Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na 14/07/25

Rahoto kai-tsaye

Ibrahim Haruna Kakangi da Isiyaku Muhammed da Aisha Aliyu Jaafar da Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Firaministan Indiya ya aike da saƙon ta'aziyyar rasuwar Buhari

    Firaministan India Narendra Modi

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan India Narendra Modi ya shiga jerin shugabanni da kuma ɗimbim alummar da ke miƙa ta'aziyyarsu bisa rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.

    A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Litinin, Modi ya jinjinawa kaifin basira da jajircewar marigayi tsohon shugaban ƙasar kan ƙarfafa alaƙar India da Najeriya a lokacin mulkinsa.

    Ya kuma ƙara da cewa '' Na shiga matuƙar damuwa da rasuwar tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.''

    '' Ina iya tuna tarukanmu da tattaunawarmu a lokuta da dama''

    ''Da ni da alummar India su biliyan 1.4, munna miƙa ta'aziyyarmu ga iyalansa da gwamnati da kuma mutanen Najeriya.'' in ji shi.

  2. Dakarun RSF na korar marasa lafiya daga asibiti - Ma'aikatan jinƙai

    Asibiti a Sudan

    Masu aikin jinƙai na sa-kai da ke Sudan sun ce dakarun RSF na ta korar marasa lafiya daga asibiti a Yammacin jihar Kordofan saboda a bai wa mayaƙansu da suka jikkata kulawa.

    Sun kuma ce mayakan RSF ɗin na dukan wasu daga cikinsu.

    Rahoton ya biyo bayan gwabza yaƙi a kwanakin ƙarshen mako a birnin Um Samima, wanda sojojin Sudan da kuma dakarun RSF ke cewa suna da iko kai.

    Ana kuma gwabza mummunar yaƙi a yankin El Fasher a yammacin yankin Darfur, inda RSF ke ta ƙoƙarin kwacewa fiye da shekara daya da ta wuce wanda hakan ya kai ga dubban fararen hula tserewa.

  3. An ɗage jana'izar marigayi Muhammadu Buhari zuwa Talata

    Marigayi Buhari

    Asalin hoton, Getty Images

    An ɗage jana'izar marigayi tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zuwa karfe 2 na ranar Talata a mahaifarsa Daura, da ke jihar Katsina.

    Tun da farko an tsara gudanar da jana'izar a yau Litinin bayan dawo da gawarsa daga birnin Landan inda ya rasu.

    Da yake magana da manema labarai a Katsina, gwamnan jihar Dikko Radda ya bayyana cewa bayan tattaunawa da iyalan marigayin da kuma makusantansa da ke Landa, an amince za a dawo da gawarsa gobe Talata da karfe 12 na rana.

    Gwamnan ya kuma miƙa ta'aziyya ga iyalan tsohon shugaban ƙasar da ƴan Najeriya a madadin kansa, gwamnati da kuma mutanen jihar Katsina.

  4. Fiye da mutane 30 sun mutu sakamakon rikici tsakanin wasu alummomi a Syria

    Rahotanni sun bayyana cewa rikici tsakanin ƴan ƙabilar Bedouin waɗanda akasari Musulmai ne da kuma mayaƙan alummar Druze a Syria ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fiye da talatin da kuma jikkatar aƙalla 100.

    Ma'akatar harkokin cikin gida ta Syria ta ce an gwabza faɗan ne a birnin Sweida .

    Shaidu sun bayyana cewa rikicin ya ɓarke ne bayan yi wa wani ɗan kasuwa ɗan alummar Druze sata tare da garkuwa da shi a ranar Juma'a wanda ya kai ga hare haren ramuwar gayya.

    Gwamnan birnin ya yi kiran kawo ƙarshen rikicin kuma hukumomi a Syria sun aike da jam'ian tsaro domin su shawo kan lamarin.

  5. Mutanen da aka kashe tun fara yaƙin Gaza sun zarce 58,000 - Ma'aikatar lafiya

    Gaza

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar lafiya ta Gaza ta ce adadin mutanen da aka kashe a yankin tun lokacin da aka soma yaki da Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoba 2023 ya zarce 58,000.

    Rahotanni sun bayyana cewa aƙalla Falasɗinawa 18 ne suka mutu zuwa safiyar Litinin.

    Rundunar sojin Isra'ila ta ɗora alhakin harin da aka kai Gaza ranar Lahadi wanda ya halaka Falasɗinawa da dama - shida daga cikinsu yara ƙanana kan abin da ta kira ''tangarɗar na'ura''.

    Shaidu sun ce wani jirgi mara matuƙi ne ya faɗa kan taron jama'a a wani sansanin rabon ruwa a sansanin ƴangudun hijira na Nuseirat.

