A Najeriya, majalisar dattawan ƙasar ta amince shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'aiakata ta kasar, wato Code of Conduct Tribunal, Ɗanladi Umar daga muƙaminsa.
Matakin ya zo ne sakamakon abin da majalisar ta kira wasu halaye na rashin ɗa'a da ba za a taɓa amincewa da su ba, da suka haɗa har zargin da ya shafi cin hanci da rashawa.
Kuma majalisar ta amince da naɗin wanda zai gaji shugaban kotun da ta sauke.
An dai kwashe shekaru da dama ana ta kai ruwa rana da shugaban kotin da ɓangarorin gwamnati da dama.
Bayanai daga zauren majalisar dattawan Najeriyar, sun ce
'yan majalisar sun yi amfani ne da tanadin sashe na 157 na
kundin tsarin mulkin ƙasar, wajen sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'ikatan daga
muƙaminsa, a zamansu na ranar Laraba.
Majalisar dattawan, ta ce ta ɗauki wannan mataki ne,
domin kare martaba da ƙimar kotun ta ɗa'ar ma'ikata.
Bayan ta sami jerin ƙorafe-ƙorafe da zarge-zarge masu
yawa kan shugaban kotun, waɗanda suka shafi cin hanci da rashawa da dai sauran
wasu laifuka da suka yi hannun riga da ɗa'ar ma'aikata.
Hakan kuma ya sa majalisar dattawan ta gayyaci shugaban
kotun a lokuta da dama, don ya bayyana a gaban tarukan bin ba'asin zarge-zargen
da ake yi masa. Amma ko da ya halarci zaman kwamitin bin ba'asin sau ɗaya, sai
ya ɗage ƙafa.
A ƙarshe dai, yau 'yan majalisar dattawan Najeriyar suka
amince da ƙudirin da ya nemi sauke shugaban kotun ɗa'ar ma'aikatan, da
gagarumin rinjayen mutum tamanin da uku cikin ɗari da tara.
Nan take kuma 'yan majalisar dattawan suka amince da naɗin
AbdulLahi Usman Bello, wanda shugaba Bola Ahmed Tinubu ya miƙa wa majalisar
sunansa, don ya maye gurbin wanda aka sauke. Kana suka umarci sabon naɗin ya
kama aiki ba tare da ɓata lokaci ba.