Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 01/01/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail da Haruna Kakangi

  1. Ƙudurin dokar haraji zai ƙara jefa jama'armu cikin talauci - Gwamnatin Kano

    Abba Kabir Yusuf

    Asalin hoton, FACEBOOK/Abba Kabir Yusuf

    Gwamnatin jihar Kano ta bayyana hamayyarta ga ƙudirin dokar harajin da yanzu haka ke gaban majalisar dokokin Najeriya wanda shugaba Tinubu ya aike wa da majalisar.

    Gwamna Abba Kabir Yusuf wanda mataimakinsa, Aminu Abdussalam Gwarzo ya wakilta ne ya bayyana haka a yayin bikin murnar shiga sabuwar shekarar 2025 a dandalin Ma'ahaha da ke birnin Kano.

    Wata sanarwa da ke ɗauke da sa-hannun mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba ta ce gwamnan ya ce "wannan kundin dokar harajin ba za ta magance matsalar tattalin arziƙinmu ba. Kano tana hamayya da wannan ƙudiri da zai shafi walwalaw al'umma."

    Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin tarayya ke ci gaba da tankiyya tsakaninta da gwamnan jihar Bauchi, Bala Muhammad wanda ya soki kundin.

  2. An gano makamai da tutar ƙungiyar IS a motar da aka kai hari New Orleans

    New Orleans

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaron FBI ta ce an gano makamai da tutar ƙungiyar IS cikin a-kori-kuran da wani mutum ya kai hari da ita a burnin New Olins na Amurka lokacin bikin shigowar sabuwar shekara.

    Sun bayyana maharin da suna Shamsudeen Jabbar Dan shekara 42, wanda tsohon ɗn Amurka ne daga jihar Texas. An kashe shi ne a musayar wuta da 'yan sanda.

    Harin dai ya yi ajalin a ƙalla mutum 10 yayin da gwammai suka jikkata.

    An kuma gano wani abin fashewa a yankin da aka kai harin.

  3. Elon Musk ya sauya sunansa zuwa Kekius Maximus a shafinsa na X

    Elon Musk

    Asalin hoton, Reuters

    Attajirin mai kuɗin nan na duniya, Elon Must ya janyo ka-ce-na-ce bayan sauya sunansa a shafinsa na X zuwa "Kekius Maximus".

    Attajirin wanda makusanci ne ga zaɓaɓɓen shugaban Amurka, Donald Trump bai yi wani bayani ba dangane da dalilin sauya sunan nasa da kuma hoton da ya saka wanda ke shaguɓe da masu tsattsauran ra'ayin siyasa ke amfani da shi.

    Wannan al'amari dai ya sanya kasuwar kirifto a duniya ta ɗaga.

    A baya dai mista Musk ya sha janyo sauyin alƙaluma a kasuwar kirifto sakamakon maganganunsa a kafafen sada zumunta duk da cewa a yanzu haka babu tabbacin cewa yana da hannu a tashin nau'in kuɗin na kirifto memecoin.

  4. Mun yi wa yara miliyan 10 rijista cikin watanni uku a Najeriya - NPC

    Hukumar ƙidaya ta Najeriya (NPC) ta ce ta yi wa yara miliyan goma rijista tare da ba su takardar shaidar haihuwa a cikin watanni ukun da suka gabata.

    Shugaban hukumar, Alhaji Nasir Isa Kwara ne ya faɗi hakan ga manema labarai bayan uwargidar shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu ta miƙa takardar shaidar haihuwa ga jaririyar da aka fara haifa a shekarar 2025 a babban asibitin Asokoro da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

    Shugaban hukumar na ƙasa wanda ya samu wakilcin Kwamishan tarayya ta hukumar daga jihar Katsina, Bala Banya, ya bayyana cewa baza suyi ƙasa a gwiwa ba waje tabbatar da cewa duk jaririn da aka haifa a Najeriya anyi masa rijista kuma an bashi takardar shaidar haihuwa.

    '' Mun ɗau wani lokaci muna wannan aikin, kuma a watanni ukun baya, munyi wa yara da basu kai shekara 1 ba zuwa ƴan shekara 5 su miliyan 10 rijista. A yanzu kuma za mu mayar da hankali kan yara ƴan ƙasa da shekara ɗaya'' a cewar shi.

    Ya kuma ce sabbin shaidar haihuwar wanda akeyi ta yanar gizo na zuwa ne da lambar shaidar zama ɗan ƙasa wato NIN.

