Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza

  1. Harin Isra'ila ya kashe mutum 73 a arewacin Gaza

    Hukumomi a Falasɗinu sun ce aƙalla mutane 73 ne aka kashe sakamakon harin da Isra'ila ta kai a yankin Beit Lahiya da ke arewacin Gaza.

    Sun bayyana cewa akwai mutane da dama da suka jikkata yayin da wasu ke maƙale a ƙarkashin ɓaraguzai.

    Hotunan da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna wani bene yana ci da wuta inda aka ce wani rukunin gidaje ne da ke ɗauke da mutane da dama.

    Isra'ila dai ta ce tana bincike kan rahotannin lamarin amma abin da ta gano zuwa yanzu shi ne alkaluman da Hamas ta wallafa ba gaskiya bane.

  2. Assalamu Alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Lahadi.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da kuma sauran sassan duniya.