Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 20/11/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya. 20/11/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, da Ibrahim Yusuf Mohammed da Isiyaku Muhammed

  1. MSF ta dakatar da aiki a babban birnin Haiti saboda hare-hare

    Ƙungiyar bayar da agaji ta likitoci Médecins Sans Frontières (MSF) ta dakatar da ayyukanta a babban birnin ƙasar Haiti, Port-au-Prince, sakamakon wani mummunan hari da aka kai wa ma'aikatanta da kuma zargin kisan wasu majinyata biyu da ta ke zargin jami'an ƴan sandan Haiti da aikatawa.

    Kungiyar agajin ta yi tir da harin a cikin wata sanarwa da ta fitar a makon da ya gabata, inda ta ce an barba wa jami’anta hayaki mai sa hawaye, kuma an tsare su ba tare da son ransu ba na tsawon sa’o’i.

    Lamarin ya faru ne yayin da tashin hankali ke ƙara ta'azzara a ƙasar.

    Kimanin mutane 25 ne aka kashe a birnin Port-au-Prince a ranar Talata kaɗai, a wani harin da ƴansanda suka ce artabu ne tsakaninsu da wasu ƴan daba suka yi yunƙurin kutsawa wata unguwar masu hannu da shuni.

    A siyasance ma, lamarin na ci gaba da yin muni yayin da majalisar mulkin ƙasar ta kori Firaministan riƙon ƙwarya Garry Conille a wannan watan - kasa da watanni shida da hawansa mulki.

  2. Ɗan gwagwarmayar dimokraɗiyya a Hong Kong ya musanta haɗa baki da ƙasashen waje

    Ɗaya daga cikin masu fafutukar tabbatar da dimokuraɗiyya a Hong Kong, Jimmy Lai, ya bayyana a gaban kotu a karon farko a shari'ar da ake yi masa na cin amanar ƙasa da ka iya kai wa a yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai.

    Ana zargin wanda ya kafa jaridar Apple Daily mai shekara 76, da haɗa baki da wasu ƴan ƙasashen waje domin ya wa gwamnatin Hong Kong zagon ƙasa.

    Sai dai Lai ya shaidawa kotun a ranar Laraba cewa "bai taɓa amfani da abokan hulɗarsa na ƙasashen waje ba, waɗanda suka haɗa da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Amurka Mike Pence da kuma tsohuwar shugabar Taiwan Tsai Ing-wen, wajen yin tasiri kan manufofin ƙetare na Hong Kong.

    Tuni dai Lai ke zaman gidan yari bisa wasu laifuffuka da ake same shi da aikatawa da ake zarginsa da hannu a zanga-zangar kafa mulkin dimokradiyya a shekarar 2019, wanda ya kai ga China ta kafa dokar tsaron ƙasa (NSL) a birnin.

    Gurfanar tasa a gaban kotun na zuwa ne kwana guda bayan an yanke hukunci kan masu fafutukar tabbatar da dimokuradiyya guda 45 - wani ɓangare na kungiyar da aka fi sani da Hong Kong 47.

    Lai yana ɗaya daga cikin ɗaruruwan masu fafutuka, da ƴan majalisa da masu zanga-zangar da aka tsare a ƙarƙashin dokar NSL, wanda Beijing ke ikirarin ya zama dole don kwantar da tarzomar Hong Kong da ta ɓarke a shekarar 2019.

  3. Sojoji za su gurfanar da jagoran ƴan adawan Uganda

    Uwargidan jagoran ƴan adawar ƙasar Uganda Kizza Besigye ta ce an yi damƙe a Kenya da ke makwabtaka da ƙasar tare da mayar da shi gida inda ake tsare da shi a gidan yarin sojoji.

    A cikin saƙon da ta wallafa a shafin X, Winnie Byanyima ta rubuta cewa an kama mijinta a Nairobi babban birnin ƙasar Kenya a ranar Asabar ɗin da ta gabata yayin wani taron ƙaddamar da littafi.

    "Yanzu an tabbatar min da cewa yana gidan kurkukun sojoji a Kampala," in ji ta, inda ta buƙaci gwamnatin Uganda ta sako mijinta.

    Kakakin rundunar sojin ƙasar Felix Kulayigye ya shaidawa kamfanin dillancin labaran ƙasar Uganda cewa za a gurfanar da shi a gaban kotu nan ba da jimawa ba.

    Bai fito fili ya bayyana ko sojoji na riƙe da shi ba. BBC ta nemi gwamnatin Uganda ta yi tsokaci, amma ya zuwa yanzu ba ta ce komai ba.