  5. Hare-haren Isra'ila a Gaza sun kashe mutum 17 na farko a 2025

    Aƙalla mutum 17 ne suka mutum a wasu hare-haren da dakarun Isra'ila suka kai yankin Gaza a lokacin da ake bikin shiga sabuwar shekarar 2025.

    Dakarun tsaron farin kaya na Civil Defence sun ce an kashe aƙalla mutum 15 wasu 20 na daban sun jikkata lokacin da harin ya sauka a wani gida a Jabaliya.

    Wakiliyar BBC ta ce Kafafen yaɗa labaran cikin gida sun ce mafi yawan wadanda abin ya shafa yara ne.

    Rundunar dakarun tsaron Isra'ila ta ce za ta yi bincike kan rahotannin harin.

    Kamfanin dillancin labaran Falasdinu WAFA ya ce an ƙara kashe wasu mutum biyu na daban a sansanin 'yan gudun hijira na Bureij.

  6. Iran za ta tattauna da ƙasashen Turai kan shirinta na makamashin nukiliya

    Iran

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta ce za ta fara wata tattaunawa ta musamman da wasu ƙasashen nahiyar Turai uku kan shirinta na makamashin nukilya a ranar 13 ga watan nan na Janairu.

    Babban mai shiga tsakani na ƙasar, Kazem Garibabadi ne ya shaida wa manema labarai cewa, za a yi tattaunawar ne a Geneva da wakilan Burtaniya da Faransa da kuma Jamus.

    Tattaunawar da ake yi yanzu na burin samar da mafita ne kan yarjejeniyar 2015 da Amurka ta sa ƙafa ta shure - ta yadda za a taƙaita shirin Tehran na samar da nukiya ita kuma a sassauta mata takunkuma da aka ƙaƙaba mata a madadin hakan.

  7. An dakatar da shigar da gas daga Rasha zuwa Turai

    Bututun mai

    Asalin hoton, Reuters

    An dakatar da shigar da gas ɗin ƙasar Rasha zuwa nahiyar Turai ta Ukraine, bayan Kyiv ɗin ta ƙi sabunta yarjejeniyarta da Moscow.

    Ukraine ta ce ba za ta ci gaba da amincewa da yarjejeniyar da za ta riƙa samarwa da maƙiyanta kudin shiga ba na biliyoyin daloli.

    Poland wadda gas ɗin da take samarwa ba zai isa buƙatar da ake da ita ba, ta bayyana matakin a matsayin gagarumar nasara. Hukumar Tarayya Turai ta ce tasirin da za a gani kan matakin ƙalilan ne.

    Wannan mataki ya fusata Slovakia, ta kuma yi barazanar dakatar da baiwa Ukraine wutar lantarki.

  8. Kenya na bincike kan wani ƙarfe da ya faɗo daga sararin samaniya

    Hukumomi a Kenya sun ƙaddamar da bincike kan wani ƙarfe mai nauyin kilogram 500 biyar da ya faɗo daga sararin samaniya a wani ƙauye da ke kudancin ƙasar a ranar Litinin.

    Hukumar kula da sararin samaniya ta Kenya (KSA) ta ce abin da ya fado, ɓurɓushin wani ƙarfe ne da ke jikin na'urar harba kumbon sararin samaniya, kuma ta tabbatar wa mazauna yankin Makueni cewa ba shi da wani barazana ga tsaronsu.

    Hukumar ta KSA ta ce ya kamata a ce ko dai ɓangaren kumbon ya ƙone, ko kuma ya faɗa wuraren da babu mutane, kamar teku.

    Hukumar ta ƙara da cewa tana aiki, bisa ƙa'idojin duniya domin gane daga inda abin ya fito.

    Dubban ɓangarorin nau'rorin da ake turawa sararin samaniya na faɗowa duniya a kullun, amma ba su cika zama barazana ga al'umma ba.

  9. Gwamnatin Najeriya ta cika sharuɗɗan taso ƙeyar Simon Ekpa daga Finland - Chirs Musa

    Chris Musa

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Babban hafsan tsaro na Najeiya Janar Christopher Musa ya ce gwamnatin tarayya ta cika akasarin sharaɗin neman taso ƙeyar Simon Ekpa daga ƙasar Finland.

    Jami'an tsaron Finland sun kama Ekpa, wanda ɗan gwagwarmayar kafa ƙasar Biafra ne a kudu maso gabashin Najeriya, a watan Nuwanban da ya gabata.

