Arsenal za ta je Mansfield a FA Cup zagaye na biyar a watan Maris, FA Cup
Asalin hoton, Getty Images
An raba jadawalin FA Cup zagaye na biyar ranar Talata - inda za a buga wasa takwas
Fulham da
Southampton
Port Vale da
wadda za ta yi nasara tsakanin Bristol City da Sunderland
Newcastle da
Manchester City
Leeds United da Norwich City.
Sauran
wasannin Arsenal mai fatan lashe dukkan kofinan bana za ta je Mansfield
Wolverhampton
da Liverpool
Wrexham da
Chelsea
West Ham da Brentford
Za a fara
wasannin FA Cup zagaye na biyar ranar 6 zuwa 9 ga watan Maris.
Saka ya zama kan gaba a karɓar albashi mafi tsoka a Arsenal, Arsenal
Asalin hoton, Getty Images
Bukayo Saka, ya rattaba hannu kan sabuwar yarjejeniyar kaka biyar, domin ci gaba da taka leda a Arsenal wanda har zuwa shekarar 2031.
Wasu majijoyin sun shaida wa BBC cewa yarjejeniyar za ta mayar da Saka mafi karɓar albashi mai tsoka a ƙungiyar, inda zai rika karɓar sama da fam 300,000 a duk mako.
An ɗauki shekara ɗaya ana tattaunawa tsakanin Arsenal da ɗan wasan tawagar Ingila kafin a kai ga cimma matsaya, wanda tun a cikin watan Janairu ya sanar zai ci gaba da zama a Gunners.
A baya Saka ya tsawaita kwantiragin ci gaba da taka leda a Arsenal a 2023, inda zai kare a 2027, yanzu kuma mai shekara 24 ya kara tsawaita yarjejeniyarsa har zuwa 2031.
Wannan batun karin karfin gwiwa ne ga Arsenal, wadda ke kalubalantar kofi huɗu a kakar nan, wadda rabonta da babban kofi tun 2020.
Wannan yarjejeniyar da Arsenal ta ƙulla da Saka na daga tsarin ƙungiyar na riƙe fitattun ƴan wasansa, domin ta koma lashe kofuna a kowacce kakar tamaula.
Sauran ƴan wasan da suka kulla yarjejeniyar ci gaba da taka leada a Gunners sun haɗa da William Saliba da Gabriel Magalhaes da Ethan Nwaneri da kuma Myles Lewis-Skelly.
Saka ya zura ƙwallo bakwai a wasa 33 da ya buga wa Arsenal a wannan kakar.
Kungiyar da Mikel Arteta ke jan ragama tana ta ɗaya a kan teburi da tazarar maki huɗu tsakani da Manchester City ta biyu.
Gunners da City za su buga wasan karshe a Carabao Cup a cikin watan Maris, kuma Arsenal ta kai zagaye na biyar a FA Cup.
Haka kuma Arsenal ta kai zagaye na biyu kai tsaye a Champions League, wadda ta yi ta ɗaya a karawar cikin rukuni da lashe dukkan wasa takwas.
Ko Atalanta za ta ci Dortmund a Jamus a Champions League?, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Ranar Talata za a buga wasan farko a neman cike gurbin Champions League domin zuwa wasannin zagaye na biyu, inda za a kara tsakanin Borussia Dortmund da Atalanta..
Borussia Dortmunda da Atalanta kuwa za su fuskanci juna karo na uku, bayan fafatawar da suka yi a 2018 a Europa League, inda Dortmund ta yi nasara 3-2 a haduwar farko, sannan suka tashi 1-1 a gidan Atalanta a Italiya.
Wasannin da za a buga ranar Talata a Champions League:
Galatasaray da Juventus
Borussia Dortmund da Atalanta
Monaco da Paris St- Germain
Benfica da Real Madrid
Sau nawa za a kara tsakanin Galatasaray da Juventus?
Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan farko a neman cike gurbin Champions League domin zuwa wasannin zagaye na biyu, inda za a kara tsakanin Galatasaray da Juventus ranar Talata.
Galatasaray da Juventus wasa na bakwai za su yi a gasar zakarun Turai a yau Talata, inda kungiyar Turkiya ta yi nasara biyu da canjaras uku, yayin da ta Italiya ta ci wasa daya.
Wasannin da za a buga ranar Talata a Champions League:
Galatasaray da Juventus
Borussia Dortmund da Atalanta
Monaco da Paris St- Germain
Benfica da Real Madrid
Monaco za ta fuskanci PSG da ƴanwasanta uku ke jinya, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Ƙungiyar Monaco na fuskantar kalubale kan koshin lafiyar ƴan wasansu uku gabanin zagayen farko a neman gurbin shiga zagaye na biyu a Champions League da za su kara da mai rike da kofin, Paris Saint-Germain, ranar Talata.
Koci Sebastien Pocognoli ya ce ɗan wasa Maghnes Akliouche da Lamine Camara an yi ta gwada koshin lafiyarsu ranar Litinin da kuma safiyar ranar Talata.
Haka kuma Ansu Fati za a ci gaba da auna koshin lafiyarsa.
Wasa
tsakanin Monaco da Paris St Germain karo na 60 za su kece raini a baya bayan
nan,
Monaco ta ci
18 da canjaras 17 da kuma 24 da PSG ta yi nasara, ko a kakar nan a gasar Ligue
1 a cikin watan Nuwamba, Monaco ce ta zura 1-0 mai ban haushi.
Wasannin da za a buga a Champions League ranar Talata:
Galatasaray da Juventus
Borussia Dortmund da Atalanta
Monaco da Paris Saint-Germain
Benfica da Real Madrid
Ko Real Madrid za ta ɗauki fansa a kan Benfica a Champions League?, Champions League
Asalin hoton, Getty Images
Za a buga wasan farko a neman cike gurbin Champions League zuwa karawar zagaye na biyu, inda
za a yi fafatawa hudu daga ciki har da wanda Real Madrid za ta je Benfica ranar Talata
Sun kara a watan jiya a wasa na karshe a cikin rukuni, inda Benfica ta doke Real 4-2, hakan ne ya hana ƙungiyar Sifaniya kai wa zagaye na biyu kai tsaye.
Kuma daga cikin ƙwallayen da aka ci Real Madrid har da wadda golan Benfica, Anatoliy Trubin ya ci da kai a minti na 98.
Wasannin da za a buga a Champions League ranar Talata:
Galatasaray
da Juventus
Borussia
Dortmund da Atalanta
Monaco da
Paris Saint-Germain
Benfica da Real Madrid
Kavanagh ba zai busa wasa ba a Premier League a wannan makon, VAR
Asalin hoton, Getty Images
Ba a nada Chris Kavanagh domin ya jagoranci wani wasan Firimiya ba a wannan karshen mako ba, bayan jerin kura-kurai da aka ce ya yi a wasan Aston Villa da Newcastle a FA Cup ranar Asabar da ta gabata.
Kavanagh tare da mataimakansa Gary Beswick da Nick Greenhalgh sun sha suka kan yadda suka tafiyar da aikinsu a wasan zagaye na huɗu a Villa Park, inda ba su yi amfani da VAR kamar yadda aka yi a dukkan sauran wasannin ba.
Sun kasa gane cewa Tammy Abraham ya yi satar gida kafin ƙwallon farko da Villa ta ci, sannan ba su ga ketar da mai tsaron bayan Villa, Lucas Digne ya yi wa Jacob Murphy na Newcastle ba – wanda ya kai kafarsa saman gwiwa, lamarin da ya kamata a ba shi jan kati kai tsaye.
Bayan haka sun bayar da bugun tazara kan cewa Digne ya taɓa ƙwallo da hannu, alhali a cikin da'ira ya yi laifin da ya kamata ya zama fenariti.