    Besigye, mai shekaru 68, ya jagoranci jam'iyyar FDC, inda ya fafata tare da shan kaye a zaɓukan shugaban ƙasa guda huɗu a hannun shugaba mai ci Yoweri Museveni, wanda ke kan karagar mulki tun shekara ta 1986.

  4. Babu sauran jagororin Hamas a Doha - Gwamnatin Qatar'

    Ɗaya daga cikin manyan jagororin Hamas da ba sa zama a cikin Gaza, Khali al-Hayya, da sauran waɗanda suke shige wa ƙungiyar gaba a tattaunawa da sauran al'amuran shugabanci sun bar birnin Doha, kamar yadda gwamnatin Qatar da wani babban jami'in gwamnatin Falasɗinu suka bayyana.

    Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Qatar ya ce yanzu ofishin Hamas ba ya wani aiki sosai saboda Qatar ta dakatar da yunƙurin da take yi na shiga tsakani domin samar da maslahar tsagaita wuta a Gaza, duk da cewa ta ce ba wai ta rufe ofishin ba ne baki ɗaya.

    Jami'in gwamnatin Falasɗinun ya shaida wa BBC cewa jagororin na Hamas sun canja salonsu a yankin, kuma za su daina bayyana inda suke domin kiyaye mutuncin ƙasashen da suke zaune.

    Amma sun ce akwai alamu Hayya na Turkiyya domin ya sha yin tafiya zuwa ƙasar a cikin watanni biyu da suka gabata.

    Jami'in ya ƙara da ewa Qatar ba ta kori ƴan Hamas ba, amma dai ya ce ƙasar na taka-tsantsan ne domin gudun shiga matsala da gwamnatin Amurka.

    Tun a shekarar 2012 ce shugabannin ɓangaren siyasa na Hamas suke zama a Qatar.

  5. Sarakunan gargajiya ba sa tsoron gwamnoni - Sarkin Musulmi

    Mai alfarma Sarkin Musulmi, Sa'ad Mohammad Abubakar II ya musanta maganar da ake yi cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

    Sarkin musulmin ya ce sarakunan gargajiya sun kasance jagorori a ƙasar tun kafin ta samu ƴancin kai, sannan ya ƙara da cewa sarakunan sun fi gwamnonin fahimtar yanayin ƙasar.

    Ya bayyana hakan ne a wani taro na ƙungiyar ci gaban matasan arewacin Najeriya da Gidauniyar Tunawa da Sardauna ta shirya a Abuja a ranar Talata kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Tun da farko, tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu, ya bayyana cewa sarakunan gargajiya suna tsoron gwamnoni.

    Da yake mayar da martani, sarkin na Musulmi ya ce, "Na ji an ce sarakunan gargajiya na tsoron gwamnoninsu. Ba haka ba ne, sarakuna ba sa tsoron gwamnoni. Sarakunan gargajiya suna girmama kansu ne, sannan suna girmamma gwamnonin domin suna da iko a jihohinsu.

    "Duk lokacin da wani abu ya faru, muna mayar da shi zuwa ga Allah ne. Muna kawo sauyi, kuma muna karɓar sauyi a yadda suka zo mana. Duk mun sani, akwai sarakunan gargajiya a Najeriya tun a shekarar 1824, amma a shekarar 1960 ce Najeriya ta samu ƴanci."

  6. An kama sojoji a Brazil bisa zargin yunƙurin kashe shugaban ƙasa Lula a 2022

    Ƴansandan Brazil sun kama mutum biyar da ake zargi da yunƙurin kashe shugaban ƙasar, Luiz Inácio Lula da Silva kafin a rantsar da shi.

    Huɗu daga cikin waɗanda aka kama sojoji ne, sai wani ɗansanda, kamar yadda kafofin watsa labarai na ƙasar suka ruwaito.

    Ana zarginsu ne da kitsa kashe Lula da mataimakinsa Geraldo Alckmin a ranar 15 ga Disamba bayan sun lashe zaɓen shugaban ƙasar, kimanin mako biyu kafin a rantsar da su.

    Lula ya lashe zaɓe a Oktoban 2022, inda ya kayar da shugaban ƙasar mai-ci, Jair Bolsonaro, wanda bai bayyana amincewa da kayin ba.

