Real Madrid na zawarcin Palmer, Lookman na son komawa Ingila
Rahoto kai-tsaye
Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da A'isha Bappa
Hotunan ababen hawa da harin Isra'ila ya ƙona a Syria
Muna ci gaba da bibiya don ganin tasirin da hre-haren Isra'ila suka yi a Syria, musamman wanda aka kai a daren jiya.
Harin ya lalata abubuwa a kusa da filin jirgin sama na Qamishli da ke arewacin ƙasar, inda wasu motoci suka ƙone ƙurmus.
Isra'ila ta kare hare-haren da take kai wa, inda ta ce tana kai su ne kan cibiyoyin soja domin hana shigar makamai hannun masu tsassaurar ra'ayi.
Daga rahotannin da muka samu zuwa yanzu, hare-haren ba su faɗa kan gine-gine ba.
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Asalin hoton, Reuters
Ana zanga-zanga kan kisan mata a Kenya
Asalin hoton, AFP
Ƴan sanda a Kenya sun yi amfani da barkono mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito don nuna fushi kan ƙaruwar kisan mata a ƙasar.
An kama mutum aƙalla uku, inda waɗanda suka shirya macin suka ce tun da farko jami'an tsaro sun ki amincewa da buƙatarsu ta yin zanga-zangar.
"Mun nemi hukumomi su ba mu damar fita zangaz-zanga amma sun ki, sun ce shugaban ƙasa ya ba mu kuɗi don haka ba su ga dalilin da zai sa mu yi zanga-zanga ba," kamar yadda Njeri Migwi, shugaban masu zanga-zangar ya faɗa wa BBC.
A watan Nuwamba, shugaba William Ruto ya ce gwamnatinsa na shirye domin daƙile ƙaruwar kisan mata, inda ya yi alkawarin bayar da dala 800,000 kan wani shiri na kare gidaje da kuma al'umma wato "Safe Home, Safe Space".
Mutane sun yi irin wannan zanga-zanga da suka ce ta lumana a baya, musamman a watan Janairu, sai dai hukumomi sun haramta ta.
Masu zanga-zangar na yin kira na kawo karshen ƙaruwar cin zarafin mata, da kuma bijiro da tsauraran dokoki don hukunta masu laifi.
Sun kuma soki yadda ƴan sanda suke yin sako-sako da batutuwa da suka shafi mata.
A watan da ya gabata, ƴan sanda suka ce sun samu rahotannin cin zarafin mata da suka kai 97 a cikin watanni uku kacal.
Kotu ta ki bayar da belin Yahya Bello
Wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta ki bayar da belin Yahya Bello.
Tsohon gwamnan na jihar Kogi ya bayyana a gaban kotun yau Talata, domin neman beli kan shari'ar da ake yi masa.
Ana zargin Yahya da halasta kuɗin haram da suka haura naira biliyan 100 wanda ya karkata lokacin yana gwamna, a cewar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC.
Da take yanke hukunci, mai shari'a Maryanne Anenih, ta ce an gurfanar da Bello ranar 27 ga watan Nuwamba, bayan da jami'ai suka kama shi ranar 26 ga watan. Sai dai an buƙaci belinsa ranar 22 ga watan na Nuwamba, kwanaki da dama kafin ma ya gurfana.
Mai shari'ar ta ce ya kamata a bukaci beli ne bayan an gurfanar da wanda ake ƙara.
"Buƙatar beli da Yahya ya yi tun da farko ba ya kan tsari, don haka ne muka yi watsi da shi," in ji mai shari'a Maryanne Anenih.
Yau Ɗan Ibro ke cika shekara 10 da rasuwa
Bayanan bidiyo, Latsa sama don kallon bidiyon
A yau Talata, Rabilu Musa Ibro yake cika shekara goma da rasuwa.
Ɗan Ibro ya rasu ne ranar Laraba 10 ga watan Disamban 2014.
Duk da ya bar duniya shekara 10 da suka wuce, har yanzu Rabilu Musa Ibro na cikin taurarin fim da ke da farin jini ga masu neman nishaɗi da kuma son kashe kwarkwatar idanunsu.
Har kawo yau abokansa na Kannywood na ci gaba da jimamin rabuwa da shi.
Alhaji Rabiu Ibrahim Daushe na cikin fitattun masu finafinan barkwanci da suka daɗe tare da Ibro, kuma ya bayyana wa BBC cewa a ganinsa, babu wanda zai maye gurbin da Ibro ya bari a Kannywood.
