Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 02/10/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Mun ƙwato naira biliyan 14 a kwana uku - ICPC

    Hukumar yaƙi da cin da hanci da rashawa ta Najeriya ICPC, ta ce ta samu nasarar ƙwato kuɗaɗe kimanin naira biliyan 14 a kwanaki uku.

    Shugaban hukumar Dr. Musa Adamu Aliyu shi ne ya bayyana wa BBC hakan inda ya ce jami'an hukumar sun ƙwato biliyan 10 daga hannun wata mata.

    Shugaban hukumar ya ce yanzu haka hukumar tasa na shirin ɓullo da wani shiri da za a rinƙa yi a manyan harsunan Najeriya domin daƙile rashawa da cin hanci.

    Dr Musa Adamu Aliyu ya ƙara da cewa hukumar za ta shiga gangamin wayar da kan ƴan Najeriya domin kimsa musu ƙiyayya ga rashawa da cin hanci da kuma nusar da su irin illar da hakan ke yi wa tattalin arziƙin ƙasar.

  2. Netanyahu ya jajantawa iyalan sojojin Isra'ila da aka kashe a Lebanon

    Firaministan Isra'ila Bejamin Netanyahu ya ce "kan ƙasar a hade yake" yayin da yake jajatawa iyalan sojoji takwas da aka kashe a Lebanon a ranar Laraba.

    A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X, Netanyahu ya ce "muna tsakiyar yaƙi mai tsanani da ta'addancin Iran da ke neman halaka mu. wannan ba zai faru ba, za mu tsaya tare kuma da taimakon Ubangiji - za mu yi nasara."

    Ya kammala jawabinsa da cewa zai tabbatar da ɗorewar Isra'ila.

  3. Hamas ta ce mayaƙanta ne suka kashe mutum bakwai a Tel Aviv

    Ƙungiyar Hamas ta ce ita ce ta kai harin bindiga da na wuka a Tel Aviv a ranar Talata, inda aka kashe mutum bakwai.

    Ƙungiyar ta ce maharan mayaƙanta ce daga birnin Hebron a Gabar Yamma da Kogin Jordan.

    Lamarin ya faru ne kusa da tashar jirgin kisa a yankin Jaffa na Tel Aviv.

    Nan take aka kashe maharan a wurin da suka kai harin.

  4. An haramta cin nama a Indiya saboda bikin addinin Hindu

    Hukumomi a birnin Ayodhya na Indiya sun haramta sayarwa da rabawa da adana nama da duk wani abu da ya shafi nama har tsawon kwana tara na bikin addinin Hindu.

    Sun ce haramcin zai fara ne daga ranar Alhamis da za a soma bikin kuma ya shafi masaukin baƙi da gidajen sayar da abinci.

    Mahukunta birnin da ke jihar Utter Uttar Pradesh sun yi gargaɗi ga ƴankasuwa cewa za su fuskanci fushin hukuma idan har suka saɓa umarnin.

    Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan'adam da kuma musulmi tsiraru sun soki matakin na haramcin nama a bikin Hindun na Navaratri.

  5. Isra'ila ta ce an kashe sojojinta a artabu da Hezbollah

    Isra'ila ta ce sojojinta takwas aka kashe a Lebanon yayin da dakarunta ke ci gaba da faɗa da mayaƙan Hezbollah ta ƙasa.

    Tun da farko rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun yi artabu da Hezbollah.

    Isra'ila ta tura dakaru a kan iyaka da Lebanon domin yaƙi da Hezbollah

    Isra'ila ta yi gargaɗi ga ƙauyuka 20 a kudancin Lebanon su fice daga gidajensu, tare da ƙara nanata gargaɗin bayan ta fara gwabza faɗa ta ƙasa.

    Hukumomin lafiya na Lebanon sun ce mutum 55 aka kashe a sassan ƙasar a hare-haren Isra'ila ta sama a ranar Talata.

    Tun da farko rundunar sojin ta tabbatar da kashe kwamandanta.

    Hezbollah ta bayar da rahoton cewa ta yi arangama da sojojin Isra'ila a aƙalla garuruwa biyu da ke kan iyaka da Isra'ila, inda ta kuma sha alwashin korar dakarun na Isra'ila daga yankin.

    A wajen taron masu ruwa da tsaki na Iran, shugaban addinin Iran ya ce dole ne ƙasashen yammaci su fice yankin Gabas ta Tsakiya domin samun zaman lafiya.

  6. Lokaci na neman ƙure mana a gabas ta tsakiya - Guterres

    Shugaban Majalisar Ɗinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana wa kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya cewa lokaci na neman ƙure musu a game da batun gabas ta tsakiya.

    "Rikicin da ake yi a gabas ta tsakiya ya fara zama kamar wata gobara," kamar yadda Guterres ya bayyana wa wakilan kwamitin.

