Rufewa
Masu bin shafin namu, nan kuma muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da kawo maku rahotannin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/10/2024
Ahmad Bawage da Abdullahi Bello Diginza
Masu bin shafin namu, nan kuma muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin a yau.
Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu
Sojojin Isra'ila sun ce an kashe wani kwamandan da ke tuka wata tankar yaki a arewacin Gaza.
Rahotanni sun bayyana cewa tankar da Kanal Ehsan Daqsa ke ciki ce ta daki wani abin fashewa lokacin da suke kai hare-hare a Jabaliya.
Shi ne babban jami'in sojin Isra'ila da aka kashe a yakin da ake yi da Hamas.
A wani labarin kuma hukumar lafiyar Hamas da ke Gaza ta ce aƙalla mutum 87 suka mutu ko suka ɓace bayan wani hari da sojojin Isra'ila suka kai garin Beit Lahiya cikin dare.
Waɗanda suka shaida abin da ya faru sun ce lamarin ya fi kama da girgizar ƙasa, ma'aikatar lafiyar Hamas ta ce Falasdinawa 87 ne suka mutu a harin, kuma har yanzu ba a gama zaƙulo gawawwakin mutanen ba.
Masar ta ayyana yaƙar cutar Maleriya a faɗin ƙasar, bayan kusan ƙarni guda da ƙaddamar da yaƙi da cutar - wadda ta kasance ɗaya daga cikin cutuka mafiya kisa a duniya.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya, WHO Dakta Tedros Adhanom Ghebreyesus ya ce a yanzu cutar Maleriya a Masar ta zama tarihi.
Cutar Maliya ta fara ɓulla a Masar kusan shekara 6,000 da suka gabata.
Dakta Ghebreyesus ya yaba wa aniyar gwamnati da mutanen Masar ta ƙudurce yaƙar cutar daga faɗin ƙasar.
Akan bai wa ƙasa shaidar rabuwa da cuta idan aka tabbatar cewa ba a samu kamuwa da cutar a cikin ƙasar ba cikin shekara uku a jere .
Cutar Maleriya na kashe fiye da mutum 600,000 a kowace shekara, galibinsu a ƙasashen Afirka.
Yahya Sinwar ya zama shugaban ƙugiyar baki ɗaya bayan kisan Ismail Haniyeh a birnin Tehran cikin watan Yuli cikin wannan shekara.
Sinwar - wanda aka haifa Zirin Gaza a 1962 - ya shiga ƙungiyar Hamas tun yana matashi.
Shi ne ya kafa sashen tsaro na ƙungiyar, da aka fi sani da Majd, wanda ya dinga lura da sha'anin tsaron ƙungiyar, da binciken waɗanda ake zargi da zama jakadun Isra'ila, tare da kama jami'an leƙe asirin Isra'ila da sauran jami'an tsaronta.
Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya, sun bayar da tallafin naira miliyan 50 kowanensu don tallafa wa iyalai da waɗanda hatsarin fashewar tankar mai ta shafa a jihar Jigawa..
Shugaban ƙungiyar gwamnonin, wanda shi ne gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ne ya bayyana haka a birnin Dutse a lokacin ziyarar ƙungiyar, kamar yadda gidan talbijin na ƙasar NTA ya ruwaito.
A ranar Talatar da ta gabata ne akwa samu fashewar tankar mai a garin Majiya da ke yankin ƙaramar hukumar Taura a jihar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar fiye da mutum 170, tare da jikkatar gommai.
Gwamnan na Gombe ya ce shi da takwarorin nasa sun bayar da tallafin ne domin taimaka wa iyalai waɗanda suka mutu, da kuma waɗanda ke kwance a asibiti suna karɓar magani.
“Wannan bala'i ya shafe mu gaba ɗaya , don haka dole ne mu agaza wa gwamnatin Jigawa a wannan mawuyacin yanayi da take ciki'', in ji gwamnan na Gombe.
Tawagar gwamnonin da suka je ziyarar jajen sun haɗa da gwaman jihar Bauchi, Bala Mohammed da mataimakann gwamnonin jihohin Borno da Katsina da Taraba da Kebbi da kuma jihar Yobe States.
Dakarun sojin Sudan - da ke fafata yaƙin basasa da mayaƙan RSF masu sanye da kayan sarki - sun ce wani babban kwamandan RSF ɗin ya miƙa wuya.
