Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/10/2025.

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 03/10/2025.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Abdullahi Bello da Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Nan za mu rufe wannan shafi na ranar Juma'a.

    Za mu kawo wasu rahotonnin gobe da safe.

  2. Amurka ta ce ta kashe ƙarin mutum huɗu a hari kan jirgin Venezuela

    Amurka ta ce ta kashe mutum huɗu yayin wani hari ta sama kan jirgin ruwan Venezuela da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.

    Sakataren Tsaro Pete Hegseth ya wallafa a shafukan sada zumunta cewa ya jagoranci kai harin ne kudancin Tekun Caribbean bisa umarnin Shugaba Trump.

    Idan ta tabbata, zai zama karo na huɗu kenan da ake kai hari kan jiragen Venezuela a makonnin nan - aƙalla mutum 18 aka kashe zuwa yanzu.

    Venezuela ta yi tir da hare-haren tana mai cewa aniyar Amurka ita ce kifar da gwamnatin ƙasar.

  3. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta amince da ɓangarorin daftarin zaman lafiya na Trump

    Wasu yara a Zirin Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Wani jami'in Hamas ya shaida wa BBC cewa ƙungiyar ta aika da martaninta kan daftarin tsagaita wuta da Amuka ta gabatar game da yaƙin Gaza.

    Jami'in ya ce Hamas ta amince da shi a dunƙule amma tana neman a yi 'yan sauye-sauye a wasu ɓangarori.

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa ƙungiyar wa'adin Lahadi domin amincewa da daftarin ko kuma ta fuskanci "azaba".

    A gefe guda kuma, wasu jami'an gwamnatin Isra'ila masu tsattsauran ra'ayi sun ce indai Hamas ta nemi wani sauyi a daftarin tamkar ta ƙi amincewa da shi ne.

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya amince da shiirin, amma kuma ya koma yana bayyana rashin amincewa da shirin kafa ƙasar Falasɗinu kamar yadda daftarin ya tanada.

  4. Tinubu zai halarci jana'izar mahaifiyar shugaban APC a Jos

    Bola Tinubu

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Bola Tinubu zai ziyarci jihar Filato da ke arewacin ƙasar a gobe Asabar domin halartar jana'izar shugaban jam'iyyarsu ta APC na ƙasa, Farfesa Nantawe Yilwatda.

    Fadar shugaban ta ce Tinubu zai yi wa jagororin addinin Kirista jawabi a hedikwatar cocin COCIN da ke birnin Jos.

    Sanarwar da fadar ta fitar ta ce shugaban zai tafi ne daga kuma ya koma can a rana ɗaya.

  5. Har na mutu ba za a daina kallo na da satar 'yanmatan Chibok ba - Goodluck

    Goodluck jonathan

    Asalin hoton, @GEJonathan

    Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya ce sace ɗalibai mata na sakandaren Chibok ya zama "wani tabo" a kan gwamnatinsa.

    Babban jigo a jam'iyyar adawa ta PDP na magana ne ranar Juma'a a Abuja yayin ƙaddamar da littafin "Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum" wanda tsohon Babban Hafsan Tsaro Janar Lucky Irabor ya rubuta.

    "Taken littafin nan yana da jan hankali sossai. Ɗaya daga cikin manyan tabbai da gwmanatina ke da su shi ne [satar] 'yanmatan Chibok," in ji shi yayin da yake jawabi a taron.

    "Kamar yadda Bishop Kukah ya bayyana, babu wata tiyata da za ta iya kawar da wannan. Tabo ne da zan mutu da shi."

    Sace 'yanmatan da mayaƙan Boko Haram suka yi a 2014 ya jawo hankalin duniya a loakcin, kuma hare-haren ƙungiyar na ɗaya daga cikin abubuwan da suka jawo wa gwamnatin Jonathan faɗuwa a 2015.

