Mahara sun hallaka mutum 45 a jihar Benue
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia ya yi Alla-wadai da da hare-hare da aka kai jihar, waɗanda suka janyo mutuwar mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Gwamnan ya ce babu abin da zai sa a salwantar da ran ɗan'adam.
Ya kuma ce ba zai gajiya ba har sai ya samar da zaman lafiya a jihar.
Jami'ai sun ce aƙalla mutum 45 ne aka kashe yayin wani hari da aka kai cikin dare a jihar Benue.
Shaidu sun ce ana zargin wasu makiyaya da kai harin, inda ƴansanda suka ce sun yi artabu da maharan.
An ƙona gidaje da dama a harin da aka kai garin Yelewata.
Rikici tsakanin manoma da makiyaya dai ba sabon abu bane a Najeriya.
Mutum 25 ne suka mutu kwanaki biyu da suka gabata bayan hari da ƴanbindiga suka kai Makurdi.
Ko a makonni biyu da suka wuce ma, ƴanbindiga sun kashe aƙalla mutum 25 a wasu hare-hare guda biyu a jihar ta Benue.