Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Shugaba Biden ya jaddada goyon bayan Amurka ga Isra'ila kan harin Iran

    Shugaban Amurka Joe Biden ya jadadda goyon bayan Amurka ga Isra'ila bayan Iran ta kai mata hari da makamai masu linzami.

    Ya bayyana harin na Iran a matsayin wanda aka tare kuma bai yi tasiri ba.

    Mista Biden ya bayyana cewa sojojin Amurka sun yi aiki da Isra'ila kan kakkaɓo makaman na Iran.

    Wata sanarwa daga Ofishin Firaministan Burtaniya na cewa Sir Keir Starmer ya tattauna da shugaban gwamnatin Jamus, Olaf Scholz, da wasu shugabanni ƙasashe biyu - manyan ƙawayen Isra'ila - da suka yi alla-wadai da harin Iran.

    Faransa a Japan suma sun nuna rashin jin daɗinsu. Sai dai kuma sun buƙaci ɓangarorin biyu su dakatar da wannan tashin hankali.

  2. Jaridar Daily Trust ta bayar da haƙuri kan labarin yarjejeniyar SAMOA

    Jaridar Daily Trust ta bayar da haƙuri kan labarin da ta yi na yarjejeniyar Samoa, wanda ya tayar da ƙura.

    A wata sanarwa da ta fitar, mai taken, Yarjejeniyar Samoa: Muna bayar da haƙuri, ta ce, "A jaridarmu ta 4 ga Yulin 2024, babban labarinmu mai taken, "LGBT: Najeriya ta shiga yarjejeniyar biliyan $150 da Samoa", labarin ya tayar da ƙura a faɗin ƙasar. Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban hukumar sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da jaridu wato National Media Complaints Commission (NMCC), wanda aka fi sani da Ombudsman."

    Sanarwar ta ƙara da cewa "bayan sauraron kowane ɓangare, NMCC ta gano cewa akwai kura-kurai a labarin, sannan an kauce daga wasu ƙa'idojin aikin jarida waɗanda ya kamata kowace jarida ta kiyaye.

    Mun amince da wannan matsaya ta NMCC. Muna ba gwamnatin tarayya haƙuri, sannan muna ba masu karanta jaridunmu da dukkan sauran mutane haƙuri bisa kuskuren da muka yi."

    Dangane kuma da hanyoyin da jaridar ke bi wajen tantance labaranta, jaridar ta ce "hanyoyin da muke bi wajen tantance labari suna da inganci, kuma sun taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu na sama da shekara 25. Amma duk da haka, bayan wannan kuskuren, mun sake dubawa tare da inganta su.

    "A matsayinmu na gidan jarida, burinmu shi ne samar da labarai masu inganci da samar da haɗin kan ƙasa da tsaronta da kuma tabbatar da cigabanta. Muna yin hakan ne ta hanyar fitar da labarai da za su taimaka wa mutane wajen fahimtar duniya da kuma bayar da damar tafka muhawara da kuma bin diddigin harkokin shugabanci.

    Daga ƙarshe jaridar ta sanar da cewa ba ta yi labarin ba da nufin nuna hamayya ga wata gwamnati "ba ma goyon baya, ko kuma adawa da kowace gwamnati ko jam'iyya, ko ɗaiɗaikun mutum. Burinmu shi ne samar da gaskiya domin ilimantar da mutane.Amma kamar sauran jaridu, dole wasu lokutan za mu iya yin kuskure," kamar yadda Daily Trust ta ƙara haske.

  3. Idan Isra'ila ta ce mana kule, za mu kai hare-hare a kan kadarorinta - Iran

    Iran ta ce za ta kai hare-hare a kan "muhimman kadarorin" Isra'ila idan har ta mayar mata da martani.

    Babban hafsan tsaron Iran, Manjo Janar Mohammad Bagheri ne ya yi wannan gargaɗin, inda ya yi barazanar ƙaddamar da hare-haren da zarar Isra'ila ta ce musu kule.

    "Idan Isra'ila ta ta cigaba da hare-haren da take yi, ko kuma ta nemi ta taɓa mutuncinmu da ƴancin ƙasarmu, lallai za mu maimaita irin waɗannan hare-haren da muka yi, ko kuma ma waɗanda suka fi zafi domin za mu kai hare-haren ne a kan dukkan kadarorinta," in ji Bagheri.

    Ya ce dakarun Iran Revolutionary Guard Corps a shirye suke domin kare ƙasar, da kuma maimaita irin hare-haren da suka kai a daren Talata.

  4. Zan iya rantsewa da Ƙur'ani ban saci kuɗin Kaduna ba - El-Rufai

    Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce zai iya rantsewa da Ƙur'ani bai saci kuɗi ba a lokacin da yake mulkin jihar.

    Ya bayyana hakan ne a wani shiri na gidan rediyon Freedom da ke Kaduna a ranar Talata kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

    Majalisar Jihar Kaduna dai tana binciken tsohon gwamnan ne bisa zargin karkatar da sama da naira biliyan 324 a zamaninsa, zargin da tsohon gwamnan da waɗanda suka aiki tare suka ƙaryata.

    A cewarsa, "Na yi shiru ne domin ganin yadda za ta kaya. Ina yawan addu'ar Allah Ya min jagora a duk abin da nake yi a rayuwa. A matsayina na ɗan Adam, ina ƙoƙari wajen guje wa cin amanar mutane ko kuma aikata wani abu da bai dace ba.

    "Na sha faɗa cewa duk lokacin da tsofaffin gwamnonin Kaduna da sauran shugabanni suka yarda a yi rantsuwa da Ƙur'ani cewa ba su saci kuɗin al'umma ba, to nima a shirye nake saboda na san ban shiga siyasa domin sata ba. Na shiga siyasa ne domin hidimta wa al'umma.

    "Amma akwai ban mamaki abin da ke faruwa, amma haka rayuwa take. Abin da zan ce kawai shi ne duk wani bita da ƙulli da ƙarairayi da ake laƙa mana a cigaba domin mun kai kukarmu wajen Allah."

    El-Rufai ya ce bayan karatun da yake yi, zai dawo siyasa dumu-dumu a shekarar 2027 saboda a cewarsa ba a yin ritaya a siyasa.

  5. Netanyahu ya ce Iran za ta ɗanɗana kuɗarta

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Iran za ta ɗandana kuɗarta bayan hare-haren da ta kai a birnin Tel Aviv a ranar Talata.

    Sai dai rahotanni daga Tel Aviv na nuna cewa yawancin makamai masu linzamin guda 180 da Iran ta harba, Isra'ila ta kakkaɓo, amma an kashe wani Bafalasɗine guda ɗaya a gaɓar yamma da tekun Jordan, sannan hare-haren sun kai ga wata makaranta da wajen cin abinci a birnin na Tel Aviv.

    A nata ɓangaren, Iran ta ce ƙaddamar da hare-haren ne a matsayin martani ga hare-haren da Isra'ila, ciki har da kashe jagoran Hezbollah, Hassan Nasrallah.

    Haka kuma Isra'ila ta ce za ta cigaba da kutsawa cikin ta ƙasar kamar yadda ta fara, a daidai lokacin a Hezbollah ɗin ta ce ta dakatar da dakarun Isra'ila ɗin shigowa yankinta.

  6. Assalu Alaikum

    Jama'a barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba daga nan BBC Hausa, inda za mu riƙa kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sadarwa domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyoyi.

    Ku kasance tare da mu.