  6. Boko Haram na ƙara zama ɓangare na rayuwarmu a Najeriya - Obasanjo

    Obasanjo

    Asalin hoton, Social Media

    Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya ce ayyukan ƙungiyar iƙirarin jihadi ta Boko Haram na ƙoƙarin zama "wani ɓangare na rayuwar 'yan Najeriya" ta yau da kullum.

    Obasanjo na magana ne a yau Juma'a a Abuja yayin ƙaddamar da littafin "Scars: Nigeria’s Journey and the Boko Haram Conundrum" wanda tsohon Babban Hafsan Tsaro Janar Lucky Irabor ya rubuta.

    "Yanzu Boko Haram na zama wani ɓangare na rayuwarmu," in ji shi. "Ya kamata mu amince da hakan? Idan ba za mu amince ba to me ya kamata mu yi?

    "Ina ganin ya kamata mu yi wa kanmu tambayoyin da suka zama dole domin samun damar shawo kan matsalar da take ƙara munana a ƙasarmu," kamar yadda tsohon shugaban ya bayyana, wanda ya rubuta babin farko na littafin.

    Ya kuma buƙaci yin tattaunawa "ta tsanaki" domin lalubo hanyoyin magance matsalar ta Boko Haram a Najeriya.

  7. Yaƙin Gaza: Trump ya bai wa Hamas wa'adin zuwa Lahadi ta amince da daftarinsa

    Donald Trump

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Amurka Donald Trump ya bai wa ƙungiyar Hamas wa'adin zuwa Lahadi domin ta amince da daftarinsa na tsagaita wuta a yaƙin Gaza ko su fuskanci "azaba".

    Trump ya wallafa a shafinsa na dandalin Truth Social yau Juma'a cewa dole ne a cimma yarjejeniya zuwa ƙarfe 6:00 agogon Washington (9:00 na dare agogon Najeriya) ranar Lahadi.

    Daftarin ya nemi kawo ƙarshen yaƙin nan take da kuma sakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su a cikin Gaza cikin awa 72. A madadin haka, Isra'ila za ta saki ɗaruruwan Falasɗinawa da take tsare da su a gidan yari.

    Rahotonni na cewa masu tsakanin na ƙasashen Larabawa da Turkiyya na matsa wa shugabannin Hamas su amince da daftarin, amma wani babban jagoranta ya faɗa wa BBC cewa da wuya su amince da shi.

  8. Cocin Ingila ta naɗa shugaba mace a karon farko

    Dame Sarah Mullally

    Asalin hoton, PA Media

    A karon farko cikin shekara 500, Cocin Ingila ta zaɓi mace a matsayin shugaba.

    Dame Sarah Mullally za ta rike muƙamin babbar jagorar cocin birnin Canterbury wato Arch-bishop, wadda ke da mabiya sama da miliyan 85 a duniya.

    Da take jawabi bayan sanarwar, Sarah ta ce burinta shi ne zama shugaba ga kowa.

    Wakilin BBC ya ce ana kallonta a matsayin wadda take da ƙwarewa wajen jagoranci, amma akwai babban ƙalubale a gabanta.

    Sai dai wata kungiya ta cocin Anglican daga ƙasashen Afirka da Asiya ta soki matakin, tana mai cewa hakan zai ƙara rarraba kawunan cocin Anglican a duniya.

  9. Cote d'Ivoire ta haramta zanga-zangar 'yan hamayya bayan hana su shiga zaɓe

    Jami'an tsaro a Ivory Coast

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar tsaron ƙasar Côte d'Ivoire ta umurci ma’aikatar shari’a da hukumomin tsaro su hana tarurka da zanga-zangar jama’a.

    Sanarwar da hukumar ta fitar a daren jiya Alhamis ta umurci ma’aikatun su ɗauki duk matakan da suka dace don tabbatar da tsaro.