    Daga baya wata kotu ta aika shi gidan yari saboda kama shi da laifin yaɗa manufofin ta'addanci a kafafen sada zumunta.

    "Gwamnatin tarayya ta tura mafi yawan abubuwan da ake buƙata ga gwamnatin Finland," in ji janar ɗin yayin da yake magana a shirin talabijin na Channels TV.

    "Ba ni son faɗar abubuwa da yawa a kansa amma ina da tabbas za a yi abin da ya dace."

  10. Shugaban gwamnatin Syria al-Sharaa ya gana da shugabannin Kiristocin ƙasar

    ...

    Asalin hoton, X/@SanaAjel

    Shugaban gwamnatin Syria Ahmed al-Sharaa ya gana da shugabannin Kiristoci a birnin Damascus ranar Talata.

    Kamfanin dillancin labarai na gwamnatin Syria, Sana , ya wallafa hoton shugaban sabuwar gwamnatin tare da wakilan al'ummar Kiristan amma bai bayar da wani ƙarin bayani ba.

    Gidan talabijin na Syria TV da ke Turkiyya ya ce wakilan ɗariƙr Katolika, da 'yan gurguzun Kiristanci na Syria, da Anglican, da cocin Latin duka sun halarci taron.

    An yi ganawar ce yayin da sabuwar gwamnatin ta 'yan Sunni ke neman tabbatar wa da ƙasashen duniya aniyarta game da tsirarun ƙabilu a ƙasar.

    ...

    Asalin hoton, X/@SanaAjel

  11. Ƙasashen Nijar, Mali da Burkina za su kafa tashar talabijin

    Nijar da Mali da Burkina Faso

    Asalin hoton, Reuters

    Kafofin yaɗa labarai a Nijar da Mali da Burkina Faso sun ruwaito a ranar Litinin cewa ƙasashen za su kafa wata tashar talabijin ta intanet da zimmar "ƙarfafa haɗin kai da kuma yaƙi da labaran ƙarya" a yankinsu na Sahel.

    Ƙasashen uku da sojoji ke mulki, sun kafa ƙawance da suka kira Alliance of Sahel States, wanda suke kira da Aes a Faransanci.

    "Ana sa ran tashar za ta inganta harkokin sadarwa tsakanin ƙasashen Sahel kuma a samu tasiri mai ɗorewa bisa muradin shugabannin ƙasashen biyu," in ji rahoton shafin Actu Niger.

    An ƙulla ƙawancen ne a 2023 bayan sun sanar da aniyarsu ta ficewa daga ƙungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas, wadda suka zarga da yi wa ƙasashen Yamma aiki.

    Nijar da Mali da Burkina duka sun yanke alaƙa da ƙasashen Yamma kamar Faransa kuma suka maye gurbinta da Rasha.

  12. Harin da ya kashe mutum 10 a New Orleans ba na ta'addanci ba ne - FBI

    Jami'ar hukumar tsaro ta FBI a Amurka, Alethea Duncan, ta ce ta karɓe ragamar bincike kan harin da wani direba ya kai wa masu bikin sabwar shekara a birnin New Orleans.

    Yayin jawabin da ta yi, ta ce "wannan ba harin ta'addanci ba ne", abin da ya saɓa da kalaman magajin garin.

    Zuwa yanzu ba a san dalilin da ya sa aka samu mabambantan bayanai ba game da lamarin da ya jawo mutuwar mutum 10.

    Duncan ta ce akwai yiwuwar wani abin fashewa da aka gano a wurin kuma ana binciken gano gaskiyar hakan.

    Ta ce mutane za su ƙaurace wa wurin "har sai mun gano abin da ke faruwa".

  13. Direba ya kashe Amurkawa 10 da motarsa yayin bikin sabuwar shekara

    Birnin New Orleans

    Asalin hoton, Reuters

    Aƙalla mutum 10 ne suka mutu a birnin New Orleans da ke Amurka lokacin da wata mota ta kutsa cikin dandazon mutane da asubahin ranar farko ta sabuwar shekara.

    Aƙalla mutum 35 ne suka samu rauni a lamarin.

    Ƴansanda sun ce wani mutum ne ya tuƙa wata motar a-kori-kura a guje cikin dandazon mutane a guje, da niyyar kaɗe mutane da dama.

    Haka nan direban motar ya buɗe wuta kan ƴansanda bayan motar tasa ta tsaya, lamarin da ya sa ya raunata jami'ai biyu.