Trezeguet ya kaddamar da kofin duniya a birnin Bogota, Gasar kofin duniya
Asalin hoton, Getty Images
Tsohon ɗan ƙwallon Faransa, David Trezeguet ya kaddamar da kofin gasar cin kofin duniya a birnin Bogota ranar Lahadi, yayin da ake ci gaba da zagaya duniya da kofin.
Kofin na FIFA ya isa Colombia a matsayin wani bangare na zagaye na kwana 150 da zai je kasashe 30 mambobin FIFA.
Za a buɗe ranar Litinin, domin jama'a su samu ganinsa da yin hotuna.
Zagayen da aka fara a 2026 an fara tun daga watan Janairu a kasar Saudiyya, wadda za ta karɓi baƙuncin gasar cin kofin duniya ta 2034, kafin kofin ya ziyarci kasashe ukun da za su shirya gasar ta bana – Amurka da Canada da kuma Mexico.
Haka kuma zagayen kofin zai haɗa da kasashen da za su shirya gasar 2030, wato Morocco da Portugal da kuma Sifaniya.
A yankin Latin Amurka, kofin wanda ya riga ya ziyarci Guatemala da Honduras, ana sa ran zai kuma je Ecuador da Argentina da Uruguay da Brazil da kuma Mexico.
Gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026 za ta fara ne ranar 11 ga watan Yuni, yayin da za a buga wasan karshe ranar 19 ga watan Yuli.
Amurka, Canada da Mexico ne za su karɓi bakuncin gasar, wadda aka kara yawan kungiyoyi daga 32 zuwa 48 a karon farko.
Real Madrid za ta so ɗaukar fansa a kanmu - Mourinho, Benfica da Real Madrid
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Benfica, Jose Mourinho, ya ce Real Madrid za ta so ɗaukar fansa a kanmu, sakamakon doke su da suka yi a watan da ya gabata a Champions League
Ranar Talata Benfica za ta karɓi bakuncin Real Madrid a wasan farko na cike gurbin kai wa zagaye na biyu a gasar ta zakarun Turai.
Benfica ta doke Real Madrid 4-2 a wasan karshe a cikin rukuni daga ciki har da ƙwallon da mai tsaron ragar Benfica, Anatoliy Trubin ya zura kwallo da kai a minti na 98.
Sakamakon wasan da suka kara a birnin Lisbon ya hana Real Madrid samun gurbin mataki na biyu a gasar kai tsaye.
Benfica, wadda ke matsayi na uku a gasar Firimiya ta Portugal, za ta karɓi bakuncin wasan farko a filin Estadio da Luz ranar Talata.
A bangaren Real Madrid kuwa, tana jan ragamar teburin La Liga, inda take da tazarar maki biyu tsakani da Barcelona, wadda ta ziyarci Girona ranar Litinin a gasar La Liga.
Toney na mafarkin lashe kofin duniya da tawagar Amurka a 2026, Gasar kofin duniya
Ivan Toney na mafarkin lashe kofin duniya tare da tawagar Ingila, yayin da yake ci gaba da sa ƙwazo a tamaula ko Thomas Tuchel zai mika masa goron gayyata.
Ɗan wasan mai shekaru 29, wanda ke taka leda a Al Ahli, ya zura ƙwallo 20 a babbar gasar tamaula ta Saudiyya a wannan kakar – wanda ya bai wa Cristiano Ronaldo tazarar biyu a raga.
Ya buga wasansa na karshe daga bakwai da ya wakilci Ingila a karawar sada zumunta da Senegal a watan Yunin bara, kuma ya samu lambar yabo a Euro 2024 bayan da Ingila ta yi ta biyu.