'Isra'ila ta kai hare-hare sama da 300 tun faɗuwar gwamnatin Assad a Syria'
Asalin hoton, Getty Images
Wata ƙungiyar kare hakkin ɗan'adam a Syria ta ce Isra'ila ta kai hare-hare aƙalla 310, tun bayan faɗuwar gwamnatin Assad.
Waɗannan hare-hare sun faɗa kan cibiyoyin tsaro, wuraren ajiye makamai da filayen jirgin sama da kuma cibiyoyin bincike.
Wuraren da aka kai hare-haren sun haɗa da wajen birnin Damascus, da yankin Qudsaya da kuma Salamiyah da ke gabashin Hama, a cewar ƙungiyar ta SOHR.
Isra'ila ta ce tana ɗaukar mataki don hana shigar makamai hannun masu tsassaurar ra'ayi, bayan kifar da gwamnatin Assad.
Kowane ɗan Najeriya na da damar takarar shugaban ƙasa a kowane lokaci - Atiku
Asalin hoton, Atiku Abubakar
Wasu kalamai da suka fito daga bakin sakataren
gwamnatin Najeriya, George Akume, na neman 'yan siyasar arewacin ƙasar su
jira har shekarar 2031 idan suna son yin takarar shugabancin ƙasar, sun janyo
cece-kuce.
Mista Akume, ya faɗi hakan ne yayin hira da wani gidan
talabijin a ƙasar, inda ya ce kamata ya yi a bar yankin kudancin Najeriya ya
karasa shekaru takwas ɗin sa, kamar yadda itama Arewa ta yi lokacin mulkin
shugaba Buhari.
Kalaman dai sun girgiza ƴan siyasar arewacin Najeriya, inda tuni aka fara mayar da martani.
Mai magana da yawun tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, Abdulrashid Shehu Uba, ya ce kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa kowaye damar fita don neman kujerar shugaban ƙasa.
"Babu wata yarjejeniya da aka yi ko kuma aka yadda za a tafi a kan wannan tsari. Idan su a APC sun yi wannan tsari mu ba haka yake a wajenmu ba. Ya kamata su tsaya su mayar da hankali kan zaɓen da suka ƙwace," in ji Abdulrashid.
Kakakin na Atiku ya ce kowa na ganin yadda al'amura suka taɓarɓare a yanzu musammman ɓangaren tsaro da kuma tsadar rayuwa, inda ya ce da gwamantin APC ta yi aiki ba za ta fito ta ce kada wani ya yi takara ba.
Ya ce babu wani ɗan siyasa da suke tsoro kamar tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Dubban mutane na neman ƴan uwansu a gidan yarin Sednaya na Syria
Asalin hoton, EPA
Dubbun al'umma a Syria sun yi fitar farin ɗango zuwa gidan yarin da ake tsare fursunonin siyasa domin neman ƴan uwansu.
Ƴan tawayen da suka ƙwace iko a ƙasar sun ce sun ƴantar da sama da mutane 100 da ake tsare da su a gidan yarin Saydnaya da ke Damascus, amma akwai sauran mutanen da ba a iya gano su ba.
Jami'an tsaro na Civil Defense sun ce su ma sun bincika kurkukun karkashin ƙasa da na ɓoye amma ba su ga sauran ba.
'Manyan jami'an gwamnatin Assad za su fuskanci hukunci'
Asalin hoton, Reuters
Shugaban ƴan tawayen Syria, Abu Muhammed al-Jawlani ya
sanar da cewa manyan jami'an gwamnati hamɓararren shugaba Assad da ke da hannu a
cin zarafin fursunonin siyasa, za su fuskanci hukunci.
A wani sako da ya wallafa a dandalin Telegram, ɗauke da
sunansa na asali Ahmed al-Sharaa, jagoran ya ce za a wallafa sunayen jami'an da
ke da hannu a azabtarwa da duba hanyoyin mayar da waɗanda suka tsere daga ƙasar.
Sanarwar Abu Muhammad ta jadadda cewa
ba za a taɓa mutanen da babu jinin kowa a hannusu ba, sannan za a kare ƴancin
mata da tsirarun kabilu.
Abu Muhammad ya kuma gana da Firaministan Syria kan
shirye-shiryen kafa gwamnatin rikon kwarya.
Buɗewa
Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Talata.
Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.
Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.