Mu zama lafiya
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.
Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke wakana a Najeriya da sassan duniya kai tsaye, na Litinin, 03/03/2025
Isiyaku Muhammed da Umar Mikail
Ƙarshen rahotonnin kenan a wannan shafi.
Mu haɗu da ku gobe domin samun wasu sababbi daga sassan duniya.
Umar Mikail ke cewa mu zama lafiya.

Asalin hoton, EPA
Ministan harkokin cikin gida na jiha a Jamus, Thomas Strobl, ya ce mutumin da ya kashe mutane da mota a yau Litinin ya yi amfani da motar ne "a matsayin makami".
Da yake magana da manema labarai tare da ministar harkokin gida ta tarayya, Nancy Faeser, Stroble ya ce: "Lamarin ɗaya ne daga cikin laifuka a baya-bayan nan inda aka yi amfani da mota a matsayin makami."
A cewar kamfanin labarai na Reuters, Strobl ya ce babu wata alama zuwa yanzu kan ko mutumin na da "aƙidar tsattsauran ra'ayin addini".
"Ƙila ya aikata hakan ne kawai saboda son zuciyarsa. Amma kuma dai lamari ne da ake ci gaba bincike a kai," in ji Strobl.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, @HMMohammedIdris
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ba da umarnin kammala aikin babbar hanyar Abuja zuwa Kano cikin wata 12.
Mai magana da yawun fadar shugaban Najeriya, Sunday Dare, ya ce a yau Litinin shugaban ya amince bayar da umarnin.
"Shugaba Tinubu ya amince da kasafin kammala wuraren da ba a gama ba a kan titin Abuja-Kaduna, da na Kaduna-Zaria cikin wata 12," kamar yadda ya wallafa a shafinsa na dandalin X.
Ya ƙara da cewa "wannan titi ne mai muhimmanci ne a kodayaushe".
A watan Janairu gwamnatin Bola Tinubu ta sanar da bai wa wani sabon kamfani ƙarashen aikin titin bayan ta ƙwace kwangilarsa daga hannun Julius Berger.

Asalin hoton, EPA
Hukumomi a ƙasar Jamus sun ce mutum biyu sun mutu bayan wani mutum ya auka cikin mutane da mota a birnin Mannheim na kudu maso yammacin ƙasar.
Wasu da dama kuma sun ji rauni, har da masu munanan raunuka.
Hukumomi a jihar Baden-Württemberg sun ce 'yansanda sun kama wani ɗan Jamus mai shekara 40.
Sai dai ba su yi ƙarin bayani ba kan ko lamarin hari ne ko kuma hatsari.
Motar ta uka kan mutanen ne lokacin da suka taru domin yin bikin kan titi na shekara-shekara a wasu sassan Jamus.

Asalin hoton, @Jossy_Dannyking
Rundunar 'yansandan Najeriya a Abuja babban birnin Najeriya ta ce jami'inta da aka bayar da rahotonnin cewa an sace ya koma gida tuni.
Da take tabbatar wa da BBC ta wayar tarho, kakakin rundunar Josephine Addeh ta ce da ma ba wani mummunan abu ne ya faru da Sufuritanda Modestus Ojiebe ba.
"Motarsa ce ta samu matsala kawai a kan hanya, kuma gaba ɗaya abin da ya faru bai fi 'yan awanni ba ya kuɓuta kuma ya koma gida," in ji ta.
Tun da farko was kafofin yaɗa labarai sun ruwaito cewa motar ɗansandan ce ta samu matsala a kan babban titin Abuja zuwa Kaduna, inda wasu da ake zargin masu garkuwa ne suka yi awon gaba da shi.

Asalin hoton, Lagos State Assembly
Majalisar Dokokin Jihar Legas da ke kudancin Najeriya ta sake zaɓar Mudashiru Obasa a matsayin kakakinta bayan Mojisola Meranda ta yi murabus.
Matakin na zuwa ne bayan makonnin da aka shafe ana rikici kan shugabancin majalisar, wanda aka fara bayan tsige Obasa tare da maye gurbinsa da Meranda.
Bayan murabus ɗin nata, nan take 'yanmajalisar suka zaɓe ta a matsayin mataimakiyar Obasa, a wani yanayi da ba a saba gani ba a siyasar Najeriya.
'Yanmajalisar sun yabi salon mulkinta da kuma jajircewarta a matsayinmace ta farko kakakin majalisa.
Rahotonni sun ce ta sauka daga muƙamin ne bayan wata ganawa da manyan 'yan jam'iyyar APC mai mulkin jihar game da yadda za a shawo kan rikicin.

