Bai kamata jagororin arewa su riƙa tsoma baki a fitar da yan takara ba - kwankwaso

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana rashin jin dadinsa, kan yadda wasu da ya kira ''Tsiraru, da ke bayyana kansu a matsayin jagororin Arewa'' ke tsoma kansu wajen fitar da ƴan takara musamman a zaɓen shugaban ƙasa, da sunan shi ne yake wakiltar yankin.

Tsohon gwamnan ya ce wannan na janyo raba kan al'umma, da kuma kawo cikas ga dimukradiyya, da uwa uba zaɓar shugabannin da basu cancanta ba.

Yayin wata hira da sashen Hausa na BBC, Kwankwaso, ya ce ya kamata abubuwan da suka faru a zaɓukan baya su zamarwa jagororin izina, su tsame kansu daga duk wani abu da ya shafi fitar da ƴan takara, da kuma yi wa jama'a ƙarfa-ƙarfa.

''Wannan abu da suke yi na zalunci na haifar da tarnaki a tsakanin al'umma, duk abun da za ka yi ka yi shi bisa kan gaskiya, bai kamata a ce dattawan nan da wasu daga cikinsu iyayenmu ne wasu yayyanta, musamman a yankin nan na Arewa masu yamma, su riƙa nuna son rai wajen fitar da ƴan takara ba'' inji shi.

Ya ƙara da cewa ''Yawanci suna zuwa su kitsa kƙarya, su tara jama'a suna gaya musu cewa Arewa ta yarda ga ƴan takararta, kuma dukka mutanen nan ba su wuce biyu ko uku ba, amma sai ka ga mutum ya je yana faɗar ƙarya, a maimakon su tafi Fatakwal ko su tafi Abuja su je su tallata mu da muke ƴaƴansu, amma sai su je suna nuna son rai.

Ya bayar da misali da zaɓen 2019, da ƴan takara guda bakwai suka fito daga Arewa maso yamma, inda ya ce ''In ma tsohon gwamna kake s akwai, in tsohon minista ne akwai, in dogo ko gajere kake so akwai, amma daga ƙarshe haka aka je aka zubar da mu aka yi abun da ake so''

Babu yarjejeniyar karɓa-karɓa a tsakanina da Atiku

A hirar ta sa da BBC Hausa, tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta raɗe-raɗin da ke cewa an cimma yarjejeniya tsakaninsa da tsofaffin ƴan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyun hamayyar ƙasar - Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP - kan cewa kowannensu zai yi mulki na wani wa'adi.

Ya ce bai san da maganar ba, amma ya samu labarin cewa ɓangaren Atikun na ta "yin taruka da shugabannin yankin ciki har da malamai, suna faɗa masu wannan magana".

Tsohon gwamnan na Kano ya ce ''Wannan magana ta ƙona mani rai matuka, a ce dattawa suna ƙarya, suna faɗar abun da ba a yi ba, an faɗa min an tara kusan malamai arba'in da biyar ana gaya masu wannan magana wacce babu ita, ko kaɗan ban ji daɗin wannan abu ba'' in ji tsohon dan takarar shugaban ƙasar na jam'iyyar NNPP.

Ya kara da cewa ''An gaya musu wai na amince cewa Atiku zai yi shekara hudu, nima zan yi hudu, shi kuma Peter Obi ya yi shekara takwas, wannan maganar babu ita, ba a yi ta ba'' in ji Kwankwaso.