West Ham za ta soke kwantiragin da ta rage tsakaninta da Wilson, West Ham United
Asalin hoton, gett
West Ham na dab da cimma yarjejeniya da ɗan Callum Wilson domin kawo ƙarshen kwantiraginsa da ta rage a tsakaninsu.
Wilson ya koma West Ham, bayan da ƙwantiraginsa ya kare a Newcastle United a karshen kakar da ta wuce, wanda ya ci ƙwallo huɗu a wasa 18 a West Ham.
Za a kai ga wannan matsaya, saboda ba zai ke samun buga wasanni da yawa ba, sakamakon sayen ƴan wasa, Pablo Felipe da Taty Castellanos da ta yi a wannan watan.
Wilson mai shekaru 33 yana son ci gaba da buga tamaula akai-akai.
Saboda haka, ana sa ran Wilson zai bar Hammers, inda majiyoyi suka tabbatar da cewa tattaunawa kan an kusan kammala kawo karshen yarjejeniyar da ta rage masa a ƙungiyar.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Korar da aka yi wa kocin Manchester United, Ruben Amorim za ta iya ba dan wasan Ingila Marcus Rashford, mai shekara 28, wanda ke zaman aro a Barcelona, hanyar komawa Old Trafford.(Mirror)
Watakila Oliver Glasner na cikin wadanda Man U ke so su maye gurbin Amorim da ta kora.
Shugabanin United na kaunar Glasner, dan kasar Australia mai shekara 51,wanda kwantaraginsa da Crystal Palace zai kare a bazara (Telegraph)
Ita ma Fulham na jiran Manchester United ta tuntube ta kan kocinta, Marco Silva, dan kasar Portugugal. (Sun)
Dan wasan tsakiya na Ingila Kobbie Mainoo, mai shekara 20 da dan wasan Netherlands Joshua Zirkzee, mai shekara 24, da kuma dan wasan tsakiya na Uruguay Manuel Ugarte, mai shekara 24, duk sun nuna alamun barin Manchester United a watan Janairu idan Amorim ya zauna. (Mail)
Juventus ta fara tattaunawa da Liverpool kan batun bada aron Federico Chiesa, inda dan wasan na Italiya mai shekara 28 ya nuna alamun yana son ya koma kungiyar ta Seria A inda ya shafe kaka biyu tsakanin 2022-2024. (La Gazzetta dello Sport)
Bournemouth ta shirya biyan Yuro miliyan 40 don siyan dan wasan Stuttgart da Jamus Jamie Leweling a matsayin wanda zai maye gurbin dan wasan Ghana Antoine Semenyo mai shekaru 25, wanda ke dab da komawa Manchester City, amma kungiyar ta Bundesliga ta yi watsi da tayin na Cherries.(Sky Sports )
Ruben Dias zai yi jinyar mako shida a Man City, Manchester City
Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan Manchester City, Ruben Dias zai yi jinyar mako shida, kamar yadda koci Pep Guardiola ya sanar.
An sauya shi sakamakon raunin da ya ji a wasan Premier League da suka tashi 1-1 da Chelsea a ranar Lahadi.
Ranar Litinin aka sanar da Josko Gvardiol, zai yi dogon jinya bayan da ya karya ƙafa, haka kuma John Stone har yanzu bai murmure ba.
Rayan Aït-Nouri yana buga gasar kofin nahiyar Afirka, yayin da Nathan Aké bai koma kan ganiya ba..
Wannan halin da ake ciki watakila Manchester City za ta nemi ɗan baya a wannan wata, kuma an ruwaito cewa Marc Guéhi na Crystal Palace yana cikin jerin ƴan wasan da take son saya.
Ana kuma ganin cewa City na dab da kammala yarjejeniya da ɗan wasan Bournemouth, Antoine Semenyo, domin ya koma Etihad da taka leda.
John Stones dai ya shafe wata guda yana jinya.
