Fitattun litattafan labaran Hausa a 2024

    • Marubuci, Ameera Souley
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Gwarzuwar Hikayata 2022
    • Aiko rahoto daga, Maradi
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Labaran zube ɗaya ne daga cikin ginshiƙan adabin Hausa.

Kuma duk da cewa akalar rubutan labaran Hausa, wanda ake yi wa laƙabi da 'adabin kasuwar Kano ta fi karkata ga ɓangaren shafukan sada zumunta sanadiyyar ci gaban zamani, amma har yanzu akwai marubuta da kan ƙuƙuta su wallafa litattafan da suka rubuta.

Yayin da muka shigo shekara ta 2025, mun yi waiwaye domin duba irin waɗannan labarai da aka fi karantawa a ƙasar Hausa cikin shekara ta 2024.

Labaran sun ƙunshi wadanda ake karantawa a shafukan sada zumunta da kuma waɗanda aka wallafa kamar yadda aka saba a al'ada.

'Furen ƙarya'

Bikin Baje-kolin Littattafai da Fasahohin Hausawa (HIBAF), wanda kamfanin Open Arts yake gudanarwa duk shekara, ya samar da wata kafa ta bunƙasa rubutun gajerun labaran Hausa.

A taron na shekarar 2021 wanda aka gudanar a garin Kaduna a ranakun 21 zuwa 23 ga watan Oktoban 2021, an horas da wasu marubuta masu tasowa, inda suka samar da gajerun labarai guda 18, waɗanda suka tayar da littafin Furen Ƙarya, a ƙarƙashin jagorancin Farfesa Ibrahim Malumfashi.

Sai dai littafin bai fito kasuwa ba sai a watan Disamba na shekarar 2023. Kuma littafin ya yi fice sosai a shekarar 2024, musamman yadda aka yi ta tafka muhawara kansa a kafar sadarwa ta Facebook, tare da babban editan littafin, Farfesa Ibrahim Malumfashi.

Labaran da ke cikin littafin suna ɗauke da jigogi mabambanta.

'Amani' na Sumayya Abdulkadir (Takori)

Amani, labari ne a kan wata yarinya mai suna Amani, wadda ta kasance tana da gurɓatacciyar ɗabi'a ta alfahari, girman kai da fariya da dukiyar da mahaifinta ya tara da sunanta.

Shigowar wani nagartaccen saurayi a duniyar Amani ya canza dukkan takunta, ya rugurguza mummunar ɗabi'arta, ta alfahari da ɗagawa, zuwa wata abar daban da tunanin Amani da duk wanda ya san ta bai taɓa tsammani ba.

Labarin AMANI ya ƙayatu da kyan tsari wajen saƙa zaren labarin, inda aka gina shi a kan masarautar Tubawa ta garin Diffa, ƙasar Nijar.

'Abin cikin ƙwai'

Abin Cikin Ƙwai, littafi ne mai ɗauke da nagartattun gajerun labarai guda hamsin da ɗaya na mabambantan marubuta; talatin da uku na gasar da aka sanya ce a ƙarƙashin jagorancin zauren Marubutan da ke WhatsApp a shekarar 2024 a kan jigon bincike, yayin da sauran suka zamo gwarazan labarai na gasar wata-wata da ake yi a zauren.

Littafin yana ɗauke da labarai masu tarin darusssa, faɗakarwa, ilimantarwa har ma da nishaɗantarwa, a cikin mabambantan jigogi na halin da al'umma take ciki a yau.

Editocin littafin su ne:

  • Yusif Yahaya Gumel
  • Nura Isma'il
  • Nana Aisha Hamissou
  • Amrah Auwal Mashi.

'Husufin farin ciki' na Ado Bala

An tsara labarai masu garɗin gaske a wannan littafin. Husufin Farin Ciki, diwanin gajerun labarai ne masu ma'ana, a kan jigogi daban-daban, cikin salon rubutun Hausa na zamani, irin wanda zai sanya makaranci ya sake yin tunani a kan wasu matsaloli na rayuwa da ya yi imani da su.

Dukkan labaran suna bisa gwadaben ilmantarwa, nishaɗantarwa da kuma faɗakarwa.

Kowanne labari zaman kansa yake yi, don haka kowanne irin tarin bajintar da aka nuna a ciki ta isa a yi jinjina.

'Wasa da rayuwa' na Zainab Abdullahi

Littafin Wasa da Rayuwa wanda marubuciya Zainab da aka fi sani da Laila ta rubuta, ɗaya ne daga cikin litattafai uku da suka sami nasara a gasar rubutu ta Gusau Institute ta shekarar 2024.