    Ya ce tun makon jiya, "abubuwa suke ta ƙara lalacewa."

    Ya ce Isra'ila ba ta sassauta hare-harenta a Lebanon, inda ya ce sun fara tunanin samar da yarjejeniyar tsagaita na ɗan lokaci, amma sai Isra'ilar "ta ƙara ƙaimi" wajen kai hare-haren.

    Ya ce shirin Majalisar Ɗinkin Duniya na samar da zaman lafiya na nan daram, sannan "tutar Majalisar Dinkin Duniya na ci gaba da kaɗawa a Isra'ila."

    Ya ce, "ina sake Allah-wadai da hare-haren makamai masu linzami da Iran ta ƙaddamar a Isra'ila."

    Tun farko, Isra'ila ta sanar da hana shi shiga ƙasarta, saboda a cewarta ya ƙi yin Allah-wadai da hare-haren da Iran ta kai mata.

    Ya ce. "lokaci na neman ya ƙure mana," in ji shi, sannan ya yi kira da a tsagaita wuta.

  7. Mataimakan ƴantakarar shugabancin Amurka sun caccaki juna a mahawara

    Masu takarar kujerar mataimakan shugaban ƙasa a zaɓen Amurka na watan gobe sun caccaki juna kan rikicin gabas ta tsakiya da batun ƴan ci-rani, zubar da ciki da tsarin haraji da sauyin yanayi da kuma wasu batutuwan da dama a muhawarar ƙeƙe da ƙeƙe.

    Tim Walz na Jam'iyyar Democrat da JD Vance na Republican kowannensu ya kare kansa da kuma iyayen gidansa da suke takara tare wato mataimakiyar shugaban ƙasa Kamala Harris da tsohon shugaban ƙasa, Donald Trump.

    Mista Vance ya ɗiga ayar tambaya da goranta abin da ya kira da gazawar Ms Harris ta gaggara taɓuka abin arziki wajen shawo kan matsalar baƙin-haure da hauhawan farashi.

    Shi kuma Tim Walz ya caccaki Donald Trump kan hana matan ƴancin zubar da ciki da kuma ƙin yarda da sahihanci zaɓen 2020 da ya sha kaye har wannan lokaci.

  8. Netanyahu ya yi zama na musamman da manyan hafsoshin tsaron Isra'ila

    Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi zama na musamman da manyan hafsoshin tsaron Isra'ila a birnin Tel Aviv a yau Laraba.

    A hoton da aka fitar, an ga Netanyahu zaune kusa da Ministan Tsaro Yoav Gallant da sauran su.

    Tun a farko, Firaiministan ya yi alwashin mayar da martani a kan hare-haren da Iran ta ƙaddamar a ƙasarsa, inda ya bayyana harin na daren jiya a matsayin "kuskure babba" da dole "Iran ta ɗanɗana kuɗarta."

  9. Mutum 10 sun rasu a hatsarin mota a Legas

    Mutum 10 ciki har da ƙananan yara uku da manya bakwai ne suke rasa rayukansu a wani hatsarin mota a yankin Abule Osun da ke babban titin Lagos-Badagry da ke jihar Legas a daren Talata.

    Wata sanarwa da babban sakatare na Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa na jihar Legas, Olufemi Oke-Osanyintolu ya fitar, wanda tashar talabijin ta Channels ta ruwaito, ya ƙara da cewa wasu mutum uku sun jikkata.

    Hatsarin ya auku ne bayan wata mota ƙirar Siena ta haɗu da wata babbar mota da ke ajiye.

    Oke-Osanyintolu ya ce binciken da suka gudanar ya nuna cewa motar ta Siena tana gudun wuce ƙima ne, inda ta buga da motar da ke tsaye ba tare da ya lura ba.

  10. Isra'ila ta ce an kashe mata soja na farko a Lebanon

    Rundunar sojin Isra'ila ta IDF ta tabbatar da mutuwar sojanta na farko tun bayan da ta ƙaddamar da shirinta na kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa.

    Rundunar IDF ta ce an kashe mata soja mai muƙamin kyaftin masi suna Eitan Yizhak Oster mai shekara 22 a cikin Lebanon ɗin a ranar Laraba.

    Matashin sojan shi ne kwamandan sashen Egoz, sashe na musamman da suka ƙware wajen yaƙin sari ka noƙe.

  11. Hezbollah ta ce hare-haren da ta kai Isra'ila somin-taɓi ne

    Kakakin ƙungiyar Hezbollah ya ce rikicin da suke yi da dakarun Isra'ila a kudancin Lebanon somin-taɓi ne na yaƙi.

    "Dakarunmu da masu ba mu kariya a shirye suke domin su fuskanci maƙiyanmu," in ji Mohammad Afif na Hezbollah, kamar yadda Reuters da NBC suka kalato.