Za a bai wa ƴanwasan da ke buga Premier damar buɗe baki lokacin wasa, Premier League
Asalin hoton, Getty Images
Gasar Firimiya ta Ingila da kuma English Football League za su ci gaba da aiwatar da tsarinsu na watan Ramadan, inda za a rika dakatar da wasa na ɗan lokaci, domin bai wa ƴan wasa Musulmi damar buɗa baki.
Ramadan zai fara a wannan mako kuma zai ɗauki tsawon wata guda. A wannan lokaci, Musulmai na kaurace wa abinci da abin sha daga fitowar alfijir har zuwa faɗuwar rana.
Da yake faduwar rana a Birtaniya tana tsakanin karfe 17:00 zuwa 19:00 agogon GMT a wannan lokaci, wasannin da za a iya dakatarwa zai fi shafar na ranar Asabar da karfe 17:30 da kuma na ranar Lahadi da karfe 16:30.
Kamar yadda aka saba a shekarun baya, shugabannin ƙungiyoyi tare da alkalai za su cimma matasaya kan lokacin da ya kamata a tsayar da wasan domin bai wa ƴan wasa ko jami’ai Musulmi damar buɗa baki.
Ƙungiyoyi da alkalai za su tattauna tun kafin taka leda, domin cimma matsaya kan lokacin da ya kamata a dakatar da wasa domin buɗe bakin.
Kuma ba za a tsayar da wasa ba a lokacin da ake gara ƙwallo, sai idan an samu damar bugun tazara ko jifa da dai sauransu.
A shekarar 2021 ne aka cimma yarjejeniya da ta bai wa ƴan wasa Musulmi damar buɗa baki yayin wasan Firimiya.
An kuma fara ne a wasa tsakanin Leicester City da Crystal Palace a watan Afrilu 2021. An dakatar da wasan a lokacin bugun falan ɗaya a minti na 30 da take leda, domin bai wa Wesley Fofana na Leicester da Cheikhou Kouyate na Palace damar buɗe baki.
Daga cikin sunayen ƴan wasa Musulmi a gasar Firimiya akwai Mohamed Salah da William Saliba da Rayan Ait-Nouri da Amad Diallo da sauransu.
A wata hira da BBC Sport a 2023, tsohon dan wasan Everton Abdoulaye Doucoure ya ce: “A gasar Firimiya kana da ƴancin yin abin da ya dace. Ba za su taɓa yin wani abu da ya saɓa wa addininka ba, kuma wannan abu ne mai kyau.
“Ina azumi kullum, ban taba ƙin yi ko da rana guda ba. Yanzu ya zama al’ada a gare ni, kuma abu ne mai sauki. Horarwa tana tafiya kamar yadda aka saba a Ramadan, amma idan mun je wasannin waje, muna iya cin abinci daga baya fiye da sauran ƴan wasa, don haka mai girki yana shirya mana abinci yadda ya kamata, kamar yadda muke samu a gida. Muna samun abinci halal, don haka babu wata matsala.”
Haka kuma a 2022, tsohon dan wasan Liverpool Sadio Mane ya bayyana cewa ƙungiyarsa tana sauya jadawalin atisaye domin tallafa wa ƴan wasa Musulmi a watan Ramadan.
Arsenal ta kai zagaye na biyar a FA Cup karon farko a kaka shida, FA Cup
Asalin hoton, Getty Images
Arsenal ta zura ƙwallo 4-0 a minti na 30 da take leda da ta kai ta doke Wigan a FA Cup ta kuma kai zagaye na biyar a karon farko a kaka shida.
Wadda take ta ɗaya a kan teburin Premier League ita ce ta mamaye wasan da ta yi da mai buga League One da fara cin kwallo tun a minti na 11 da fara karawar.
Rabon da Arsenal ta kai zagaye na biyar a kofin tun 2020 - lokacin da Mikel Arteta ya karbi aikin jan ragamar Gunners da daukar FA Cup.