    Wannan umurnin ya zo ne kwana biyu kafin zanga-zangar da manyan ‘yan hamayya, ciki har da tsohon shugaban kasa Laurent Gbagbo, za su yi domin nuna rashin amincewa da hukuncin kwamitin kundin tsarin mulki da ya hana su tsayawa takara a zaben shugaban kasa da za a yi ranar 25 ga watan Oktoba.

    Laurent Gbagbo da tsohon ma'aikacin banki wanda ya koma siyasa Tidjane Thiam, sun yi kira ga magoya bayansu da su halarci zanga-zangar don nuna adawa da wannan hukunci a Adbijan babban birnin kasuwancin ƙasar.

  10. Darajar naira na farfaɗowa

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Farashin dalar Amurka na ci gaba da sauka a Najeriya, inda a wasu kasuwannin bayan fage ake sayar da dalar daya a kusan naira 1,450.

    Wannan farashi ya yi kasa idan aka kwatanta da na makonnin baya, inda darajar dala ta kai har naira 1,560 a wasu wuraren.

    A jihar Kano, cibiyar harkokin kasuwancin arewacin Najeriya, masu hada-hadar kudaden kasashen ketare sun tabbatar da cewa farashin dalar na ta sauka a kullum.

    Shugaban ƙungiyar masu canjin kuɗaɗen waje a jihar, Alhaji Sani Salisu Dada, ya ce, "Dangane da faduwar darajar dala, kusan sati biyu kenan a kowace rana tana karyewa. Idan aka duba baya, dalar ta kai kusan naira 1,560, amma a yau Babban Bankin ƙasa yana sayarwa a kan naira 1,466, yayin da kasuwar bayan fage take a naira 1,450."

    "A halin yanzu farashinmu ya fi armashi, saboda yana kusa da na CBN," in ji shi.

    A cewar Dr Abdulrazak Fagge, masanin kimiyyar kasuwanci a Najeriya, akwai yiwuwar naira ta ƙara daraja kan dala a cikin makon da ke tafe.

    "Daga nan zuwa mako mai zuwa, naira za ta dinga samun tagomashi a kan dala,saboda idan aka lura, dalar na sauka ne a duk fadin duniya, ba a Najeriya kaɗai ba tun bayan da shugaban Amurka, Donald Trump, ya kafa haraji kan wasu kasashe, abin da ya haifar da martani daga wadannan kasashe." in ji shi.

    Rahotanni sun nuna cewa akwai wasu dalilai da suka taimaka wajen rage darajar dalar a Najeriya, ciki har da sabon tsarin da wasu bankuna suka kirkiro na bai wa matafiya damar samun katin ATM mai ɗauke da dala dubu hudu.

  11. Me ya sa har yanzu PDP ta kasa magance matsalolin da ke damunta?

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rikici ya kunno kai a babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya, sakamakon rushe shugbannin reshen jam'iyyar na jihar Akwa Ibom.

    Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Debo Ologunagba ne ya bayar da sanarwar rushe shugabannin reshen daga muƙamansu, tare da maye gurbinsu da wasu.

    To amma matakin ya fuskanci turjiya daga babban sakataren jam'iyyar na ƙasa, Sanata Samuel Anyanwu wanda ya soki matakin tare da neman yin watsi da shi.

    Yana mai cewa an ɗauki matakin ne ba tare da sanin kwamitin zartarwar jam'iyya na ƙasa ba.

    Mista Anyanwu ya ce ya bisa tanadin kundin tsarin mulkin jam'iyyar da aka yi wa gyara a 2017, dakatarwar ba ta da wani tasiri.

  12. Shugaban Madagascar ya yi allawadai da yunƙurin juyin mulki a ƙasar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Madagascar, Andre Rajoelina, ya yi allawadai da abin da ya kira yunƙurin juyin mulki da ke da alaƙa zanga-zangar da ake gudanarwa a ƙasar.

    Rajoelina ya yi jawabi ga al’umma a safiyar yau ta shafinsa na Facebook, bayan mako guda da matasa ke gudanar da zanga-zanga kan gwamnatinsa.

