Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/06/2025

Rahoto kai-tsaye

Ahmad Bawage

  1. Rufewa

    Karshen rahotannin kenan a wannan shafi.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Za ku iya ci gaba da bibiyar shafinmu na intanet bbchausa.com domin samun ƙarin labarai.

    Ahmad Bawage ke cewa mu zama lafiya.

  2. Hotunan sabon harin da Iran ta kai Isra'ila

  3. Labarai da dumi-dumi, Iran ta kaddamar da sabbin hare-hare kan birnin Tel Aviv

    Gidan talabijin na ƙasar Iran ya ce ƙasar ta kai hari kan Tel Aviv, Haifa da kuma sauran birane tare da amfani da "gomman makaman linzami da kuma jirage marasa matuki".

    Ta kuma ruwaito cewa makaman linzamin sun "zarta garkuwar tsaron samaniyar Isra'ila" - sai dai sojojin Isra'ila ba su ce komai ba.

  4. Babu abin da muke so face sauyin gwamnati a Iran - Netanyahu

    A tattaunawar da aka yi da Benjamin Netanyahu, an tambaye shi ko ganin sauyin gwamnati a Iran yana cikin abubuwa da Isra'ila ke ƙoƙari a kai.

    "Babu abin da muke so face sauyin gwamnati, saboda gwamnatin Iran tana da rauni," in ji shi.

    Netanyahu ya yi iƙirarin cewa gwamnatin da ke kai a yanzu "ba ta kyautatawa mutane", kuma "kashi 80 na mutane" na son a ƙawar da ita.

  5. Netanyahu ya ce suna aiki tare da Trump

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce "suna aiki" tare da shugaban Amurka Donald Trump, inda ya kuma yaba masa.

    Ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da gidan talabijin na Fox da ke Amurka.

    Trump dai ya ce babu hannun Amurka a rikicin Isra'ila da Iran.

    Lokacin da aka tambaye shi kan ya nemi taimakon Amurka - don samun makamai da za su wargaza shingaye na ƙasa - Netanyahu ya ce: "Ba zan bayyana abin da muka tattauna da shugaban ƙasar ba."

    "Sai dai duk matakin da ya ɗauka, matakinsa ne," in ji Netanyahu.

    Ya kuma ce Isra'ila ta riga da ta lalata ƙarfin nukiiyar Iran, ciki har da kai hari kan babbar tashar nukiliya a Isfahan.

  6. Cuta al'aurar mata da ta daɗe tana rikitar da likitoci

    "Na yi tunanin dukkan mata na fuskantar ƙaiƙayi," in ji Clare Baumhauer.

    Wata mata mai shekaru 52 daga Kent, Burtaniya ta ce tana ƴar kimanin shekara biyar lokacin da ta fara jin ƙaiƙayi a bakin gabanta.

    "Yana yi min ƙaiƙayi a kowane lokaci, yana zafi, ina samun kumburi da tsatstsagewa mai fitar da jini, sannan kuma idan na je tsuguno wurin na matuƙar zafi," kamar yadda ta ƙara bayani cewa zama ko tafiya na yi mata wuya.

    Ta shafe shekaru da dama tana ganin likitoci waɗanda suka shaida mata cewa tana da ƙwayar cutar da ta kumbura mata mafitsara amma kuma dukkannin magungunan da aka ba ta babu wanda ya yi aiki a ciki.

  7. Ƙasashen duniya na mayar da martani kan rikicin Isra'ila da Iran

    Ga wasu martani daga faɗin duniya kan rikicin Isra'ila da Iran da ke ci gaba da bazuwa.

    Firaministan Iraqi, Mohammed Shiaa al-Sudani, ya faɗa wa jakadan Tarayyar Turai a Baghdad cewa hare-haren Isra'ila kan Iran "barazanar tsaro ce kai-tsaye da kuma ɗorewar Iraqi da yankin", kuma hakan zai kawo katsalanda ga tattaunawar diflomasiyya.

    Ministan harkokin wajen Faransa, Jean-Noel Barrot, ya ce shirin nukiliyar Iran na yin "barazana ga ɗorewar" tsaron Isra'ila da kuma Turai.

    Shugaban gwamnatin Jamus, Friedrich Merz, ya ce Tehran ta dakatar da "far wa fararen hula a Isra'ila cikin gaggawa". Ya ƙara da cewa Jamus na yin shiri kan yiwuwar cewa ko Iran za ta kai wa wuraren Isra'ila ko na Yahudawa hari a Jamus.

    Ministan harkokin wajen Turkiyya, Hakan Fidan, ya faɗa wa takwaransa na Rasha ta wayar tarho cewa tattaunawar diflomasiyya ce kaɗai za ta iya "warware" rikicin, a cewar wata majiya yayin tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Reuters.

