EFCC ta kama tsohon gwamnan Taraba kan zargin almundahanr naira biliyan 27
Hukumar EFCC mai yaƙi da cin hanci da rashawa ta kama tare da tsare tsohon gwamnan Taraba, Darius Ishaku bisa zargin almundahanar kuɗi da yawansu ya kai naira biliyan 27.
Jaridun Najeriya sun ruwiato cewa tsohon gwamnan zai fuskanci tuhume-tuhume 15 da suka haɗa da cin amana, ɓarnatar da kuɗi da kuma karkatar da kuɗaɗen gwamnatin jihar da na ƙananan hukumomi.
Laifukan da ake zargin tsohon gwamnan, an aikata su ne tsakanin 2015 zuwa 2021 lokacin da yake riƙe da matsayin gwamnan jihar da ke arewa maso gabashin Najeriya.