    Afif ya ƙara da cewa a shirye ƙungiyar take ta fuskanta tare da gwabzawa da dakarun Isra'ila wato IDF.

    Hezbollah da dakarun IDF dai suna cigaba da fafatawa ne bayan sojojin na Isra'ila sun fara kutsawa cikin Lebanon ta ƙasa.

  12. Shugaba Tinubu ya fara hutun makonni biyu

    Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu zai tafi ƙasar Ingila domin hutun mako biyu, wanda yana cikin hutunsa na shekara.

    Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin watsa labarai da tsare-tsare, Bayo Onanuga ya fitar.

    Ya ce shugaban zai yi amfani da damar wajen yin nazari a kan muhimman matakan da ya ɗauki a gwamnatinsa, musamman ta ɓangaren inganta tattalin arziki.

    Zai dawo domin cigaba da gudanar da mulki da zarar hutun ya ƙare.

  13. China ta ce a shirye take ta inganta alaƙarta da Rasha

    Shugaba Xi Jinping na China ya ce a shirye yake ya inganta da kuma faɗaɗa alaƙarsa da Rasha a wani saƙo da ya aike wa Shugaba Vladimir Putin.

    Shugabannin biyu su aike wa juna saƙon cika shekara 75 da ƙulla kyakyawar hulɗar diflomasiyya tsakanin ƙasashensu.

    A cewar kafar yaɗa labaran China Mista Xi ya ce maƙwabtaka mai kyau, tsare-tsare masu ƙarfi da inganci da haɗin-kai da kowanne ɓangare ke ganin riba, su ne muhimman abubuwan da ke sake ƙarfafa ƙawance da ke tsakanin China da Rasha.

    Shugaba Putin na samun taimakon China sosai tun soma mamayar Rasha a Ukraine a 2022, ta fuskar haɓɓakar kasuwanci yayinda Moscow ke fuskantar takunkuman karayar tattalin arziki daga ƙasashen yamma

  14. Sojojin Isra'ila sun ce sun lalata ramukan da Hezbollah ke ɓoyewa

    Sojoji a Isra'ila sun ce suna kai hare-harensu na Beirut ne a kan mayaƙan Hezbollah na Lebanon.

    Isra'ilar ta kuma ce ta gargaɗi mazauna yankunan kudancin birnin ƙasar inda Hezbollah ke da zama da su sauya matsugunai.

    Ma'aikatar lafiya a Lebanon ta ce hare-haren Isra'ila a jiya Talata sun yi ajalin mutum 55 a sassan ƙasar.

    Wakiliyar BBC a kudancin Lebanon ta ce ta iske garin ko'ina babu mutane, sannan Isra'ilar ta sanar da cewa a tsawon watanni dakarunta na ta kai farmaki a yankunan da ke kan iyakokin kudancin Lebanon, kan ƙungiyar da ke samun goyon-baya daga Iran.

    A cewar sojojin sun lalata ramukan ƙarƙashin ƙasa da rumbunan makamai.

  15. An sassauta umarnin neman mafaka a Tel Aviv bayan harin Iran

    An sassauta umarnin neman mafaka a sassan Isra'ila, bayan hare-haren Iran na tsakiyar daren jiya. Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya gargaɗi cewa Iran ta tafka babban kuskure kuma za ta ɗanɗana kudarta bayan ƙaddamar da ruwan makamai masu linzami da ke cin dogon-zago cikin ƙasarsa.

    Sojojin Isra'ila sun ce makamai masu linzami kusan 180 aka harba musu, sai dai Iran na cewa kusan 200 ta harba.

    A wata sanarwa ta kafar talabijin, babban hafsan sojin Iran, Mohammad Bagheri, ya ce sun ƙaddamar da harin ne a kan sansanonin sojin Isra'ila da hedikwatar hukumar leken asirinta, Mossad.

    Isra'ila na cewa ta kakkaɓo galibin makaman, sai dai kuma wakiliyar BBC a birnin Ƙudus ta tabbatar da cewa wasu daga cikin makaman sun faɗa a sansanin sojoji.

    Ta kuma shaida cewa a harin na jiya, an sanarwa ƴan ƙasar su gaggauta ɓuya a mafakar kare kai daga hare-haren bama-bamai.

    Iran ta kuma yi gargaɗin cigaba da wadannan hare-hare muddin Isra'ila ta tanka.

  16. Isra'ila ta haramta wa sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya shiga ƙasar

    Ministan ƙasashen waje na Isra'ila, Israel Kartz ya ce Isra'ila "ba ta maraba" da sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Guterres kuma an haramta masa shiga ƙasar.

    Israel Katz ya ce an cimma wannan matsaya ne bisa la'akari da gazawar Antonio Guterres ta ƙin yin kakkausan suka ga harin da Iran ta kai wa Isra'ilar ranar Talata.

