Rufewa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labarai kai-tsaye. Da fata kun ji daɗin kasancewa da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 10-12-2024.
Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da A'isha Bappa
A nan muka kawo ƙarshen wannan shafi da muke kawo muku labarai kai-tsaye. Da fata kun ji daɗin kasancewa da mu.
A madadin sauran abokan aiki, ni Isiyaku Muhammed nake cewa mu kwana lafiya.

Asalin hoton, Economic and Financial Crimes Commission
Kotun tarayya da ke zamanta a Maitama ta ƙi amincewa da belin da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ya nema, inda ta bayar da umarnin a ajiye shi a gidan yarin Kuje.
Mai shari'a Maryann Anineh ta ce an yi gaggawar neman belin.
Yahaya Bello da wasu masu suna Abdulsalami Hudu da Umar Oricha ne suke fuskantar tuhuma kan zargin almundahanar kuɗi naira biliyan 110.4.
Hukumar EFCC ce ta yi ƙarar Yahaya Bello da sauran mutanen kan tuhume-tuhume 16 da suka haɗa cin amana da almundahana.
Sai dai kotun ta bayar da belin sauran waɗanda ake zargi tare da shi.

Asalin hoton, Dauda Lawal/Instagram
Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawal ya ce wasu jihohin da ba su da ƙarfin tattalin arziki za su shiga tasku idan aka amince da ƙudurorin haraji da shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika majalisa.
"Don haka dole a nazarci ƙudurorin cikin tsanaki saboda kar mu cuci kanmu," in ji shi a tattaunawarsa da tashar Channels a ranar Talata.
Ya ƙara da cewa, "a cikin ƙudurorin akwai abubuwa masu kyau, akwai kuma marasa kyau, wannan ya sa muke ƙara nazartar abubuwan da ke ciki domin ba mutanenmu shawara kan abin da ya kamata."
Lawal ya ƙara da cewa jihohi da dama ba za su iya biyan albashin naira 70,000 matuƙar an tabbatar da gyare-gyaren da ke cikin ƙudurorin.
"Gyare-gyare na da kyau, amma yana da kyau mu guji gaggawa domin gudun yin da-na-sani daga bisani."

Asalin hoton, Bayo Onanuga
Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya naɗa Shamseldeen Babatunde Ogunjimi akanta-janar na riƙo.
Naɗin ya biyo bayan tafiya hutun ritaya da Oluwatoyin Sakirat Madein ta yi, kamar yadda tsarin aiki ya tanada.
Ogunjimi ne babban darakta a ofishin na akanta-janar ɗin na ƙasa, kuma ya kwashe sama da shekara 30 yana aiki a matakai daban-daban na harkokin kuɗi a kamfanoni da gwamnati, kamar yadda sanarwar da Bayo Onanuga ya fitar.
Sanarwar ta ƙara da cewa Tinubu ya ce, "ofishin akanta-janar na da matuƙar muhimmanci, kuma Ogunjimi yana da ƙwarewae da ake buƙata domin tabbatar da aikin ofishin ya tafi daidai domin tabbatar da nasarar ƙoƙarinmu inganta tattalin arzikin ƙasar."
Tinubu ya kuma yaba wa Madein, wadda za ta yi ritaya daga muƙamin daga ranar 7 ga Maris na shekarar 2025.

Asalin hoton, Reuters
Majalisar ƙasar Chadi ta ɗaga darajar shugaban ƙasar, Janar Mahamat Deby zuwa muƙamin Field Marshal, wanda shi ne muƙami mafi girma a rundunar sojin ƙasar.
Ƴanmajalisar sun ɗauki wannan matakin ne bayan kaɗa ƙuri'a a ranar Litinin, inda suka ce, "an ɗaga muƙaminsa saboda sadaukawarsa ga ƙasar da ma rundunar soji, da kuma nasarorin da sojoji ke samu a ciki da wajen ƙasar."
Ƴanmajalisa 160 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa, biyu suka ƙi amincewa, sannan shida ba su halarci zaman ba.
An daga muƙamin Mahamat Deby ne a bayan ya ƙaddamar da yaƙi da Boko Haram a yankin tafkin Chadi, bayan wani hari da suka kai ga sojojin ƙasar.
An ruwaito cewa shi ne ya jagoranci sojoji zuwa fatattakar ƴan Boko Haram, wanda aka yi mako biyu ana gwabzawa.
Ya karɓi mulki ne daga mahaifinsa Idris Deby Itno, wanda shi ma ya samu muƙamin a shekarar 2020 yana mai shekara 68.
A watan Mayu ne aka zaɓi Mahamat a matsayin shugaban ƙasar Chadi, inda ake tunanin zai bi tafarkin mahaifinsa wajen yin mulki ba sani ba sabo.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA, ta bayyana aniyarta ta sanya takunkumi ga kamfanonin jiragen sama da ke jinkirta dawo da kuɗin tikitin ga fasinjoji, bayan jinkiri ko soke tashin jirgin sama.
Wannan dai wani ɓangare ne na tsare-tsare na Hukumar NCAA, wanda ke ba da fifikon haƙƙin fasinjoji.
Hukumar ta NCAA ta gabatar da dokar ce sakamakon abin da ya faru da wani fasinja da kamfanin jirgin sama na Airpeace.

Duk da cewa akwai sauran lokaci kafin babban zaɓen Najeriya a shekarar 2027, ana ci gaba da musayar yawu kan shirye-shiryen jam'iyyu na fuskantar zaɓen mai zuwa.
Jam'iyyun hamayya na zargin APC mai mulki a ƙasar da yunƙurin haifar da rikice-rikice a cikinsu domin hana su sukunin da za su iya fuskantarta da ƙarfi har su ƙwace mulki, lamarin da jam'iyyar mai mulki ta sha musantawa.
A shekarar 2023 ne dai Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya yi nasarar doke Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP a zaɓen shugaban ƙasa, inda aka samu wasu gwamnonin PDP da ake zargin sun yi wa APC aiki.