Sojojin sun ce Abuagla Keikal - shugaban dakarun RSF na jihar Gezira, da ke kudu maso gabashin Khartoum - ya miƙa wuya tare da wasu dakarunsa masu yawa.
Kawo yanzu babu wani martani daga rundunar RSF ɗin a hukumance.
An yi ta yaɗa wani hoto a shafin intanet, da ke nuna kwamandan lokacin da yake miƙa wuyar, to amma babu wata sanarwa da ke tabbatar da iƙirarin sojojin daga ɓangaren Keikal ɗin.
A baya sojojin Sudan da dakarun RSF sun riƙe mulkin ƙasar a tsakaninsu, bayan da suka haɗa kai wajen yin juyin mulki shekara uku da suka wuce, to amma ƙawancen nasu ya samu tangarɗa a watan Afrilun shekarar da ta gabata.
A kudancin Gaza, an yi wa ƙananan yara 'yan ƙasa da shekara 10 fiye da 145,000 allurar riga-kafin polio a ranar Asabar, kamar yadda sashen da ke lura da ayyukan gwamnatin Isra'ila wasu yankunan (Cogat).
Cogat, wanda cibiyar soji ne da ke lura da shiga Gaza, ya ce gangamin riga-kafin - wadda ake yi ƙarƙashin kulawar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO da Unicef zai ci gaba a yau zuwa gobe.
Zagayen farko na riga-kafin an gudanar da shi cikin watan Satumba, bayan rahotonnin ɓullar cutar a Gaza karon farko cikin shekara 25 a jikin wani jariri mai wata 10 da har cutar ta sanya masa shanyewar ɓarin jiki.
Manufar gangamin riga-kafin shi ne yi wa yara kimanin 640,000 'yan kasa da shekara 10, kamar yadda WHO ta bayyana.
Hukumar asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano da ke Kano ya ɓullo da sashen kula da tsofaffi a Asibitin.
Shugaban sashen Farfesa Ibrahim D Gezawa, ya ce an keɓe sashen ne domin bai wa tsofaffi kulawar da ta dace, saboda yadda matsalolinsu suka sha bamban da sauran mutanen da ba su tsufa ba.
''Sashen ya ƙushi abubuwa biyu, na farko sashen kula da su domin ba su maganin da suke buƙata, sai kuma sashen kwantar da tsofaffin idan buƙatar hakan ta taso'', kamar yassa ya yi bayani
Sojojin Isra'ila sun ce an harba kusan rokoki 70 zuwa cikin ƙasar daga Lebanon ƙasa da mintoci kaɗan.
Na'urorin tsaron sama na Isra'ila sun kakkaɓo wasu daga cikin rokokin, in ji sojojin a wata sanarwa a shafin X.
"Bayan ƙara jiniya tsakanin karfe 11:09 zuwa 11:12 na safe, an harba rokoki sama da 70 zuwa yankin Galilee daga Lebanon," in ji sojojin.
Ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam ta duniya, Amnesty International ta yi Alla-wadai da kama wasu matasa da suka fita don tun waɗanda aka kashe lokacin zanga-zangar EndSars.
Jami'an ƴansanda sun yi dirar miƙiya kan matasan waɗanda suka taru a Lekki toll gate yau Lahadi.
Matasan sun ce sun fita domin tuna mutanen da aka kashe a watan Oktoban 2020 lokacin zanga-zangar adawa da cin zalin ƴansandan Sars.
An ruwaito cewa matasan sun taru ne da misalin karfe 8 na safe a Lekki toll gate riƙe alluna da kuma kwalaye ɗauke da rubuce-rubuce da dama.
Wata sanarwa da ƙungiyar Amnesty ta fitar, ta ce ba za a lamunci abin da jami'an ƴansandan jihar Legas suka yi ba.
"Muna Allah-wadai da kakkausar murya kan abin da ƴansandan Najeriya suka yi kan mutanen da suka fita a Lekki toll gate domin tunawa da masu zanga-zangar lumana da aka kashe yayin zanga-zangar EndSars a Oktoban 2020. Ba za mu amince da amfani da hayaki mai sa hawaye ba da kuma kame," in ji ƙungiyar ta Amnesty a wani sako da ta wallafa a shafin X.