    “An yi amfani da matasa domin tayar da zaune tsaye da kuma haddasa yunƙurin juyin mulki. Abin da nake son fada muku shi ne wasu mutane suna son halaka kasar,” in ji Rajoelina, kamar yadda AFP ta ruwaito.

    A ranar Litinin ɗin da ta gaba ne shugaban kori dukan ministocinsa nufin rage fushin jama’a, amma matakin bai warware korafe-korafen da ake yi ba.

    A yau, rundunar ‘yan sandan kwantar da tarzoma ta rufe tsakiyar birnin Antananarivo, a daidai lokacin da ake sa ran ƙarin zanga-zanga.

    Dubun-dubatan mutane daga cikin masu zanga-zangar sun yi kokarin shiga tsakiyar birnin da safiyar yau, amma ‘yan sanda suka tarwatsa su da hayaki mai sa hawaye.

    Zanga-zangar da ta fara a babban birnin tun ranar Alhamis ɗin makon da ya gabata ta bazu zuwa wasu manyan biranen kasar.

  13. Ina makomar arewacin Najeriya idan matsalar tsaro ta hana yara karatu?

    ...

    Matsalar ƴanbindiga a yankin arewacin Najeriya, babbar damuwa ce da ta shafi fannonin ci gaban yankin da dama.

    Ƴanbindigar sun kwashe shekaru suna ƙaddamar da hare-hare a wasu yankunan arewacin ƙasar tare da kama mutane domin neman kuɗin fansa.

    A wasu lokuta ƴanbindigar kan kai hare-harensu kan makarantu tare da sace ɗalibai.

    Matsalar ta sa an rufe makarantu masu yawa na furamare da sakandire a jihohin da matsalar ta fi ƙamari.

    Wani bincike da jaridar Daily Trust ta gudanar ta gano cewa akwai makarantu furamare da na sakandire aƙalla 180 da aka rufe sakamakon matsalolin tsaro a jihohin Zamfara da Katsina da Sokoto da Kaduna.

  14. Ƴansanda sun fara kame kan amfani da gilashin mota mai duhu a Neja

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴansanda a jihar Niger sun fara aiwatar da dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu a fadin birnin Minna inda suka fara kamen waɗanda suka yi amfani da gilashin mai duhu kuma ba su da lasisi.

    Kwamishinan 'Yan Sanda, CP Adamu Elleman ne da kansa ya sa ido kuma ya jagoranci aikin a cikin birnin, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.

    A yayin aikin da aka gudanar a muhimman wurare a cikin birnin, jami’an ‘yan sanda sun tsayar da motocin da ke amfani da gilashi mai duhu domin tabbatar da sun bi doka ta hanyar mallakar lasisi.

    A ranar Alhamis, CP Elleman ya gana da jami’an ‘yan sanda da sauran ma’aikata da aka tura a fadin birnin, inda ya umarce su da su kasance masu kwarewa da ladabi, da tsayin daka wajen tabbatar da cewa direbobi sun bi ka’idojin amfani da gilashin mota mai duhu.

    Ya kuma yi kira ga masu motocin da suka saka gilashi mai duhu da ba su da lasisi da su je suyi rijista domin su mallaki lasisin cikin gaggawa domin kauce wa hukunci, yana mai jaddada cewa rashin sani ba hujja ba ce.

  15. Indiya da China za su koma zirga-zirgar jirage kai tsaye bayan shekara biyar

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar harkokin wajen Indiya ta ce, ƙasar da China za su koma zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye tsakaninsu a wannan watan bayan dakatarwar shekara biyar.

    Tun a shekarar 2020, babu jiragen da ke tafiya zuwa ƙasashen kai tsaye saboda rikicin da ya faru tsakanin sojojin kasashen biyu a kan iyakar Himalaya inda aƙalla sojojin Indiya 20 da na China 4 suka mutu.