  8. Shugaban Iran ya buƙaci Iraqi ta hana Isra'ila amfani da sararin samaniyarta

    Shugaban Iran ya yi kira ga Iraqi da ta hana Isra'ila amfani da sararin samaniyarsu wajen kai mata hare-hare, a cewar wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar.

    Kasar Iraqi dai na tsakanin Isra'ila da Iran.

    Yayin wata tattaunawa ta wayar tarho, shugaba Masoud Pezeshkian ya buƙaci takwararsu Iraqi da su "ƙara tsaurara tsaro" ... don ganin ba a yi amfani da yankinta ba wajen aikata abu mara kyau kan al'ummar Iran", a cewar sanarwar.

  9. Ambaliya ta kashe mutum 19 a Kongo

    Ambaliyar ruwa ta kashe aƙalla mutum 19 a Kinshasa, babban birnin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kongo.

    Mamakon ruwan sama da ya sauka a cikin 'yan kwanakin da suka gabata ya haifar da zabtarewar ƙasa da ambaliyar ruwa a sassa da dama na birnin Kinshasa.

    Wani jami'in gwamnatin ƙasar ya ce ruwa ya mamaye sama da gidaje 500 a wata unguwa.

    Ambaliya dai ta daɗe tana addabar birnin Kinshasa, sakamakon kusancinsa da gaɓar kogin Kongo.

  10. Shugaban Iran ya sha alwashin 'martani mai tsanani' kan Isra'ila

    Kafin waɗannan sabbin hare-hare da Iran ta kai wa Isra'ila, shugaban ƙasar Massoud Pezeshkian ya yi gargaɗin cewa idan Isra'ila suka ci gaba kai musu hari, to za ta ga "martani mai zafi kuma mai tsanani".

    A tattaunawa ta wayar tarho da firaministan Iraqi, ya ce sauran ƙasashe a yankin su ma za su iya shiga cikin barazana idan hare-haren suka ci gaba, kuma ya buƙaci ƙasashen Musulmi su tsaya kan "manufarsu".

    Ya ce ba Iran ce ta soma faɗan ba, amma ta jajirce wajen mayar da "martanin" da ya kamata.

  11. Isra'ila da Iran za su 'cimma yarjejeniya' - Trump

    "Ya kamata Iran da Isra'ila su cimma yarjejeniya, kuma za a iya hakan," a cewar shugaban Amurka Donald Trump, inda ya ƙara da cewa shi zai iya tabbatar da hakan.

    A wani sako da ya wallafa a kafofin sada zumunta, Trump ya yi nuni kan rikice-rikice da aka samu baya-bayan nan a faɗin duniya, wanda ya ce ya taimaka wajen yayyafa musu ruwa.

    Amurka dai na taimakawa a tattaunawar tsagaita wuta tsakanin Uraine da Rasha, da kuma Isra'ila da Hamas.

    Sai dai duka ɓangarorin na ci gaba da gwabza faɗa.

    "Za mu iya samar da zaman lafiya nan ba da jimawa ba, tsakanin Isra'ila da Iran", in ji Trump.

    "Ana yin zama da kuma tattaunawa. Ina yin hakan sosai, kuma ba a taɓa jinjina min kan haka ba, amma ba komai, mutane suna sane da haka.

    "A dawo da martabar Gabas Ta Tsakiya".

  12. Labarai da dumi-dumi, Iran ta harba makaman linzami cikin Isra'ila - IDF

    Dakarun tsaron Isra'ila sun ce an ji ƙarar jiniyar anƙararwa a faɗin yankunan ƙasar, bayan da suka gano cewa Iran ta harba makaman linzami zuwa cikin ƙasar.

    Sojojin saman ƙasar na "aikin kakkaɓe makaman a wajen da ya kamata don kawar da barazanarsu," in ji sojojin.

    Sun ƙara da cewa mutane su ci gaba da bin umarni daga hukumomi.

  13. Me ya sa al'ummar Katsina suka yi sulhu da Ado Aleru?

    Wasu al'ummar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya sun yi sulhu da wasu shugabannin ƴanbindiga da suka addabe su.

    Al'ummar garin Bicci da ke yankin ƙaramar hukumar Danmusa sun zauna tare da Ado Aleru da sauran wasu shugabannin 'yanbindigan akalla goma, kamar yadda kwamishinan tsaro da harakokin cikin gida na jihar Katsina Dakta Nasiru Mu'azu ya shaida wa BBC.

    "An zauna da Ado Aleru da Kamilu Buzaru da Dogo Nahali da Wada Jargaba da Dahiru Buzu haka ma da Nagoggo," in ji shi.

  14. Iran za ta ɗanɗana kuɗarta, in ji Netanyahu

    Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce Iran za ta "ɗanɗana kuɗarta" kan kashe fararen hula a Isra'ila.