Kano Pillars ta samo maki ɗaya a ƙwara a Premier League, Gasar Premier ta Najeriya
Asalin hoton, NPFL
Kano Pillars ta je ta tashi 1-1 a gidan Kwara United a wasan mako na 26 a gasar Premier da suka buga a ranar Lahadi.
Mai masaukn baƙi ce ta fara cin ƙwallo ta hannun Johnmark Atule a minti na 10 da take leda haka suka je hutu ana cin Pillas 1-0.
Bayan da suka sha ruwa suka koma zagaye na biyu ƙungiyar da ake kira sai masu gida ta farko ta hannun Lius Dadong, saura minti 11 lokaci ya cika.
Wasa na biyar kenan da ta raba maki da yanzu haka take mataki na 17 da maki 29.
Sakamakon wasu wasannin da aka buga ranar Lahadi:
El Kanemi Warriors 1-0 Plateau United
Katsina United 1-0 Nasarawa United
Bayelsa United 0-0 Bendel Insurance
Enugu Rangers 2-0 Wikki Tourists
Enyimba 0-1 Ikorodu United
Kwara United 1-1 Kano Pillars
Remo Stars 1-1 Abia Warriors
Shooting Stars 4-2 Warri Wolves
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ce kan gaba a fafatawar da ake yi tsakanin kungiyar da Manchester City da Arsenal wajen neman tsohon dan wasan gefe na Everton Anthony Gordon, mai shekaru 24 wanda ke taka leda a Newcastle United inda ya je aro, amma farashin dan wasan na Ingila zai kan fam miliyan 95. (Caughtoffside)
Wannan na faruwa ne yayin da Mohamed Salah, mai shekaru 33, ke shirin barin Liverpool a karshen kakar wasan nan, inda kungiyoyi a Masar da Saudiyya ke nemansa. (Teamtalk)
Har wayau Liverpool din na kuma fafatawa da Manchester United, wajen kokarin daukar dan wasan gaba na Wolves Mateus Mane mai shekaru 18 a wannan bazarar. An kiyasta farashin Matashin dan wasan na Ingila wanda aka haifa a Portugal da fam miliyan 50. (Fichajes)
Tottenham ta ƙi amincewa da bukatar Aston Villa da Chelsea ta neman ɗan wasan tsakiyarta dan asalin Sweden Lucas Bergvall, mai shekaru 20. (Athletic)
An bai wa Juventus hakuri, saboda jan katin bisa kuskure, Serie A
Asalin hoton, Getty Images
Mai tsara alkalai da za su busa Serie A, Gianluca Rocchi, ya ce alkalin wasa Federico La Penna ya yi kuskuren bai wa ɗan wasan Juventus, Pierre Kalulu, katin gargaɗi na biyu wanda ya jawo masa jan kati a karawa da Inter Milan ranar Asabar, tare da neman afuwa kan lamarin.
An kori Kalulu ne bayan ɗan wasan Inter, Alessandro Bastoni, ya fadi kasa sannan nan take ya yi wa alkalin wasa alamar an ja rigarsa ya kamata ya bayar da kati - Amma hotunan talabijin sun nuna cewa ba su taɓa juna ba a tsakaninsu.
Juventus, wadda ta karasa karawar da ƴan wasa 10 bayan jan katin, ta sha kashi da ci 3-2, lamarin da ya sa Inter ta kara tazara maki takwas a saman teburin.
Daga bisani kocin Juventus, Luciano Spalletti, da daraktan ƙungiyar, Giorgio Chiellini, sun tunkari La Penna a hanyar shiga ɗakin hutun ƴan wasa bayan kammala fafatawar.