    Wannan lamari ya zama shi ne karo na farko da ya haifar da mutuwa tun 1975, kuma ya haifar da dakatar da dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Babban kamfanin jiragen Indiya, IndiGo, zai fara jigilar fasinjoji kai tsaye tsakanin Kolkata da Guangzhou daga 26 Oktoba.

    Wannan mataki zai sauƙaka hulda tsakanin mutane kuma ya taimaka wajen dawo da dangantaka kasuwanci tsakanin ƙasashen biyu a hankali, ciki har da ɗaukar matakai na rage tashin hankali a kan iyaka.

  16. NAFDAC ta rufe manyan kantunan ƴan China biyu a Abuja

    ...

    Asalin hoton, Nafdac/X

    Hukumar kula da abinci da magunguna ta ƙasa NAFDAC ta rufe manyan kantunan ƴan China biyu da ke yankin Jabi, Abuja saboda karya dokar siyar da kayayyaki a Najeriya.

    Hukumar ta kuma rufe shagunan kayan kwalliya guda takwas a kasuwar Wuse.

    Hukumar ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar Jumma’a kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

    Hukumar ta kuma ce ta rufe kantunan ne bisa umarnin shugabar hukumar, Prof. Mojisola Adeyeye.”

    “Manyan kantunan waɗanda ke a Jabi, an rufe su ne bayan samun ƙorafe-ƙorafe daga masu saye da amfani da kayayyakinsu da kuma binciken da tawagar hukumar ta yi."

    "Binciken da ƙorafe-ƙorafen sun nuna cewa masu kantunan suna sayar da kayan abincin da ba a yi rijistarsu ba da kuma kayayyakin da laƙabinsu kawai a harshen China ne wanda ya saɓawa ƙa’idar NAFDAC wadda ke bukatar fassarar turanci domin masu saye da hukuma su fahimta.

  17. Habasha ta haramta shigo da manyan motoci masu amfani da man fetur

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Ethiopia, Abiy Ahmed, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta haramta shigo da manyan motoci masu amfani da man fetur a ƙasar, a yayin kaddamar da matakin farko na masana’antar iskar gas ta LNG da aka gina a yankin Somali da ke gabashin ƙasar, kamar yadda gidan talabijin na gwamnati ETV ya ruwaito.

    Ya ƙara da cewa, za a ba da dama ga ’yan ƙasa su riƙa shigo da manyan motoci masu amfani da iskar gas ba tare da biyan haraji ba.

    Abiy ya ce wannan mataki ya yi kama da wanda aka ɗauka tun a watan Janairun 2024, lokacin da aka haramta shigo da motoci masu amfani da man fetur.

    Duk da cewa firaministan bai bayyana dalilin haramcin kai tsaye ba, ana danganta wannan mataki da tsadar farashin mai a ƙasar da kuma manufofin gwamnatinsa na yaƙi da tasirin canjin yanayi.

    Masana’antar LNG mai girma da aka kaddamar a yankin Somali ana sa ran za ta samar da sama da lita miliyan 100 na iskar gas a kowace shekara.

    Firaministan ya kuma ƙaddamar da mataki na biyu na aikin, wanda ake sa ran zai samar da lita biliyan 1.33 a duk shekara idan an kammala shi.

  18. Ƙungiyoyi a Madagascar na son shugaban ƙasar ya yi murabus

    ...

    Asalin hoton, AFP via Getty Images

    Ƙungiyoyin masu fafutuka a Madagascar sun kira gagarumin zanga-zangar adawa da gwamnati a babban birnin ƙasar, Antananarivo, domin neman shugaba Andry Rajoelina ya yi murabus.

    Zanga-zangar dai ta fara ne tun ranar 25 ga Satumba sakamakon yawan yanke wutar lantarki da ruwan sha, amma daga bisani ta rikide zuwa neman kawo ƙarshen mulkin shugaban mai shekaru 51 wanda yake kan madafun iko tun 2018.

