Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Abdullahi Bello da Umar Mikail

  1. An kama mutum uku kan zargin hari a wurin ibadar Yahudawa a Birtaniya

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan sanda sun kama wasu mutum uku, maza biyu da mace ɗaya a matsayin waɗanda ake zargi da hannu a harin da aka kai a wani wurin ibadar Yahudawa a garin Manchester.

    Hukumar tsaro ta bayyana cewa ɗaya daga cikin maharan ɗan asalin Syria ne amma yana zama a ƙasar Birtaniya inda firaministan Birtaniya, Keir Starmer ya ce an harbe shi a wajen.

    Firaministan ya yi kira ga ƙasar da ta tashi tsaye domin magance abin da ya kira yawaitar kyamar yahudawa yana mai jaddada buƙatar matakan gaggawa don kare al'ummomin da abin ya shafa.

    Rahotanni sun bayyana cewa an kashe Yahudawa biyu yayin da uku suka samu raunuka.

    Hukumar 'yan sanda da sauran jami'an tsaro suna ci gaba da bincike don gano musabbabin harin da kuma yiwuwar rawar wasu a ciki.

  2. Wasu ƴan majalisar dattawa na son a sake duba dokar ƙwadago

    ...

    Asalin hoton, @NgrSenate

    Wasu ƴanmajalisar dattawan Najeriya sun ce za su gabatar da ƙudiri na neman sake diba dokar kwadago a Najeriya sakamakon rikicin ƙungiyar manyan ma'aikatan kamfanonin iskar gas da fetur ta PENGASSAN da matatar mai ta Dangote.

    Sanata Ali Ndume ya ce duk da an samu maslaha tsakanin ɓangarorin biyu amma rikicin ya yi mummunan tasiri ta hanyar jefa yan Najeriya cikin wahala, don haka akwai buƙatar sake diba dokar tare da yin gyara.

    Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya ce yajin aikin ƙungiyar PENGASSAN na kwana uku ya janyo wa Najeriya hasara na raguwar man da ƙasar ke samarwa da kashi 16.

    A hirarsa da BBC, Sanata Ali Ndume ya ce dole su gudanar da bincike.

  3. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake saduwa a shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa a hantsin Juma'a.

    Shafin na yau zai fi mayar da hankali ne kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da maƙwabtanta, da kuma sauran sassa na duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo.

    Ku kasance da mu.