Ma'aikatar lafiya karkashin ikon Hamas a Gaza ta ce an kashe mutum 84 tare da jikkata wasu 158 cikin sa'o'i 24 da suka wuce.
Aƙalla Falasɗinawa 42,603 aka kashe sannan 99,795 suka jikkata, tun bayan da Isra'ila ta kaddamar da farmaki kan Gaza ranar 7 ga watan Oktoban bara, a cewar ma'aikatar ta lafiya.
har yanzu ana ci gaba da garkuwa da mutum aƙalla 100 a Gaza.
A farkon makon nan ne Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce za a ci gaba faɗa har sai an sake sauran Isra'ilawa da ake garkuwa da su.
Shugaban Cuba, Miguel Diaz-Canel, ya yi gargaɗin cewa akwai yiwuwar tsibirin zai fuskanci wata gagarumar guguwa a yau Lahadi.
A halin da ake ciki dai babu wutar lantarki a tsibirin bayan matsalar da aka samu da babbar tashar lantarki ta ƙasar.
Gabashin Cuba dai na shirin fuskantar iskar da gudunta ya zarce kilomita 130 da kuma mamamkon ruwan sama.
Mista Diaz-Canel ya ce tuni hukumomi suka dukufa wajen shirin kare rayuka.
Mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima zai jagoranci tawagar ƙasar da za ta wakilci shugaba Bola Tinubu a wajen taron ƙasashe renon Ingila wato CHOGM 2024.
Shettima zai bi sahun Sarki Charles na Ingila da sauran shugabannin ƙasashen duniya daga mambobi 56 a taron wanda shi ne irinsa na farko da za a yi a Apia, da ke tsibirin Samoa daga 21 zuwa 26 na watan Oktoba.
Wata sanarwa da mai taimakawa Shettima kan harkokin yaɗa labarai Stanley Nkwocha, ya fitar, ta ce shugabannin da za su halarci taron za su mayar da hankali kan "Manufar samar da makoma ɗaya kuma mai kyau tsakanin mambobin ƙasashe."
Taken taron na bana zai mayar da hankali kan yadda mambobin ƙasashen na renon Ingila za su karfafa gwiwar juna wajen samar da ci gaba a wannan lokaci.
Sanarwar ta ƙara da cewa Najeriya da sauran ƙasashe za su kuma zaɓi sabon sakatare-janar na ƙasashen na renon Ingila yayin taron.
Ana sa ran mataimakin shugaban ƙasar zai yi amfani da damar wajen janyo hankalin masu zuba jari zuwa Najeriya.
Wani likita a arewacin Gaza ya roki da a dakatar da kai hare-hare kan asibitoci "kafin lokaci ya kure".
Dr Eid Sabbah, darektan asibitin Kamal Adwan, ya ce hare-haren da Isra'ila ta kai a Beit Lahia, ya lalata gine-gine da dama.
Hare-haren sun afka wa wasu gidaje, in ji Dr Sabbah, a tsakanin shatale-talen Abu Jidian da masallacin Al Qassam.
Dr Sabbah ya ƙara da cewa an kashe gomman mutane tare da jikkata wasu da dama, "wasu daga cikinsu sun isa asibiti, wasu kuma suna karkashin ɓaraguzan gine-gine".
Ya yi kira da a kawo karshen "ƙawanyar" da ake yi wa asibitoci a arewacin Gaza "domin rayuwa ta koma daidai...kafin lokaci ya kure, kafin a halaka al'ummarmu baki-ɗaya".
A safiyar yau Lahadi Isra'ila ta kai sabbin hare-hare kan Beirut, babban birnin Lebanon.
Ga wasu hotuna da ke fitowa daga birnin na irin ɓarnar da hare-haren suka yi.
Ma'aikatar lafiya a Gaza karkashin ikon ƙungiyar Hamas ta ce aƙalla mutum 87 ne aka kashe yayin da wasu fiye da 40 suka jikkata a harin da Isra'ila ta kai a Beit Lahia.
Bayanai da ma'aikatar ta fitar ta ce wasu da dama na karkashin ɓaraguzai, kuma motocin ɗaukar marasa lafiya na fuskantar wahala wajen kai wa wurin.
A daren Asabar, hukumomin Hamas suka ce aƙalla mutane 73 ne suka mutu a tashin bama-bamai.