, Daga Jaridu
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ƙuduri aniyar siyan ɗan wasan tsakiya na Faransa Castello Lukeba, mai shekaru 23, daga RB Leipzig, inda ƙungiyar ta Jamus ta shirya sayar da shi kan fam miliyan 52.1. (Sports Boom)
Har wayau Arsenal din na neman ɗan wasan gefe na RB Leipzig mai shekaru 20, Antonio Nusa, wanda aka kimanta tsakanin Yuro miliyan 50-60 (£43m-£52m). (Fussball Daten)
Masu sa ido a kan 'yan wasan Manchester United sun je San Siro ranar Asabar don kallon Federico Dimarco na Inter Milan mai shekaru 28, dan wasan gefe na Italiya da kuma Pierre Kalulu na tsakiya na Faransa, mai shekaru 25, daga Juventus. (Calciomercato)
Har yanzu Enzo Maresca ne kan gaba, a jerin kwaca-kwacan da ake kyautata zaton za su maye gurbin Pep Guardiola idan ya tashi daga Manchester City (Fabrizio Romano)
Barca ta mayar da hankali kan yadda za ta koma ta ɗaya a La Liga, Barcelona
Asalin hoton, Getty Images
Kocin Barcelona, Hansi Flick, ya ce ya kamata su amince da rashin nasarar da suka yi a Copa del Rey a hannun Atletico Madrid, sannan su maida hankali kan wasan La Liga ranar Litinin da za su je su buga da Girona, wadda ke matsayi na 14.
Har yanzu Marcus Rashford ba zai buga karawar ba, wanda ke jinya, bayan raunin da ya ji a karawa da Real Mallorca, sai dai ana sa ran Raphinha zai buga wasan.
Flick, wanda ya ce ya fi son mayar da hankali kan inganta ƙungiyar, ya amince cewa ya ji takaici bayan an soke ƙwallo da suka ci a wasan Copa del Rey, kuma ya ce ya tattauna da alkalin wasan bayan karawar da suka yi da Atletico Madrid.
Barcelona na matsayi na biyu a teburin gasar, Bayan da Real Madrid ta ɗare kan teburi.
Forest ta naɗa Pereira sabon kociyanta, Nottingham Forest
Asalin hoton, Getty Images
Nottingham Forest ta nada Vitor Pereira sabon kociyanta kan kwantiragin wata 18.
Mai shekara 57 ɗan asalin Portugal ya maye gurbin Sean Dyche, wanda aka kora ranar Alhamis.
Ɗaya daga cikin manyan aikinsa shi ne taimaka wa Forest wajen kauce wa faduwa daga gasar Firimiya ta Ingila a kakar nan.
A halin yanzu ƙungiyar tana matsayi na 17 a teburin gasar, maki uku tsakani da ƴan ukun karshen teburi, bayan cin wasa biyu daga 10 a baya-bayan nan.
Pereira zai fara jagorantar atisayen Forest ranar Litinin, sannan wasansa na farko a matsayin koci shi ne karawar farko a zagayen cike gurbin Europa League, inda za su kara da tsohuwar ƙungiyarsa Fenerbahce a Turkiyya ranar Alhamis.
Bayan nan, Forest za ta karɓi bakuncin Liverpool a gasar Firimiya ranar Lahadi, 22 ga Fabrairu.
Forest ta kafa tarihin amfani da kociya huɗu a kakar tamaula ta Ingila, bayan da ta kori Nuno Espirito Santo da Ange Postecoglou da kuma Sean Dyche da ya fara aiki a watan Satumba.
An kori Dyche ne bayan da Foresrt ta tashi 0-0 da Wolverhampton, wadda ke kasan teburi.
Pereira ya dawo Ingila da horar da tamaula karo na biyu, bayan da aka kore shi daga Wolverhampton a watan Nuwamba bayan shafe wata 11 yana jan ragamar ƙungiyar Molineux.
Barkanmu da shiga sharhi da bayanan wasanni
Jama'a barkanmu da shiga shirin sharhi da bayanan wasanni kai tsaye tare da ni Mohammed Abdu Mamman Skipper Tw.
Za ku iya tafka muhawara a shirin ko bayar da gudunmuwa a BBCHausa Facebook.