Littafin ya bayar da labarin irin halin da yankin Arewa-maso-yamma yake ciki, na masu garkuwa da mutane da kuma hakaito abubuwan da suka haifar da wannan matsala.

Littafin ya yi shuhura kuma ya haifar da mahawara sosai sakamakon yadda matsalar take ci wa al'umma tuwo-a-ƙwarya.

Babu shakka littafin ya cancanci a sanya shi cikin jerin litattafan da za a riƙa nazari idan an zo batun da ya shafi matsalolin tsaro a ƙasashen Afirka ta yamma.

'Ɗaukar jinka'

A shekarar 2022 Gidauniyar Arc. Ahmed Musa Ɗangiwa ta sake sanya wata gasa ta biyu domin rubutun gajerun labaran Hausa a kan matsalolin matasa, musamman abin da ya shafi taɓarɓarewar tarbiyya da zaman kashe-wando da ɗaukar makami da kuma safara da shaye-shayen kayan maye.

Wannan gasar ta samar da littafin gajerun labaran Hausa wanda aka sanya wa suna Ɗaukar Jinka.

Littafi ne da yake ɗauke da gajerun labarai 15. Littafin ya kasance wanda ake amfani da shi a makarantun Sakandire na jihar Katsina da wasu manyan makarantu a Najeriya.

Editocin labaran su ne:

  • Abdurrahman Aliyu
  • Mujaheed Abdullahi
  • Yazid Abdul'aziz
  • Jibril Yusuf

'Tauraruwa' na Nafisa Auwal Ƙaura Goje

Tauraruwa labari ne a kan wata matashiya mai suna Zaitun, wadda take da ƙulafucin ɗaukaka da shahara ko ta wacce hanya.

Zaitun ta sami ɗaukakar ta ne ta sanadin wani rubutu da ta yi a Facebook, a ƙoƙarin fusata tsohon saurayinta.

Sai dai hoton da ta yi amfani da shi ya kasance na wani riƙaƙƙen ɗan ta'addan ƙasar Nijar ne da aka sanar da mutuwarshi, sai ga shi Zaitun ta farfaɗo da tarihinsa har hakan ya yi sanadin rasa rayukan al'umma.

Zaitun ta sami ɗaukaka fiye da yadda ta yi fata, amma hakan ya kusan tafiyar da rayuwarta.

Daga ƙarshe ta gane kuskuren ta na bijire wa maganar iyaye da kafewa kan wata buƙata maras ma'ana.

'Shu'umar masarauta' na Aisha Adam Hussain

Littafin Shu'umar Masarauta ƙirƙirarren labari ne da aka gina shi a kan masarautu biyu masu ɗauke da mabambantan jinsi, wato jinsin aljanu da na mutane, yayin da suke wanzar da mulki a muhalli ɗaya.

Labarin ƙunshe yake da tsagwaron baƙaƙen makirce-makircen masarauta haɗe da tarin darussa, duba da tsagwaron zalunci da cin amanar da aka ƙulla a ciki.

Daga ƙarshe, labarin yana nusar da al'umma su san duk faɗin gona tana da kunyar ƙarshe, don haka duk irin shukar da mutum ya yi da hannunsa, to ita zai girba, walau mai kyau ko akasin ta.

'Rai da ƙaddara' na Lubna Sufyan

Labari ne a kan ahali guda, ahalin Malam Datti. Wani mutum mai son aibata yaran kowa da jifar su da munanan kalmomi.

Labarin ya yi duba a kan yadda 'ya'ya, har da ma jikoki za su iya biyan bashin zunubin mutum ɗaya, duk da kowanne rai da tashi ƙaddarar.

Labarin ya nuna wa al'umma illar fariya da jin cewa kai fa ka fi ƙarfin aikata mummunan aiki, haka ma ahalinka sun fi ƙarfin aikata ba dai-dai ba, don an ce kyakkyawar magana ma sadaka ce.

'Kwasar ganima' na Fauziyya D. Suleiman

Littafin yana ƙunshe da gajerun labarai guda 25 waɗanda aka yi amfani da mabambanta jigogi wajen samar da su.

Labaran sun hasko rayuwar talakawa a ƙasar Hausa a wannan zamani. Ban da rayuwar duniya, har wani sashe na lahira sai da marubuciyar ta nuno.

Wata nasara ta wannan littafi a fagen adabin Hausa ita ce, yana cikin ƙalilan da aka samu cewar mace ta wallafa littafi mai ɗauke da gajerun labarai a Hausa.

Littafin ya yi shuhura sosai ta yadda yara da manya kowa zai iya karanta shi.