Maresca ya yi ban kwana da magoya bayan Chelsea cikin ban tausayi, Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Enzo Maresca ya yi ban kwana da magoya bayan Chelsea cikin ban tausayi a ranar Talata, inda ya ce ya cimma duk abin da zai iya a cikin wata 18 da ya yi yana jagorantar ƙungiyar, bayan da aka kore shi ranar 1 ga watan Janairu.
Kocin ɗan Italiya shi ne na baya-bayan nan da ya shiga cikin jerin sauye-sauyen masu horaswa a Chelsea ƙarƙashin mallakar BlueCo, bayan wasa ɗaya kacal da ya ci a cikin bakwai a Premier League da ta kai mahukuntan suka ɗauki matakin rabuwa da shi.
A ƙarƙashin jagorancinsa, Chelsea ta lashe gasar Conference League da Fifa Club World Cup, sannan ta samu tikitin shiga gasar Champions League a kakar bara — karo na farko cikin shekaru biyu — amma kocin ɗan Italiya bai samu cikakken goyon bayan mahukuntan ba.
Bayan tafiyarsa a makon da ya gabata, an naɗa kocin ƴan ƙasa da shekara 21 na Chelsea, Calum McFarlane, a matsayin rikon kwarya, daga baya aka tabbatar da Liam Rosenior a ranar Talata a matsayin sabon babban kocin Chelsea.
, Daga jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Dole Chelsea ta dauki mataki cikin gaggawa idan tana son ta sayi dan wasan Rennes Jeremy Jacquet, mai shekara 20, saboda Liverpool da Arsenal da Real Madrid da kuma Manchester United duk suna sha'awar dan wasan na Faransa (Teamtalk)
Barcelona na son Al-Hilal ta bada aron dan wasan Portugal Joao Cancelo, mai shekara 31, yayin da Inter Milan ke zawarcinsa. (La Gazzetta dello Sport)
Crystal Palace na shirin fafatawa da West Ham don siyan dan wasan Norway Jorgen Strand Larsen, mai shekara 25, daga Wolves. (Mail)
Tottenham ta tattauna da Santos kan kulla yarjejeniyar siyan dan wasan Brazil , Souza, mai shekara 19, wanda ke daukar hankalin Newcastle. (Teamtalk)
Dan wasan Ingila Callum Wilson, mai shekara 33, na tattaunawa da West Ham domin kawo karshen kwantiraginsa bayan ya shafe wata biyar a kungiyar (Athletic)
Tsohon kocin Wolves Gary O'Neil ya tattauna da Strasbourg kan zama sabon kocinta inda, kocin na kungiyar Faransa na yanzu Liam Rosenior ke cikin wadanda za su iya maye gurbin Enzo Maresca a Chelsea. (Athletic)
Dan wasan gaban Crystal Palace Romain Esse mai shekaru 20 a duniya ya shirya tsaf domin shafe sauran kakar wasan a matsayin aro a Coventry City.(Sky Sports)
Me Rosenior zai fara fuskanta a Chelsea, Chelsea
Asalin hoton, BBC Sport
Da yake Chelsea za ta buga wasan Premier League a gidan Fulham ranar Laraba da daddare, Liam Rosenior ba zai fara aiki a hukumance ba sai karawar FA Cup da Charlton a ƙarshen mako, wato ranar Lahadi, abubuwa na iya sauyawa kafin wasansa na farko a gasar Premier League.
Musamman ganin cewa maki uku ne ya raba ƙungiya takwas daga Chelsea har zuwa Everton da ke matsayi na 12.
Amma yanzu, Chelsea tana matsayi na biyar bayan da ta samu maki ɗaya a wasan da ta tashi canjaras da Manchester City, a karkashin jagorancin kocin riƙon ƙwarya, Calum McFarlane.
Da yake Liverpool da ke matsayi na huɗu za ta je gidan wadda take jan ragamar teburin, Arsenal ranar Alhamis, watakila Rosenior ya kalli wasan da Chelsea za ta je Fulham a Premier League ranar Alhamis.
