Ƴan sanda a Kenya sun yi amfani da barkono mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga-zangar da suka fito don nuna fushi kan ƙaruwar kisan mata a ƙasar.
An kama mutum aƙalla uku, inda waɗanda suka shirya macin suka ce tun da farko jami'an tsaro sun ki amincewa da buƙatarsu ta yin zanga-zangar.
"Mun nemi hukumomi su ba mu damar fita zangaz-zanga amma sun ki, sun ce shugaban ƙasa ya ba mu kuɗi don haka ba su ga dalilin da zai sa mu yi zanga-zanga ba," kamar yadda Njeri Migwi, shugaban masu zanga-zangar ya faɗa wa BBC.
A watan Nuwamba, shugaba William Ruto ya ce gwamnatinsa na shirye domin daƙile ƙaruwar kisan mata, inda ya yi alkawarin bayar da dala 800,000 kan wani shiri na kare gidaje da kuma al'umma wato "Safe Home, Safe Space".
Mutane sun yi irin wannan zanga-zanga da suka ce ta lumana a baya, musamman a watan Janairu, sai dai hukumomi sun haramta ta.
Masu zanga-zangar na yin kira na kawo karshen ƙaruwar cin zarafin mata, da kuma bijiro da tsauraran dokoki don hukunta masu laifi.
Sun kuma soki yadda ƴan sanda suke yin sako-sako da batutuwa da suka shafi mata.
A watan da ya gabata, ƴan sanda suka ce sun samu rahotannin cin zarafin mata da suka kai 97 a cikin watanni uku kacal.