  6. Cambodia za ta fara tilasta wa fararen hula shiga aikin soja

    Sojojin ruwa na Cambodia

    Asalin hoton, Getty Images

    Cambodia ta ce daga shekara mai zuwa za ta soma tilasta maza fararen hula shiga aikin soji, a yayin da ake zaman tankiya tsakaninta da makwafciyarta Thailand.

    An samar da dokar da ta bayar da damar yin hakan tun shekaru ashirin da suka gabata, sai dai har yanzu ba a soma aiwatarwa ba.

    Da ya ke sanar da hakan, Firaministan Cambodia Hun Manet ya kuma ce za a tsawaita wa'adin aikin sojin daga watanni 18 zuwa shekara biyu.

    Ya ce wata ƴar hatsaniya da aka samu tsakanin sojojin Cambodia da na Thailand sakamakon wani rikici kan iyaka a watan Mayu ne ya nuna buƙatar yin haka.

  7. Shugaba Trump ya ce Amurka za ta aike wa Ukraine naurorin kakkaɓe makamai masu linzami

    Trump

    Asalin hoton, EPA

    Shugaba Donald Trump ya ce Amurka za ta aike wa Ukraine makaman da ke kakkaɓo makamai masu linzami samfurin Patriots, makonni biyu bayan da Washington ta ce za ta dakatar da tura wa ƙasar makamai.

    Shugaban Amurkar ya ce tura makaman ya zama wajibi domin kare Ukraine, yayin da ya ce Shugaban Rasha Vladmir Putin yana daɗin baki amma daga bisani kuma ya kai hari.

    Trump ɗin ya ce bai gama tantance adadin makaman ba amma za su aika musu saboda suna buƙatar kariya, kuma Tarayyar Turai ce za ta biya kuɗin makaman, Amurka ba za ta biya komai ba.

    Mista Trump ya ce zai yi babbar sanarwa kan Rasha a yau Litinin.

    A makonnin baya-bayan nan, Rasha ta zafafa hare-haren jirage marasa matuƙa da na makamai masu linzami kan biranen Ukraine, lamarin da ya illata farar hula masu yawa.

  8. Buhari jajirtaccen abokin aiki ne kuma dattijon kirki - Goodluck Jonathan

    Marigayi Muhammadu Buhari da Goodluck Jonathan

    Asalin hoton, TWITTER/GARBA SHEHU

    Tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana marigayi tsohon shugaban ƙasar Muhammadu Buhari a matsayin mutumin da ya sadaukar da rayuwarsa ga aikinsa kuma ya yi wa ƙasar aiki yana cike da kishin ta.''

    Bayan samun labarin rasuwar mutumin da ya cire shi daga ofishin shugaban ƙasa a 2015, Mista Jonathan ya bayyana alhinin sa inda ya ce Najeriya ta yi rashin ɗaya daga cikin jigo a shugabanninta.

    Goodluck Jonathan ya kasance shi ne shugaban ƙasa mai ci a jamiyyar PDP wanda kuma ke neman wa'adi na biyu, kafin Muhammadu Buhari na jamiyyar APC ya kayar da shi a zaɓen shugaban ƙasa.

    '' Na yi rashin abokin aiki mai mutumci kuma dattijon arziƙi. Tarihinsa zai ci gaba da kasancewa a zukatan mutanen da ke mutunta gaskiya da sadaukarwa da juriya da kuma jajircewa ga bin dokokin ƙasa,'' in ji Jonathan.

    Ya bayyana Buhari a matsayin shugaba na musamman, mai kishin kasa, dattijo wanda ya yi wa kasa hidima a matsayin shugaban mulkin soji da shugaban farar hula dai-dai gwargwadon iyawarsa.

    '' Za a tuna shi a matsayin shugaba mai ƙarfin zuciya, soja mai kiyaye dokokin aiki, kuma ma'aikacin gwamnati mai jajircewa da ya yi ayyukan da za a yaba wajen samar da zaman lafiya da ci gaba ga ƙasar mu,'' a cewar Jonathan.

  9. Buhari ya rayu cikin sadaukarwa ga Najeriya - Yemi Osinbajo

    Muhammadu Buhari da Yemi Osinbajo

    Asalin hoton, Bayo Omoboriowo

    Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya miƙa ta'aziyyarsa bisa rasuwar tsohon maigidansa, Muhammadu Buhari.

    Osinbajo ya kasance abokin takarar Buhari a zaɓukan shugaban ƙasa na 2015 da 2019, kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa tare da Buhari na shekara takwas.