    Haka kuma mako ɗaya bayan an rantsar da Lula, magoya bayan Bolsonaro sun kutsa majalisa da Kotun Ƙolin da fadar shugaban ƙasar, suka yi ɓarna, kafin ƴansanda suka fatattake su, tare da kama wasu.

    Tun lokacin ne ake binciken lamarin da ma na yunƙurin kashe Lula, amma wannan karo na farko da aka tsare waɗanda ake zargi suna da hannu.

  7. Ma'aikata a Zamfara sun yi barazanar shiga yajin aiki

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC rehen jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya ta sanar da shirin ma’aikatan jihar na tsunduma yajin aiki nan da ƙarshen wannan wata na Nuwamba, muddin gwamnatin jihar ba ta fara biyan sabon albashi mafi ƙaranci na naira dubu saba’in ba.

    Ƙungiyar ta ce matakin jan ƙafar na nuna yadda wasu gwamnonin jihohi ba su jin tausayin ma’aikata musamman a wannan lokaci da al’umma ke fama da tsadar rayuwa.

    Gwamnatin Zamfara dai ta sanar da amincewa da naira dubu 70 ne a matsayin mafi ƙarancin albashi ga ma'aikatan jihar.

  8. Ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziki sun ƙaddamar da yaƙi da yunwa da talauci

    Ƙungiyar ƙasashe masu ƙarfin tattalin arziƙi na duniya ta G20 ta ƙaddamar da shirin yaƙi da yunwa da kuma kawar da talauci a yayin buɗe taronta na shekara-shekara karo na 19 wanda ake yi a birnin Rio de Janeiro na Brazil.

    Shirin da duka ƙasashen ƙungiiyar suka sanyawa hannu za a gudanar da shi ne tsakanin shekarun 2025 zuwa 2030.

    Shugaban Brazil Luiz Lula da Silva ya ce shirin wanda aka fara aiwatar da shi tun daga watan Yuli tuni na da goyon bayan sama da ƙasashe 80 a duniya, bayan ga gwamman gwamnatoci da ƙungiyoyin fararen hula.

  9. Farashin kayayyaki sun tashi a Burtaniya saboda tsadar makamashi

    Hauhawar farashin kayayyaki a Burtaniya ya ƙaru a watan da ya gabata saboda ƙaruwar kuɗin makamashi, kamar yadda alƙaluman gwamnati suka nuna.

    Hauhawar farashin, ya ƙaru ne da kashi 2.3 a shekarar a watan Oktoba, wanda ƙari ne daga kashi 1.7 a watan Satumba.

    Kuɗin wutar lantarki da gas da matsakaicin gida ke biya ya tashi ne zuwa £149 a watan da ya gabata, amma dai duk da haka farashin na tashi ne kaɗan-kaɗan.

    Grant Fitzner, babban masanin tattalin arziki a Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar ya ce farashin makamashin na cikin abubuwan da suke jawo tashin farashin kayayyaki a ƙasar.

    "Kayayyakin da masana'antu ke buƙata sun yi tsada, kuma suna ƙara tsadar, ga kuma faɗuwar farashin ɗanyen mai," in ji shi.

    Wani mazaunin Burtaniya mai suna Darren Jones, ya ce gwamnati ta san, "iyalai na shan wahala saboda tsadar rayuwa. Muna tunanin akwai abin da ya kamata gwamnati ta yi."

  10. Ƴan Boko Haram sun kashe sojoji a Borno

    Ƴan Boko Haram sun kai hari a wani sansanin sojoji da ke Borno, inda suka kashe wasu sojoji, sannan ake tunanin sun yi awon gaba da wasu makamai.

    Wata majiya ce ta tabbatar wa tashar Channels aukuwar lamarin, inda ta ce mayaƙan Boko Haram na ɓangaren IS ne suka kai farmakin a sansanin soji da ke garin Kareto a ranar Asabar.

    Majiya ta ce an kashe kusan sojoji 20, amma hedkwatar tsaro ta Najeriya ta ce sojoji biyar aka kashe mata a harin.

    Sai dai majiyar ta ƙara da cewa an gwabza yaƙi sosai tsakanin ƴan Boko Haram ɗin da sojoji, sannan wani ɗan ƙunar bakin wake ya tayar da motar da yake ciki, wanda a ƙarshe ƴan Boko Haram ɗin suka ƙona motocin sojoji 14.

    A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Borno ta yi sojojin Najeriya jaje bisa rasa jami'anta a garin na Kareto.

  11. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Laraba daga nan sashen Hausa na BBC, inda za mu kawo muku labarai kai-tsaye na abubuwan da suke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.