Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/03/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/03/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza, da Umar Mikail

  1. Amurka ta fara aiwatar da ƙarin harajin kashi 25 kan karafa da aka shigar da su ƙasar

    Shugaba Trump

    Asalin hoton, Getty Images

    A yau ne Amurka ta fara aiwatar da shirinta na sanya harajin kashi 25 cikin 100 kan duk wasu ƙarafa da sanholo da ake shigar da su amurka daga duka ƙasashen duniya.

    Ƙasar Australia na daga cikin ƙasashen da suka fara korafi kan wannan mataki inda Firaministanta Anthony Albanese ya ce wannan matakin da shugaba Trump ke ɗauka bai dace ba.

    Ya ƙara da cewa matakin ya saba wa ginshikin abotar da ke tsakanin ƙasashen biyu ya kuma saɓa wa fa'idar da ƙawancen tattalin arzikinsu ya samar sama da shekaru 70.

    Mista Trump dai ya kare manufofinsa a wani taro da ya yi da shugabannin manyan kamfanonin Amurka a fadar White House a jiya Talata

  2. Assalamu Alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Laraba, da Hausawa ke yi wa kirari da ta Bawa ranar samu.

    Sannunmu da sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci domin sanar da ku halin da duniya ke ciki.

    Ku leƙo shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.