    A saƙon ta'aziyyar da ya aike, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya wallafa cewa : ''Ni da mai dakina Dolapo mun sami labarin rasuwar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da rana''

    Ya kuma ce ya yi magana da Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasar, da kuma ɗansa Yusuf Buhari domin miƙa ta'aziyyarsa da kuma taya su alhinin rashinsa, wanda a cewarsa yana alfahari da aiki tare da shi na tsawon shekara 8 da ba zai taɓa mantawa dasu ba.

    Mista Osinbajo ya ce Najeriya ta yi asarar mai ƙishin ƙasa na asali, wanda rayuwarsa ta kasance cike da ayyukan da ke nuna sadaukarwa ga ƙasarsa da yake ƙauna.

    '' Tarihin Buhari zai bayar da shaida game da martaba aikin gwamnati da ke cike da gaskiya, da kuma sadaukarwa ga cigaban alumma,'' in ji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.

  10. Shettima ya isa Landan domin raka gawar marigayi Muhammadu Buhari Najeriya

    mataimakin shugaban Najeriya Kashin Shettima a filin jirgin sama a Landan

    Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA/FACEBOOK

    A safiyar yau Litinin ne mataimakin shugaban Najeriya Kashim Shettima ya isa birnin Landan domin raka gawar marigayi shugaba Muhammadu Buhari da ya rasu a wani asibiti da ke birnin a jiya Lahadi bayan jinya zuwa Najeriya.

    Mataimakin shugaban ƙasar ya isa ne tare da rakiyar shugaban ma'aikatan fadar gwamnati Femi Gbajabiamila.

    Sun kuma sami tarba daga Ministan harkokin waje Yusuf Tuggar, da Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum a filin jirgin.

    Ana sa ran za su dawo Najeriya a yau domin jana'izar tsohon shugaban ƙasar.

    mataimakin shugaban Najeriya Kashin Shettima a filin jirgin sama a Landan

    Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA/FACEBOOK

    mataimakin shugaban Najeriya Kashin Shettima a filin jirgin sama a Landan

    Asalin hoton, KASHIM SHETTIMA/FACEBOOK

  11. Buhari ya yi wa Najeriya iya ƙoƙarinsa - Obasanjo

    BUHARI DA OBASANJO

    Asalin hoton, NIGERIA PRESIDENCY

    Tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana rasuwar tsohon shugaba Muhammadu Buhari a matsayin rashi da Najeriya, ba ga iyalinsa kaɗai ba.

    Ya kuma ce ''ana buƙatar kwarewar duk mutanen da suka samu damar jagorantar kasar nan a baya domin fitar da kasar a cikin halin da take ciki.''

    Obasanjo ya kuma ce Buhari ya yi iya ƙoƙarinsa ga Najeriya, kuma ya yi adduar Allah ya yafe masa kurakurensa ya kuma a aljannah ce makomarsa.

  12. Buhari mutum ne mai gaskiya da kishin ƙasa - IBB

    IBB

    Asalin hoton, Getty Images

    Tsohon shugaban mulkin soji a Najeriya Janar Ibrahim Babangida ya miƙa ta'aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari inda ya bayyana shi da mutum mai kyawawan halaye, kuma mai kishin ƙasa.

    IBB wanda ya hamɓarar da Buhari daga mulkin soji a ranar 27 ga watan Agustan 1985, ya bayyana shi a matsayin mutumin da ko bayan barinsa mulki, ya cigaba da kasance abin koyi ga mutane da dama kuma abin misali.

    Ya kuma tuna lokacin da ya fara haɗuwa da marigayi Buhari a shekarar 1962 a lokacin da suka shiga makarantar horar da sojoji da ke Kaduna.

    "Tun a lokacin Muhammadu Buhari mutum ne na daban, bai cika magana ba, amma yana da jajircewa, kuma mutum ne mai bin ƙa'ida kuma mai sauƙin kai, mai tsananin kishin ƙasa ne da sadaukar da kai ga Najeriya. A cikin shekarun, mun kasance tare cikin wahala da daɗi da jarabawa da kuma cin nasara da rashinsa.''

    Babangida ya ce duk da shi da Buhari sukan saɓa kan wasu abubuwa, kamar yadda a kan samu tsakanin ƴanuwa, "amma ko kaɗan ban taɓa kokwanto game da gaskiyarsa da kishin ƙasa ba.

    ''Bayan aiki kuma na san shi a matsayin mutum mai addini wanda kuma ke tafiyar da rayuwarsa cikin tawali'u.'' in ji tsohon shugaban mulkin sojin.

  13. Buɗewa

    Masu bibiyar shafinmu na BBC Hausa kai tsaye, barkanmu da safiyar Litinin. Za mu kawo muku muhimman labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwaftanta da ma sauran sassan duniya.

    Za kuma ku iya ziyartar shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da kuma tafka muhawa.

    Ku kasance tare da mu