Sai dai ana sa ran zai ja ragamar wasa da Chalton a FA Cup zagaye na uku da Premier League da Arsenal da kuma Brentford.
Ko me ya sa Chelsea ta ɗauki Rosenior sabon kociyanta, Chelsea
Asalin hoton, Getty Images
Kasa da shekaru biyu bayan an kore shi daga Hull City, an naɗa Liam Rosenior a matsayin sabon kocin Chelsea.
Tun bayan barinsa Hull, Rosenior ya nuna kansa a matsayin ɗaya daga cikin matasan masu horaswa mafi taka rawar gani a Turai, a cikin watanni 18 da ya yi a Strasbourg ta Faransa.
An bayyana shi a matsayin “mai ƙirƙira sabbin dabarun tamaula” kuma mutum ne da ke “tafiyar neman kaiwa zuwa kololuwa”, inda mai shekaru 41 ya burge manyan mahukuntan Chelsea, da cewar yana aiki a cikin tsari da cewar ba kamar yadda wanda ya gada, Enzo Maresca ke yin nashi kokarin.
To sai dai tambayar da ake me ya sa Chelsea ta amince da ɗaukar mai horarwar da ba shi da kwarewa a kololuwar wasannin Turai?
Ƴan wasan da suka fi zura ƙwallo a Gasar Kofin Afirka ta 2025, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Gasar cin kofin nahiyar Afirka ta fara nisa, inda yanzu haka ake buga matakin 'yan 16.
Bayan nan za a tafi matakin kwata-fainal sai kusa da ƙarshe, sannan kuma a buga wasan ƙarshe ranar 18 ga watan Janairun 2026.
Ya zuwa yanzu zaratan ƴan kwallo na ci gaba da ɗaga raga.
Aljeriya za ta kara da Jamhuriyar Congo a Afcon, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Za a yi tata burza tsakanin Aljeriya da Jamhuriyar Congo a wasan zagaye na biyu a gasar kofin Afirka da ake gudanarwa a Morocco.
Sau bakwai suka kara a dukkan haduwa, Aljeriya ta yi nasara uku da canjaras huɗu.
Daga ciki za suyi tata burza a Afcon bayan 1998 da Aljeriya ta yi nasara cin 1-0 da a shekarar 2000 da suka tashi 0-0 a Kumasin, Ghana.
Aljeriya tana da kofin nahiyar biyu, itama Jamhuriyar Congo tana da Afcon biyu a tarihi.
Afcon zagaye na biyu: Ivory Coast da Burkina Faso, Afcon Morocco 2025/26
Asalin hoton, Getty Images
Wasan Ivory Coast da Burkina Faso na makwabta ne da zai ja hankalin masu ruwa da tsaki a fannin taka leda.
Za kuma su kara ranar Talata a wasan zagaye na biyu a gasar cin kofin Afirka da ake yi a Morocco.
Sun fuskanci juna sau 20 a dukkan fafatawa, Ivory Coast ta yi nasara takwas, Burkina Faso ta ci wasa uku da canjaras tara a tsakaninsu.
Wannan ne karo na uku da za su kece raini a Afcon, bayan 2010 da kuma 2012, amma wasan farko a zagayen ƴan 16 a babbar gasar tamaula ta Afirka.
Ivory Coast mai rike da kofin tana da uku jimilla, ita kuwa Burkina Faso ta taba yin ta biyu a 2013 da aka yi a Afirka ta Kudu.
Chelsea ta naɗa Rosenior a matsayin sabon mai horaswa
Asalin hoton, Getty Images
Bayanan hoto, Liam Rosenior
Ƙasa
da shekara biyu bayan korar da ƙungiyar Hull City ta yi masa daga aiki,
ƙungiyar Chelsea ta bayyana Liam Rosenior a matsayin sabon mai horas da ƴan
wasanta.