    A ranar 29 ga Satumba, a yunkurin kwantar da hankulan masu zanga-zanga, Rajoelina ya kori dukan ministocinsa tare da alƙawarin naɗa sabon firaminista.

    ’Yan wasan kwaikwayo da masu tasiri a kafafen sada zumunta da ƙungiyoyin ƙwadago da na farar hula sun bayyana goyon bayansu ga zanga-zangar.

    A yau da safe gidan rediyon Faransa RFI ya ruwaito cewa masu zanga-zangar sun naɗa mutum takwas a matsayin jakadunsu, domin su wakilci muryar gungun masu adawa da gwamnati.

    Sai dai Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce aƙalla mutum 22 ne suka mutu yayin da sama da 100 suka jikkata a rikicin da ta ɓarke a lokacin zanga-zangar da aka gudanar a makon da ya gabata, abin da hukumomin Madagascar suka musanta, suna mai cewa labaran “jita-jita da bayanan karya” ne.

  19. Muna so majalisa ta gaggauta amincewa da sabbin dokokinmu - INEC

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban hukumar zaɓe ta Najeriya INEC, farfesa Mahmood Yakubu, ya buƙaci majalisar dokokin Najeriya da ta gaggauta amincewa da sabbin sauye-sauyen dokokin zaɓe na ƙasar.

    Ya bayyana haka ne a ranar Alhamis a Abuja yayin wata ganawa da tawagar sa ido kan zaɓe ta Tarayyar Turai (EU) ƙarƙashin jagorancin Barry Andrews, wanda shi ma ya jagoranci sa ido a babban zaɓen 2023.

    A farkon shekarar nan ne dai hukumar INEC ta aikewa majalisa wasu dokoki da take so a yi gyara da suka haɗa da;

    • Zaɓen wuri (Early Voting)
    • Zaɓen mazauna ƙasashen waje (Diaspora Voting)
    • Gyara amfani da katin zaɓe na dindindin
    • Bai wa INEC damar naɗa shugabannin zaɓe na jihohi
    • Samar da hukumomin sasanta rikicin zaɓe

    Farfesa Yakubu ya jaddada cewa amincewa da sabbin dokokin da wuri zai taimaka wa INEC wajen tsara shirye-shirye cikin nasara kafin babban zaɓe na gaba.

    Ya bayyana cewa hukumar INEC ta yi nazari sosai kan dukkan shawarwari guda takwas da masu sa ido kan zaɓe ta EU ta bayar da suka shafi hukumar kai tsaye a rahotonsu na zaɓen 2023.

    Yakubu ya ce hukumar ta riga ta ɗauki matakai a kan waɗanda ke buƙatar sauye-sauye cikin gida, sannan tana aiki tare da sauran sassa kan shawarwari da suka shafi kowa.

    Ya kuma ce hukumar tana jiran kammala nazarin sauye-sauyen doka da majalisar dokoki ke yi.

    Shugaban INEC ɗin ya ƙara da cewa shawarwarin EU da na sauran masu sa ido, na cikin muhimman abubuwan da aka yi la’akari da su yayin nazarin bayan zaɓe na 2023.

  20. TikTok na nuna abubuwan batsa ga shafukan yara — Rahoto

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani sabon rahoto na wata ƙungiyar fafutika ta Global Witness da ke sa ido kan kamfanonin sadarwa ya ce TikTok na bankado abubuwan batsa ga shafukan yara.

    Masu bincike sun ƙirƙiri shafin yara na bogi tare da saita ka'idoji na kariya ga yara, amma duk da haka TikTok ya turo masu abubuwan batsa.

    Dandalin TiKTiko ya ce zai yi bincike tare da goge shafukan da kuma inganta kafarsa.

    Global Witness dai ƙungiya ce da ke gudanar da binciken yadda manyan kamfanonin fasaha ke tasiri ga tattaunawar 'yancin dan adam da dimokuraɗiyya da kuma sauyin yanayi