabannin za su yi amfani da ƙwarewarsu wajen gina sabuwar hukumar.

  19. Za a kwashe marasa lafiya daga asibitocin kudancin Beirut

    Ma'aikatar lafiyar Lebanon ta umarci asibitocin da ke tsakiyar birnin Beirut da kewaye su shirya kwaso marasa lafiyar da ke asibitocin yankin kudancin birnin.

    Cikin wata sanarwa da ta fitar da safiyar yau, Asabar ta ce asibiton tsakiyar birnin da sauran wuraren da ''hare-haren Isra'ila ba su shafa ba'' su daina karɓar marasa lafiyar da ba su da buƙatar kulawar gaggawa har zuwa ƙarshen makon gobe.

    Matakin na zuwa ne yayin da Isra'ila ta shafe tsawon dare tana luguden hare-hare zuwa kudancin birnin.

  20. Hotunan yadda saman birnin Beirut ta turnuƙe da hayaƙi bayan hare-haren Isra'ila

    Yayin da Isra'ila ta shafe tsawon dare tana luguden hare-hare a birnin Beirut har zuwa wayewar yau, wakilin BBC da ke birnin ya ce mutane da dama da suka rasa muhallansu sun kwana gefen titunan birnin.

    Ga hotunan wasu sassan birnin a safiyar yau Asabar