    Ya kuma zargi shugaban na Majalisar Ɗinkin Duniya da "nuna ƙiyayya ga Isra'ila" da "goyon bayan ta'addanci da fyaɗe da kisan jama'a.

    "Tarihin Majalisar Ɗinkin Duniya ba zai taɓa manta wa Guterres ba a matsayin gurɓatacce ."

    A jiya ne dai sakatare janar na Majalisar Ɗinkin ta Duniya ya alawadai da abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya inda kuma ya yi kira da cimma tsagaita wuta.

  17. Dole ne ƙasashen yammaci su bar Gabas ta Tsakiya - Khamenei

    Shugaban addini na ƙasar Iran, Ayatollah Ali Khamenei, ya gana da ƙungiyar masana na ƙasar a birnin Tehran a yau ɗin nan.

    Khamenei ya ɗora laifin rikicin da yankin Gabas ta Tsakiya ke fuskanta a kan ƙasar Amurka da wasu ƙasashen Turai waɗanda "ke karyar samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin".

    Shugaban addinin ya kuma ce "dole ne su bar yankin" domin al'ummar wurin su samu zaman lafiya.

    Ya kuma ƙara da cewa yana alhinin rasuwar shugaban Hezbollah, Hassan Nasrallah, duk da cewa bai ɗage ganawar tasa da mutanen ba kasancewar Iran ta ayyana kwanakin alhini biyar ga rasuwar shugaban na Hezbollah.

    Ayatollah Khamenei dai ya bayar da umarnin kai wa Isra'ila harin mizayil a ranar Talata, wanda yanzy haka yake a wani wurin da ba kowa ne ya sani ba kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

  18. An rage shigo da fetur da lita biliyan 2.58 bayan cire tallafi – Gwamnatin Najeriya

    Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa ta ce Najeriya ta samu ragowar shigo da man fetur bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin Bola Tinubu ta yi a watan Mayun 2023.

    Hukumar ta ce an samu ragowar shigo da fetur ɗin daga lita biliyan 20.30 a 2023 daga lita biliyan 23.54 da aka shigo da shi a shekarar 2022, wanda hakan ke nufin ragowar kashi 13.77 cikin 100.

    "Maganar shigo da man fetur, an shigo ga lita biliyan 20.30 a shekarar 2023, maimakon lita biliyan 23.54 na shekarar 2022, wato an samu ragowa da kashi 13.77. Ragowar ma za ta fi bayyana ne idan aka kwatanta da wata shidan ƙarshe na shekarar 2022.

    "A wata shidan karshe na 2022, man da aka shigo da shi ya kai lita biliyan 11.98, wanda ke nufin ragowar kashi 30.22 idan aka kwatanta da wata shidan farko na 2023, wato ragowar lita biliyan 3.62.

    Shi ma ministan yaɗa labarai na ƙasar Idris Mohammed ya ce amfani da man fetur ya ragu da kashi 50 a ƙasar bayan cire tallafin man fetur da aka yi.

  19. Yadda kwale-kwale ya kife da masu Mauludi 300 a jihar Naija

    Wata sanarwa da kakakin hukumar agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Arah ya fitar, ta ce akwai sama da fasinjoji 300 a cikin kwale-kwalen lokacin da ya kife a madatsar ruwa ta Jebba a garin Gbajibo da ke ƙaramar hukumar da yammacin ranar Talata.

    Abdullahi Arah ya ce kwale-kwalen wanda ya taso daga Mundi zai tafi Gbajibo domin halartar bikin Maulidi cike yake maƙil da mata da ƙananan yara.

  20. Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya ɗauki nauyin marayu 95 a Kano

    Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya sanar da cigaba da ɗaukar ɗawainiyar marayu 95 a Kano.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne bayan ziyarar da ya kai gidan marayu na Nasarawa a cikin bikin Ranar Ƴancin Najeriya na 64, inda ya ci abincin rana tare da marayun.

    A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamnan zai cigaba da ɗaukar ɗawainiyar dukkan marayun baki ɗaya.

    "Mun ɗauki ɗawainiyar dukkan marayun da suke wannan gidan, tun daga karatunsu daga firamare har zuwa jami'a da lafiyarsu da sauran buƙatun har zuwa ƙarshen mulkina."

    Gwamnan ya ƙara da cewa gwamnatinsa za ta ba marayun dama domin su cimma dukkan muradunsu na rayuwa.

    "Yanzu kun zama ƴaƴana, zan cigaba da kula da ku. Da yardar Allah yanzu za ku fara jin daɗin rayuwa," in ji shi.

    Sanarwar ta kuma ƙara da cewa gwamna ya ba gidan marayun tallafin abinci na miliyoyin naira ga gidan na maryu.