Gwamnatin Sokoto ta bayar da bashin babura da masu ƙafa uku
Gwamnatin jihar Sokoto ta bayar da bashin babura a farashi mai rahusa ga wasu matasan jihar domin sauƙaƙa wa al'ummar jihar.
Mataimakin gwamnan jihar, Injiniya Idris Gobir ne ya bayyana haka lokacin bikin bayar da baburan da aka gudanar ranar Asabar a birnin Sokoto.
Mashinan - da suka ƙunshi babura 1,000 da masu ƙafa uku su 500 - an bayar da su ne a farashi mai rahusa na ragin kashi 80 cikin 100 kan asalin farashinsu, a cewar mataimakin gwamnan.
Injiniya Gobir ya ce shirin na daga cikin manufofin gwamnatin Sokoto na samar da ayyukan yi da sauƙaƙa wa al'umma rayuwa.
Ya ƙara da cewa an sayi kowane babu a kan kuɗi naira miliyan 1.3 yayin da kowane mai ƙafa uku aka saye shi a kan naira miliyan 3.6, amma aka karyar da farashinsa domin taimaka wa matasan da suka amfana da tsarin.
“Su waɗanan masu ƙafa uku mun ba ku su a kan naira miliyan ɗaya, yayain da su kuma babauran muka ba ku su a kan naira 300,000, bayan biyan kuɗin kafin-alƙalami na naira 150,000 ga kowane mai ƙafa uku, da kuma naira 50,000 ga kowane babur'', in ji mataimakin gwamnan.
Ya ƙara da cewa waɗanda suka amfana da babura masu ƙafa uku za su riƙa biyan naira 15,000 a kowane wata, yayin da waɗanda suka karɓi babura za su riƙa biyan naira 5,000 a kowane wata.
Haka kuma mataimakin gwamnan ya buƙaci matasan da suka amfanan su faɗaɗa tallafin zuwa ga fasinjojin da za su ɗauka da baburan nasu, ta yadda su ma al'ummar gari za su ji tallafin a jikinsu.
“An ba ku waɗannan babura ne domin amfanin al’umma, kada ku sayar da su, kuma kada ku yi wa mutane tsada. Idan masu karɓar bashin babur ta hanyar biyan naira 90,000 a matsayin kuɗin kafin-alƙalami, na karɓar naira 100 a hannun fasinja, muna sa ran ku ku riƙa karɓar naira 20 zuwa 40, ya danganta da nisan wurin da za ku kai su'', in ji Injiniya Gobir.