, Najeriya 0-0 Moroko
An yi karon-batta a mintuna bakwai na farkon wannan wasa. Kowa jininsa a ƙumba.
Ana goge raini.
Karawar Moroko da Najeriya a matakin kusa da wasan ƙarshe domin tantance ƙasar da za ta buga wasan ƙarshe da Senegal a ranar Lahadi a Gasar Kofin Ƙwallon Ƙafa ta Nahiyar Afirka 2025.
Ibrahim Haruna Kakangi tare da taimakon fasahar AI
An yi karon-batta a mintuna bakwai na farkon wannan wasa. Kowa jininsa a ƙumba.
Ana goge raini.

Asalin hoton, Getty Images
Babban jami'in hukumar ƙwallon ƙafa ta duniya Fifa, Arsene Wenger, yana halartar wannan karawa.
Semi Ajayi ya yi asarar ƙwallo inda Ismael Saibari ya ɗauka, amma an ƙwace nan take domin hana ɗan wasan na Moroko doka ta.
Magoya bayan masu wasa a gida sun shirya fashewa da sowa in da ƙwallon ta je raga.
Ian Williams, wakilin BBC Sport a Rabat
Wannan filin wasa ba a cewa komai. Ko ina ya yi ja jajir.
Lokacin da alƙalin wasa ya hura usur domin fara wasa ko ina ka duba ana kaɗa jan ƙyalle.
Wannan ne abin da ake kira fa'idar wasa a gida.
Moroko ce ta fara wasa.

Asalin hoton, Getty Images
Matakin rukuni:
Morocco 2-0 Comoros
Morocco 1-1 Mali
Zambia 0-3 Morocco
Zagaye na 16
Morocco 1-0 Tanzania
Kwata-fainal
Kamaru 0-2 Morocco

Asalin hoton, Getty Images
Matakin rukuni:
Najeriya 2-1 Tanzania
Najeriya 3-2 Tunisia
Uganda 1-3 Najeriya
Zagaye na 16
Najeriya 4-0 Mozambique
Kwata-fainal:
Algeria 0-2 Najeriya
Mai tsaron raga: Nwabali
Masu tsaron baya: Osayi-Samuel, Ajayi, Bassey, Onyemaechi
Tsakiya: Onyeka, Onyedika, Iwobi
Gaba: Osmihen, Lookman, Adams
Mai tsaron raga: Bounou
Masu tsaron baya: Hakimi, Aguerd, Masina, Mazraoui
Tsakiya: Diaz, El Khannouss, El Aynaoui, Saibari, Ezzalzouli
Gaba: EL Kaabi
An sanar da sunayen ƴanwasa kuma ƴanwasan suna motsa jini.