Kamfanin rarraba wutar lantarki na AEDC ya kori ma'aikata 800

Asalin hoton, TCN
Kamfanin rarraba wutar lantarki na Abuja ya kori ma'aikatansa 800, a daidai lokacin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar da matsalar wutar lantarki da tsadar rayuwa.
Jaridar Punch a Najeriya ta ruwaito cewa AEDC ya ɗauki matakin ne a wani ɓangare na sake fasalin kamfanin, da ke bai wa birnin Abuja da jihohin Nasarawa da Neja da Kogi wutar lantarki.
Bayanai sun ce tun da farko kamfanin ya sanar da korar ma'aitaka 1,800 ne kafin daga bisani ya rage su zuwa 800, bayan jerin tattaunawa da ƙungiyoyin ma'aikatan lantarki da sauran masu ruwa da tsaki a ƙasar.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar tsadar wutar lantarki da rashin wutar a wasu wurare a faɗin ƙasar.

