Wane ne zai jagoranci Hamas bayan kisan Yahya Sinwar?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Bayan tabbatar da kisan shugaban Hamas a ranar Alhamis, wasu jami'an ƙungiyar Hamas biyu sun shaidawa BBC cewa nan ba da jimawa ba za a yi zaman zaɓen wanda zai gaji Yahya Sinwar a shugabancin ƙungiyar.

Jami'an sun ce mataimakin Sinwar, Khalil al-Hayya, wanda shi ne mafi girman muƙami a cikin jagororin ƙungiyar da ba a Gaza suke zaune ba, yana kan gaba a cikin waɗanda ake sa ran su zama shugaban Hamas.

Al-Hayya, wanda ke zaune a Qatar, shi ne ke jagorantar tawagar Hamas a zaman tattauna tsagaita wuta tsakanin ƙungiyar da Isra'ila, kuma ana masa kallon wanda ya fahimci halin da ake ciki a Gaza sosai, kuma yana da zurfin ilimi.

Jagororin Hamas za su ƙara taruwa domin zaɓen wanda zai gaji marigayi Sinwar, wanda ya karɓi shugabancin ƙungiyar watanni biyu da suka wuce, bayan kisan tsohon shugaban Hamas, Ismail Haniyeh a birnin Tehran.

Wani babban jami'in Hamas ya bayyana Sinwar a matsayin wanda ya tsara harin ranar 7 ga watan Oktoba da Hamas ta kai cikin Isra'ila, ya kuma jaddada cewa nadin shi shugabancin ƙungiyar a wancan lokacin, saƙon barazana ne ga Isra'ila.

Tun a watan Yuli ne tattaunawar tsagaita wuta ta tsaya cak, kuma da dama sun yi amanna cewa jagorancin Sinwar ne ya kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita wutar.

Duk da kisan Sinwar da aka yi, wani babban jami'in Hamas ya shaidawa BBC cewa matsayar ƙungiyar ba ta canza ba game da sharuɗɗan da za a cika kafin ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma sakin fursunonin da ta yi garkuwa da su.

Hamas na ci gaba da neman Isra'ila ta fice baki ɗaya daga Gaza da daina kai hare-hare, da bayar da damar shigar da kayan agaji da kuma gina wuraren da yaƙi ya ɗaiɗaita daga cikin sharuɗɗan tsagaita wuta, amma Isra'ila ta ƙi amincewa da su, ta kuma jajirce cewa dole sai Hmas ta miƙa wuya.

Da aka tambaye su game da kiran da firaiministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu ya yi na cewa su miƙa wuya, sai jami'an ƙungiyar Hamas suka ce ''abu ne da ba zai yiwu ba mu miƙa wuya''.

Sun ƙara da cewa ''Mu na faɗa ne domin ƙwatar wa jama'armu ƴanci, don haka ba zamu miƙa wuya ba. Za mu yi yaƙi har zuwa lokacin da harsashi zai ƙare kuma har sai an ƙarar da mu baki ɗaya, kamar yadda aka kashe Sinwar.''

Kisan Sinwar na daga cikin munanan koma baya da ƙungiyar ta samu a cikin gomman shekaru. Kuma duk da ƙalubalen da ke aban ta na neman wanda zai gaje shi, Hamas ta saba jure matsalar rashin shugabanni tun daga 1990.

Isra'ila ta samu nasarar kashe mafi yawan shugabannin Hamas da kuma waɗanda suka kafa ta, amma duk da haka ƙungiyar ta jajirce wajen turjiya da kuma sake naɗa wasu sabbi a ko da yaushe.

Yayin da ake cikin wannan rikici, ana ci gaba da tambayar ko ina ƴan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su suke, kuma wa ye zai ɗauki alhakin ceto su.

Ana ganin cewa Mohammed Sinwar, ɗan uwan Yahya Sinwar ya cancanta ya jagoranci ƙungiyar. Ana ma zaton shi ne jagoran mayaƙan ƙungiyar a a yanzu, wanda kuma ake ganin zai bayar da gudunmuwa wajen tafiyar da Hamas a Gaza, nan gaba.

Yayin da Hamas ke ƙoƙarin zaɓen shugabanta, ana ci gaba da gwabza yaki a Gaza.

A ranar Asabar an kashe gomman mutane a sansanin Jabalia da ke arewacin Gaza, yayin da dakarun Isra'ila suka ƙara ƙaimi wajen buɗe wuta a kan wuraren da suka ce mayaƙan Hamas na sake taruwa.