    Wani jami'in Hukumar bincike ta FBI ya ce an kuma samu wani abu da ake zaton abin fashewa ne a wurin da lamarin ya faru, sai dai ya ce ba hari ba ne na ta'addanci - duk kuwa da cewa magajin garin birnin ya yi zargin hakan.

    An gargadi mutane su ƙaurace wa wurin da lamarin ya faru.

  14. PDP ta nemi Tinubu ya yi bincike kan tiriliyan 25 da ta zargi 'yan APC da sacewa

    Ilya Damagun

    Asalin hoton, PDP

    Babbar jam'iyyar adawa a Najeriya ta PDP ta nemi Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya ƙaddamar da bincike kan kuɗaɗe naira tiriliyan 25 da ta zargi 'yan jam'iyyarsa ta APC da sacewa.

    PDP ta yi wannan kira ne a saƙon da ta wallafa na sabuwar shekara, wanda kakakinta na ƙasa Debo Ologuagba ya sanya wa hannu ranar Talata.

    "Ya kamata shugaban ƙasa ya wanke kansa game da yaƙi da cin hanci da rashawa ta hanyar ba da umarnin yin bincike da kuma dawo da sama da tiriliyan 25 da aka ce shugabannin APC da jami'an gwamnati sun sace," in ji sanarwar.

    Jam'iyyar ta kuma nemi shugaban ya bayyana adadin kuɗaɗen da gwamnatinsa ta tara daga cire tallafin man fetur da ya yi a watan Mayun 2023.

    Haka nan, PDP ta nemi Tinubu ya kawo ƙarshen matsalar tsaro, da yunwa, da kuma ƙarancin man fetur "domin sauƙaƙa wa rayuwar 'yan Najeriya".

  15. Rasha ta yi wa Ukraine ruwan bama-bamai a daren sabuwar shekara

    Hari kan Ukraine

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Masu aikin ceto kenan a Kyiv babban birnin Ukraine bayan wani harin Rasha a daren da ya gabata

    Rasha ta yi wa Ukraine ruwan wuta da jirage marasa matuƙa 111 a daren ranar sabuwar shekara.

    Sai dai rundunar sojin Ukraine ta ce ta kakkaɓo 63 daga cikinsu.

    Sojin Ukraine sun ƙara da cewa sauran jirage 46 ba su iya kaiwa wurin da aka aika su ba.

    Hare-haren sun faɗa kan yankuna akalla 10.

  16. Laraba ce 1 ga watan Rajab a Najeriya - Fadar sarkin Musulmi

    Sa'ad Abubukar III

    Asalin hoton, Sultanate Council Sokoto

    Fadar Sarkin Musulmi a Najeriya ta ayyana yau Laraba 1 ga watan Janairu a matsayin 1 ga watan Rajab na shekarar Hijira ta 1446.

    Wata sanarwa da Wazirin Sokoto Farfesa Sambo Wali ya fitar a daren da ya gabata ta ce Sarkin Musulmi Sa'ad Abubukar III ne ya bayyana hakan bayan ganin jaririn watan.

    Rajab shi ne wata na bakwai a kalandar Musulunci, wanda Hausawa ke yi wa laƙabi da watan Azumin Tsofaffi.

  17. Ya kamata Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji - NLC

    Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero

    Asalin hoton, NLC

    Bayanan hoto, Shugaban ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya, Joe Ajaero

    Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya, NLC ta buƙaci shugaban ƙasar, Bola Tinubu ya janye ƙudurin dokar haraji da ya gabatar ga majalisar dokokin ƙasar domin bayar da dama kan sake yin nazari.

    Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda shugabanta Joe Ajaero ya fitar a yau Laraba.

    Saƙon ya ce “domin samar da tsarin dimokuraɗiyya mai tabbatar da ci gaban ƙasa, dole ne mu gina tsari kan tubalin tattaunawa, da bai wa masu ruwa da tsaki damar tsoma baki a harkar gina ƙasa.

    “A kan haka ne muke sake yin kira ga gwamnatin tarayya da ta janye ƙudurin harajin da yanzu haka ke a gaban Majalisar dokoki domin bai wa duk ɓangarorin da suka dace bayar da gudumawa a kansa”.

    Sanarwar ta ce ƙungiyar, ita ma za ta so ta taimaka wajen samar da kyakkyawan tsarin haraji wanda zai samu karɓuwa a tsakanin al’umma, kuma ya taimaka wajen ci gaban ƙasa.