    Da yake jawabi a wani wurin da harin makami mai linzami ya afka wa a birnin Bat Yam, Netanyahu ya kira lamarin da cewa "dagan-gan Iran ta kashe fararen hula, mata da kuma yara", kuma Iran na "barazana ga ɗorewar" Isra'ila.

    Ya ƙara da cewa "yana jajantawa" wadanda aka kashe, kuma "muna miƙa ta'aziyya ga iyalansu", yayin da ya buƙaci mutane da su bi matakan kariya daga wajen jami'ai.

  15. Mutum bakwai sun mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a Indiya

    Mutum bakwai sun mutu bayan hatsarin da jirgin sama mai saukar ungulu ya yi a jihar Uttarakhand da ke arewacin ƙasar Indiya, a cewar jami'ai.

    Kafofin yaɗa labaran ƙasar sun ce jirgin ya taso ne daga babban birnin jihar zuwa wani shahararren wurin ibada da ke cikin tsaunukan Himalayas.

    Matukin jirgin da wani ɗan shekara biyu na cikin waɗanda suka mutu, a cewar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Indiya.

    Ana ci gaba gudanar da ayyukan ceto yayin da ake bayyana rashin kyawun yanayi a matsayin abin da ya janyo hatsarin.

    A watan Mayu, mutane shida ne suka mutu a wani lamari makamancin wannan a jihar ta Uttarakhand.

  16. Labarai da dumi-dumi, Birtaniya ta gargaɗi ƴan ƙasar kan balaguro zuwa Isra'ila

    Ma'aikatar harkokin wajen Birtaniya ta gargaɗi ƴan ƙasar kan yin balaguro zuwa Isra'ila, a daidai lokacin da suke yaƙi da Iran.

    Ma'aikatar ta ce ta yi gargaɗin saboda barazanar bazuwar rikicin.

    Ta buƙaci waɗanda suka riga suka kasance cikin Isra'ila ko yankunan da aka yi wa ƙawanya da su bi shawarwarin hukumomi.

  17. Isra'ila ta far wa wurare 80 a Tehran cikin dare - IDF

    Sojojin Isra'ila sun ce gomman jiragen yaƙinta sun far wa wurare aƙalla 80 a Tehran cikin dare, a daidai lokacin da ake shiga kwana na uku a yaƙi da Iran.

    Wuraren sun haɗa da shelkwatar ma'aikatar tsaron Iran, da sashen binciken sojoji da kuma ƙarin wurare da gwamnatin Iran ta ɓoye kayayyakin nukiliya.

    Sauran wurare sun haɗa da na man fetur, waɗanda soji ke amfani da su da kuma ayyukan nukiliya, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters - kamar yadda ya ruwaito wani jami'i na faɗa.

    IDF ta ce ta far wa wurare sama da 170 da kuma shingayen soji 720 a cikin ƙasa da kwanaki uku a wani samame da ta saka wa suna da Rising Lion.

  18. Dakarun Isra'ila sun gargaɗi ƴan Iran su tashi kusa da shingayen soji

    Dakarun tsaron Isra'ila Isara'ila sun fitar sakon gargaɗi ga ƴan Iran, inda suka buƙaci mutane da su tashi daga yankunan da ke da cibiyoyin soji.

    A wani sako a shafin X, IDF ta ce: "Dukkan mutane ... da ke zaune kusa da wuraren sojoji da kuma na ƙera makamai su tashi nan take, kuma kada su koma har sai abin da hali ya yi.

    "Zamanku a waɗannan wurare babban barazana ce gare ku."

  19. Saudiyya ta ɗauki nauyin kula da alhazan Iran har sai sun samu damar komawa gida

    Ma'aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta fara shirye-shiryen ganin an bai wa alhazan Iran da ke Makkah da Madinah dukkan kulawa da ta kamata.

    Wannan ya biyo umarni da gwamnatin ƙasar ta bayar, na ganin an kula da alhazan ƙasar har sai sun samu damar komawa gida.

    Ma'aikatar ta ce jami'anta na aikin duba irin kulawa da ake bai wa mahajjatan Iran 76,000, don tabbatar da cewa babu abin da ya same su yayin da suke Saudiyya.

    Haka kuma, ma'aikatar tare da haɗin gwiwar takwararta ta Iran, sun tsara yadda za a yi shirin mayar da alhazan gida.

    "Muna son a gudanar da shirin mayar da alhazan na Iran cikin tsanaki ba tare da wata matsala ba," in ji ma'aikatar ta Aikin Hajji da Umara.

    Alhazan za su bi ta filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz da ke Jeddah da kuma na Mohammed bin Abdulaziz a Madinah, sannan su zarce na birnin Arar, har su kai gida.

    An fara aikin jigilar alhazan ne tun ranar Juma'a, inda jami'ai ke ƙoƙari sau da ƙafa wajen ganin an mayar da kowa lami lafiya.