Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo maku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, 12/06/2024

Rahoto kai-tsaye

Daga Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Kwamandan Hezbollah ya mutu a wani harin da Isra'ila ta kai

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani harin da Isra'ila ta kai a kudancin Lebanon ya kashe mutane huɗu ciki har da wani kwamandan ƙungiyar Hizbullah.

    Ƙungiyar ta bayyana sunan kwamandan nata da Taleb Abdallah wanda ɗaya ne daga cikin manyan mayaƙan Hezbollah da aka kashe a cikin watanni takwas da suka kwashe suna gwabzawa da Isra'ila.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar Lebanon sun ce an yi amfani da jirage marasa matuƙa a harin da aka kai a garin Joya.

    Isra'ila dai ta sha alwashin ɗaukar fansar hare-haren da ƙungiyar ke kai mata a kan iyakoki, inda a baya-bayan nan wani harin da Hezbollah ta kai ya haddasa wutar daji da aka daɗe ba a kashe ba.

    Ƙungiyar Lebanon a nata ɓangaren ta ce tana kai hare-haren ne kan Isra'ila da sunan martanin hare-haren kwamandojinta da Isra'ilar ke yi da kuma yaƙin da take yi a Gaza.

  2. Dakarun RSF na dab da ƙwace birnin El-Fasheer - Amurka

    ..

    Asalin hoton, AFP

    Jakadan Amurka na musamman a Sudan ya yi gargaɗin cewa daga nan zuwa kowanne lokaci dakarun RSF na iya ƙwace garin El-fasheer da suka yi wa ƙawanya.

    A wata hira da BBC, Tom Perriello ya yi kira da a kawo ƙarshen yaƙin nan take.

    Ya ce halin da ake ciki a El-fasher, ya yi munin gaske, fararen hula da dama sun rasa rayukansu, sannan lamarin zai ƙara munana idan garin ya suɓuce daga hannun dakarun gwamnati.

    Dubban fararen hula da suka yi gudun hijira fiye da shekara guda ne ke neman mafaka a garin na El-fasheer.

    A cikin watanni biyun da suka gabata, dakarun RSF sun yi wa garin ƙawanya, wanda shi ne ɗaya tilo da ke ƙarƙashin ikon sojoji a ɗaukacin yankin na Darfur.

  3. 'Akwai barazanar ambaliya a jihohi 31 da ƙananan hukumomi 148'

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar Bayar da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce akwai hasashen jihohin ƙasar 31 da ƙananan hukumomi 148 ka iya fuskantar ambaliya a damunar bana.

    Hukumar ta buƙaci gwamnatocin jihohin ƙasar da su bi gargaɗinta sannan su aiwatar da matakan kariya daga bala'in ambaliya domin tabbatar da kare rayuka da dukiyoyi al'umma.

    Shugabar hukumar, Zubaida Umar wadda ta tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da jami'an gwamnatin jihar Edo, ta nanata muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfe da jihar wajen samar da shirin ko-ta-kwana domin tunkarar barazanar ta ambaliya.

    Hukumar ta NEMA dai ba ta lissafa jerin sunayen jihohin da ƙananan hukumomi ba amma ta ce yawanci birane da garuruwan da ke kusa da ruwa ka iya fuskantar barazanar.

  4. Majalisar Dinikin Duniya ta zargi Isra'ila da Hamas kan cin zarafin yara

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A karon farko, Majalisar Ɗinkin Duniya ta saka Isra'ila da Hamas cikin jerin kasashen da suka aikata abun da ta kira abun kunyar cin zarafin Ƙananan yara.

    A cikin rahotonsa na shekeara-shekara kan yadda tashe-tashen hankali ke shafar yara, Sakatare Janar, na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce yaƙin da ake yi a Gaza ya haifar da cin zarafin yara da ba a taɓa ganin irinsa ba.

    Gwamnatin Isra'ila ta mayar da martani a fusace bayan ɓullar labarin shirin ɗaukar wannan mataki a makon jiya.

    Firaministan ƙasar, Benjamin Netanyahu, ya bayyana matakin na Majalisar Ɗinkin Duniya a matsayin wasan kwaikwayo.

    Ita dai Majalisar Ɗinkin Duniya na sakin sunayen ne domin kunyata duk ƙasar da aka samu da laifi irin wannan.

  5. Tinubu ya yi gum kan batun albashi mafi ƙanƙanta

  6. Masar da Qatar na shiga tsakani kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Masar da Qatar sun ce za su ci gaba da ƙoƙarin shiga tsakani kan yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a zirin Gaza, bayan samun martanin farko a hukumance daga ƙungiyar Hamas kan shirin da kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ke mara wa baya.

    Ƙasashen biyu ba su bayar da cikakken bayani kan abun da martanin Hamas ɗin ya ƙunsa ba.

    Kakakin ma'aikatar tsaron ƙasar Amurka, John Kirby ya ce ana duba martanin na Hamas. Kungiyar dai ta ce za ta hau teburin sulhu da zuciya ɗaya.

    "Mun karɓi maratanin Hamas da ta gabatar ta hannun Qatar da Egypt muna kuma nazartarsa yanzu haka kuma ina tunanin cewar iya abin da za mu iya yi kenan yanzu, tunda mun sami wannan martanin a hannun yanzu, kuma za mu yi aiki a kansa." In ji Kirby.

    Wakiliyar BBC ta ce wani jami'in Hamas Aze Tariksh ya ce martanin na su ya bude kofar cimma yarjrjeniya.

    To amma wani jami'in Isra'ila da ya nemi a sakaye sunansa ya zargi Hamas da sauya wasu muhimman sassa na daftarin yarjejeniyar, kuma haka a wajensu, tamkar ta yi watsi da yarjejeniyar ne.

  7. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barka da safiyar ranar Laraba wadda Hausawa ke yi wa kirari da ta Bawa ranar samu. Da fatan za ku kasance da shafin namu na kai tsaye domin samun labarai da rahotanni da bayanai daga Najeriya da Nijar da wasu ƙasashen Afirka da ma fadin duniya. Mun gode!