    Batun ƙudurin harajin da Tinubu ya gabatar, na daga cikin manyan sauye-sauyen da sabon shugaban ƙasar ya bijiro da su tun bayan hawa mulki a shekara ta 2023.

    Sai dai ƙudurin harajin ya fuskanci turjiya daga ɓangarori da dama na ƙasar, ciki har da Majalisar tattalin arziƙi ta ƙasar, da gwamnoni da kuma ƙungiyoyi.

    Lamarin da ya tursasa wa Majalisar dokokin ƙasar jinkirta muhawara kan ƙudurin, yayin da shugaban ƙasar ya buƙaci ma’aikatar shari’a ta ƙasar ta haɗa hannu da majalisar domin warware ɓangarorin dokar da ake ganin su ne suka haifar da taƙaddama.

    Sai dai a tattaunawarsa da kafafen yaɗa labaru sa’ilin hutun ƙarshen shekara a birnin Legas, wadda ita ce ta farko tun bayan hawa kan mulki, Tinubu ya sha alwashin tabbatar da ganin sabuwar dokar harajin ta fara aiki.

  18. Wahalhalun 'yan Najeriya ba za su tashi a banza ba - Tinubu

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce wahalhalu da "sadaukarwar" da 'yan ƙasar suka yi ba su tashi a banza ba tun bayan hawa mulkinsa a watan Mayun 2023.

    Da yake bayani cikin saƙonsa na sabuwar shekara da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya ce sabuwar shekarar "za ta kusanta mu da kakkyawar Najeriya da muke ta hanƙoro".

    A cewarsa: "Gare ku 'yan ƙasa, sadaukarwar da kuka yi cikin wata 19 da suka wuce ba ta tashi a banza ba. Ina tabbatar muku cewa kuma ba za ta tashi a banza ba nan gaba. Mu ci gaba da aikin gina ƙasa tare."

    Tinubu ya kuma jaddada cewa gwamnatinsa za ta ƙara mayar da hankali wajen aiwatarwa da kuma "bijiro da sauye-sauyen da suka zama wajibi" domin haɓaka tattalin arzikin Najeriya.

  19. Senegal za ta kori duka dakarun ƙasashen waje a 2025

    Bassirou Diomaye Faye

    Asalin hoton, EPA

    Bayanan hoto, Bassirou Faye ya hau mulki a watan Afrilun da ya gabata bayan kayar da ɗantakarar jam'iyya mai mulki a watan Maris

    Shugaban Senegal Bassirou Diomaye Faye ya ce gwamnatinsa za ta kawo ƙarshen zaman dukkan sojojin ƙasar waje a ƙasar tasa da ke Afirka ta Yamma.

    Yayin wani jawabi na sabuwar shekara da ya yi ta talabijin ranar Talata, Faye ya ce ya bai wa ministan tsaro umarnin tsara sabon daftarin tsaro da kuma ƙawance, ciki har da kawo ƙarshen zaman dakarun ƙasashen waje a ƙarshen 2025.

    A ranar 28 ga watan Nuwamba, Faye ya sanar cewa zaman sojojin Faransa a Senegal bai dace da 'yancin ƙasar na cin gashin kanta ba.

    Sanarwar da Faye ya bayar ta zo daidai lokacin da ƙasashen Afirka da dama suka kori dakarun Faransa kuma suka koma ƙawance da Rasha.

    Faransa na da dakaru kusan 350 a Senegal.

  20. Zimbabwe ta haramta aiwatar da hukuncin kisa a ƙasar

    Emmerson

    Asalin hoton, Getty Images

    A hukumance ƙasar Zimbabwe ta kawo karshen yanke hukuncin kisa, bayan shugaba Emmerson Mnangagwa ya rattaɓa hannu kan dokar.

    A yanzu za a maye gurbin hukuncin kisa da zaman kaso na har abada, kuma mutane kusan 60 ne za su fara cin gajiyar dokar a ƙasar.

    An shafe gwamman shekaru ana ta kai ruwa rana kan batun hukuncin kisa, amma kotuna suka ci gaba da yanke hukuncin da suka haɗa da samun mutum da laifin kisan kai da cin amanar ƙasa da ayyukan ta'addanci.

    Kungiyar kare haƙƙin ɗan'adam ta Amnesty International ta yi maraba da wannan doka da ta ce mai cike da tarihi ce.