Isra'ila ta ce tana duba rahotannin asarar rayuka, amma ta yi imanin alkaluman da hukumomin Hamas suka wallafa ba gaskiya bane kuma bai yi daidai da bayanan da sojojinta ke da su ba.
Hukumar zaɓen jihar Kogi ta ayyana jam'iyyar APC mai mulkin jihar a matsayin wadda ta lashe zaɓen duka shugabannin ƙananan hukumomin jihar 21 da kuma na kansiloli 239 da aka gudanar a ranar Asabar.
Shugaban hukumar zaɓen jihar, Mamman Nda-Eric wanda ya ayyana haka, ya ce zaɓen ya gudana cikin gaskiya da adalci ba.
Gwamnan jihar ta Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓen da kuma ƴan jihar da suka kasance cikin tsanaki tare da zaɓar abin da suke so ba tare da nuna bambancin jam'iyya ba.
Sai dai jam'iyyu adawa a jihar irinsu PDP da CNPP sun yi zargin cewa abin da aka yi a matsayin zaɓe, abin kunya ne ga dimokraɗiyya.
Sun ce ba a gudanar da wani zaɓe ba a jihar, inda suka ce hukumar zaɓen jihar ta sake nuna gazawarta wajen shirya sahihin zaɓe.
A yau Lahadi al'ummar Moldova ke kaɗa kuri'a a zaɓen shugaban ƙasar mai matukar muhimmanci da kuma kuri'ar raba gardama kan hanyar shiga ƙungiyar tarayyar Turai.
Shugaba mai ci Maia Sandu wanda ke da muradin ƙungiyar na fatan lashe wa'adi na biyu, amma tana fuskantar ƙalubale daga wasu ƴan takara goma.
Zaɓen dai na fuskantar zarge-zargen katsalandan daga gwamnatin Rasha.
Babbar mai shigar da ƙara kan yaƙi da cin hanci Veronica Dragalin ta ce tana fargabar cewa an biya kusan kashi goma cikin ɗari na al'umma kan su ki amincewa da shiga ƙungiyar ta EU.
Ta ce: ''Ba ni da labarin wasu wurare da aka fito karara ake nuna cewa ana son a yi katsalandan cikin harkar zaɓe irin wannan, yaƙi da wannan lamari zai yi wuya.''
Jiragen yaƙin Isra'ila sun sake kai hare-hare a yankunan kudancin birnin Beirut na ƙasar Lebanon a safiyar yau Lahadi.
Wannan dai shi ne karo na biyu da Isra'ila ke kai hari tun bayan da wani jirgi mara matuki ya kai hari gidan Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a ranar Asabar.
Hezbollah dai ba ta ɗauki alhakin kai harin ba.
Mista natanyahu ya sha alwashin cewa Iran da wakilanta za su ɗanɗana kuɗarsu, kuma ƴan sa'o'i kaɗan bayan haka Israila ta fara luguden wuta a Lebanon.
Har yanzu Isra'ila ba ta mayar da martani kan Iran ba, bayan harin maƙamai masu linzami da ta kai mata a farkon wannan watan.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya koma birnin Abuja bayan hutu zuwa Birtaniya.
Shugaban ya sauka a Filin Jiragen Sama na Nnamdi Azikiwe International da yammacin ranar Asabar.
A ranar 3 ga watan Oktoba ne shugaban ya tafi Birtaniya domin yin hutun mako biyu.
Tinubu ya samu tarba daga manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da shugaban jam'iyyar APC ta ƙasa Abdullahi Ganduje da shugaban ma'aikata na fadarsa Femi Gbajabiamila da mai ba shi shawara kan harkar tsaro Malam Nuhu Ribadu da gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu da sauransu.
Shugaba Tinunu ya zarce zuwa ƙasar Faransa daga Birtaniya ranar 11 ga watan Oktoba domin domin halartar wasu al’aumara, kamar yadda babban mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Masari ya bayyana.
Komawar Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da mataimakinsa Kashim Shettima ya fice daga ƙasar ranar Laraba zuwa ƙasar Sweden domin halartar wasu tarukan ƙulla alaƙar ci gaban kasuwaci da wasu yarjejeniyoyi a tsakanin ƙasashen biyu.
Mutane da dama dai sun yi ta sukar balaguron shugaban da mataimakinsa, inda ake ganin ganin cewa an bar ƙasar babu shugabanci.