Tun
bayan barin shi daga ƙungiyar Hull, Rosenior ya yi ƙoƙarin fito da kansa a
matsayin ɗaya daga cikin matashin masu horaswa masu hazaƙa a nahiyar Turai
yayin da yake aiki a ƙungiyar Strasbourg.
Mai
shekara 41 a duniya, Rosenior ya burge mahukuntan Chelsea bayan sun samu saɓani
da magabacinsa Enzo Maresca.
Akwai
matsi kan Chelsea wajen ganin ta samu koci mafi dacewa, inda a ranar Lahadin
da ta gabata magoya bayan ƙungiyar suka riƙa ambaton sunan tsohon mamallakin
ƙungiyar Roman Abrahamovich lokacin da ƙungiyar ta yi canjaras da Manchester
City.
Haka
nan wasu daga cikin magoya bayan sun shirya yin zanga-zanga gabanin karawar ƙungiyar
na gaba a gasar Premier da ƙungiyar Brentford.
Wane ne zai maye gurbin Amorim a United?
Asalin hoton, Getty Images
A ranar Litinin ne ƙungiyar Manchester United ta sallami mai horas da ƴan wasanta Ruben Amorim bayan kwashe lokaci ƙungiyar na faɗi-tashi.
Ƙungiyar ta sanar da cewa Darren Fletcher ne zai jagoranci wasanta na gaba da ƙungiyar Burnley.
To amma yanzu wane ne zai maye gurbin Amorim a matsayin kociyan ƙungiyar na dindindin?
Bayan gazawar Erik
ten Hag, da Ralf Rangnick da kuma Amorim a yanzu, shin ko ya kamata United ta nemo
wani kociyan da ya yi abin a zo a gani a gasar Premier?
Unai Emery na yin kyakkyawan aiki a Aston Villa, inda ya ɗago
ƙungiyar daga can ƙasar teburin Premier zuwa gasar nahiyar Turai, ga shi kuma a
wannan kakar suna gogayya don lashe Premier.
To amma bai taɓuka abin kirki ba a lokacin da ya riƙe
Arsenal, ko duk da haka United za ta ce tana son shi?
Andoni Iraola shi ma babu shakka za a samu ƙungiyoyin da ke
son shi bayan jagorantar Bournemouth har ta ƙare a matsayi na 9 a kakar da ta
gabata.
Zai yi wahala ya ce a’a idan Manchester United ta neme shi.
Kwantaragin Oliver Glasher zai kare a Crystal Palace a ƙarshen kaka, kuma ƙungiyar ce ta lashe kofin ƙalubale na FA a kakar da ta gabata.
Shi kuwa Eddie Howe ya kawo ƙarshen tsawon shekarun da Newcastle
ta kwashe babu kofi, inda ya ci mata kofin Carabao.
Ko kuwa United za ta fi son ta ɗauki ɗan cikin gida?
Tsohon ɗan wasan tsakiya na ƙungiyar Darren Fletcher shi ne
mai horas da ƴan ƙasa da shekara 18 na ƙungiyar, kuma ya yi shekara 11 yana
wasa ƙarƙashin Alex Ferguson.
Wani da za a iya sa ran zai karɓi aikin shi ne Michael
Carrick.
Yanzu ba ya da aiki bayan Middlesbrough ta sallame shi a watan Yuni.
A wajen Ingila kuma akwai kociyoyi da yawa da United za ta
iya ƙyalla ido a kansu:
Ɗaya daga cikin irin waɗannan da aka sha alaƙanta United da
shi, shi ne Mauricio Pochetinho.
Wani da mutane da dama ke tunani a kai kuma shi ne tsohon
kocin Barcelona Xavi.
Shi ma Zinedine Zidane ya kwashe shekara huɗu yanzu ba ya aikin
horaswa tun bayan barin Real Madrid.
Wane ne ya kamata United ta ɗauko?
Barka da warhaka!
Wannan shafin zai kawo muku labaran wasanni a faɗin duniya daga ranar 4 zuwa 10 ga watan Janairun 2026.