Man United na nazari kan Eze da Semenyo, Inter ta sanya Calhanoglu a kasuwa

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 2

Manchester United za ta karkata akalarta wajen zawarcin ɗan wasan Crystal Palace da Ingila Eberechi Eze, mai shekara 26, ko kuma ɗan wasan gaban Bournemouth ɗan ƙasar Ghana Antoine Semenyo, mai shekara 25, idan har ta kasa samun ɗan wasan Brentford da Kamaru Bryan Mbuemo, mai shekara 25. (ESPN)

Inter Milan ta shirya sauraron tayi kan ɗan wasan tsakiya Hakan Calhanoglu, mai shekara 31, inda Galatasaray ke nuna sha'awar ɗaukar dan wasan na ƙasar Turkiyya. (Gazetta)

Arsenal na shirin gabatar da sabon tayi kan ɗan wasan gaba na Sporting ɗan ƙasar Sweden Viktor Gyokeres, mai shekara 27, a daidai lokacin da Atletico Madrid ita ma ta nuna sha'awar zawarcin ɗan wasan. Tuni dai Gyokeres ya yi watsi da batun komawa Manchester United. (Record)

Ana sa ran Tottenham Hotspur za ta sanya hannu kan yarjejeniyar din-din-din da ɗan wasan gaban Bayern Munich Mathys Tel, mai shekara 20, bayan zaman aro da ya yi a ƙungiyar. (Bild)

AC Milan ta tuntubi Valencia kan yiwuwar ɗaukar ɗan wasan tsakiya Javi Guerra mai shekara 22 (Calciomercato).

Bayer Leverkusen tana son ɗan wasan gaban Netherlands Justin Kluivert bayan ta sayar da ɗan wasan tsakiyar Jamus Florian Wirtz, mai shekara 22, ga Liverpool, kuma tuni ta tuntuɓi Bournemouth game da yiwuwar ɗaukar ɗan wasan mai shekara 26. (Mail)

West Ham ta tattauna da Reims kan cinikin kan ɗan wasan gaban Gambia Adama Bojang, mai shekara 21, inda ake sa ran za ta miƙa tayin fam miliyan 11. (Mirror)

Bournemouth ta amince da cinikin ɗan wasan baya Adrien Truffert, mai shekara 23, daga Rennes, wanda zai bai wa ɗan wasan bayanta ɗan ƙasar Hungary Milos Kerkez, mai shekara 21, damar komawa Liverpool. (ESPN)

Wolves na gwagwarmayar ci gaba da riƙe kocinsu ɗan ƙasar Portugal Vitor Pereira, a daidai lokacin da Benfica ke neman ɗaukarsa zuwa birnin Lisbon. (Sun)

Ɗan wasan tsakiya na ƙasar Sifaniya Fer Lopez, mai shekara 21, ya amince ya koma Wolverhampton Wanderers daga Celta Vigo amma har yanzu ƙungiyoyin ba su cimma matsaya kan farashin ɗan wasan ba. (Diario AS)

Southampton na nazari kan ɗan wasan Cologne dan ƙasar Amurka Damion Downs, mai shekara 20. (Sky Germany)