Asalin hoton, Getty Images
Rahotanni na cewa an yi garkuwa da wani ɗansanda mai suna Modestus Ojiebe wanda ke aiki da rundunar ƴansandan jihar Kwara, a babban titin Kubwa da ke cikin birnin.
Shafin masanin harkokin ƴanbindinga na Zagazola Makama ya ce majiyoyin tsaro sun faɗa masa cewa lamarin ya auku ne a kusa da unguwar Dei-Dei gab da barikin ƴansanda da ke Abuja.
"Lamarin ya auku a daidai lokacin da ya tsaya domin ya duba motarsa da ta lalace, sai wasu mutane suka zo a mota, suka ƙwace masa wayoyi da na matarsa. Da suka gane ɗansanda ne sai suka saka shi a motar suka tafi da shi, suka bar matar da motar."
Sai dai an ce ƴansanda sun baza jami'ansu, domin suke binciken masu wucewa da motoci da zimmar ceto abokin aikin nasu.
Sai dai an yi yunƙurin jin ta bakin kakakin rundunar ƴansandan Abuja, Josephine Adeh, amma haƙar ba ta cimma ruwa ba.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce kusan mutum 400 ne suka rasu a sanadiyar ambaliyar ruwa da ta dabaibaye yankunan ƙasar a shekarar da ta gabata.
Haka rahoton hukumomin ya nuna cewa sama da gidaje 150,000 ne ambaliyar da lalata a ƙasar.
Masana sun ce sauyin yanayi na taimakawa wajen ƙara ta'azzara matsalolin muhalli irin su fari da faɗaɗa ɓarnar da mamakon ruwan sama ke jawowa.
A wasu yankunan Afirka, fari na kan gaba wajen ta'azzara ambaliya saboda ƙasa na bushewa ta kasa shanye ruwan sama.

Asalin hoton, EPA
Shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelensky ya ce idan har ana so ya shiga tattaunawa da Rasha kan batun tsagaita wuta, dole ta daina yi wa ƙasarsa luguden wuta.
"Ukraine na yaƙi ne domin kare kanta, sannan muna yunƙurin dawo da zaman lafiya a ƙasar. Muna so yaƙin nan ya ƙare, amma ita Rasha ba ta so a kawo ƙarshensa, domin har yanzu tana cigaba da mana luguden wuta.
"Daga makon jiya zuwa yanzu, aƙalla hare-haren jirage marasa matuƙa guda 1,050 Rasha ta yi, sannan ta jefa mana bama-bamai kusan 1,300, da makamai masu linzami sama da 20 duk domin lalata biranemu da kashe mutanenmu."
"Idan ana so mu fara tattaunawa, to a daina yi wa mutanenmu luguden wuta," in ji shi, sannan ya ƙara da cewa "Idan ana so a dakatar da Rasha, dole ƙasashen duniya su haɗa ƙarfi da ƙarfe," in ji Zelensky.
Rundunar ƴansandan Ukraine ta ce wasu mutane sun raunata a hare-haren Rasha a yankin Donetsk, sannan an kashe kusan mutum biyar a kudancin Kherson, sannan aka jikkata 13 ciki har da ƴansanda da suka je ɗauko gawar wani dattijo.

Asalin hoton, Getty Images
Darajar wasu kuɗaɗen kirifto sun tashi bayan shugaba Donald Trump ya sanar da cewa za a kafa wani rumbun adana kuɗaɗen kirifto na ƙasar Amurka.
Ya ambaci kuɗin kirifto na Bitcoin da Ethereum da XRP, da ADA SOL a cikin wani jawabi da ya yi a kafofin sadarwa, inda ya ƙara da cewa Amurka ce za ta zama babbar cibiyar hada-hadar kirifto ta duniya.
Jim kaɗan da yin jawabin ne darajar kuɗaɗen da ya ambata suka tashi, inda Bitcoin da Etherium suka ƙara daraja da kusan kashi 10 kafin suka ja baya, sannan sauran kuɗaɗen ma suka tashi.
A baya dai Trump da matarsa Melania sun fitar da kuɗinsu na kirifto na matakin meme.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar kula da filayen jiragen sama na Najeriya ta sanar da rufe ɗaya daga cikin titunan tashin jirgin sama na Murtanal Muhammed da ke Legas domin yin gyara.
Wata sanarwa da hukumar ta fitar ɗauke da sa hannun daraktar hulda da jama'a ta hukumar, Mrs Obiageli Orah, ta ce za a rufe titin tashin jirgi mai lamba 18R/36L ne daga ƙarfe uku na asubahin ranar 3 ga watan Maris, zuwa ƙarfe 11:59 na daren ranar Talata 4 ga watan Maris, 2025.
Sanarwar ta ce za a rufe titin ne domin gyara kwaltan wani ɓangare na hanyar da jirage ke bi kafin hawan babban titin da suke tashi.
Sai dai sanarwar ta ƙara da cewa domin ganin ba a kawo cikas ga sufurin jirage ba, an karkata sauka da tashin jiragen zuwa wani titin, mai lamba 18L/36R.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Asalin hoton, NYSC Facebook
Hukumar NYSC ta ce ta kusa fara biyan masu yi wa ƙasa hidima alawus ɗin naira 77,000.
Hukumar ta bayyana haka ne a matsayin martani kan rashin fara biyan sabon alawus ɗin bayan an sanar da ƙari daga naira 33,000 da ake biya biyo bayan ƙara mafi ƙanƙantar albashi.
A watan Yulin shekarar da ta gabata ne gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin fara biyan sabon alawus ɗin, amma har yanzu ba a fara biya ba, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito daga masu bautar ƙasar.
A watan Janairu, darakta-janar na NYSC, Birgediya-janar Yushau Ahmed ya sanar da cewa daga watan Fabrairu za a fara biyan sabon alawus ɗin, amma kuma ba a biya ba a watan na Fabrairu da ya gabata.
Daraktan riƙo na hulɗa da jama'a na hukumar, Caroline Embu, ta ce suna jiran kuɗi ne da umarni kafin fara biyan sabon alawus ɗin, duk da cewa ba ta bayyana zuwa yaushe ba.
Sai dai ta ce duk shirye-shiryen da suka kamata a yi, duk an yi, "jiran lokaci kawai ake yi."

Asalin hoton, ORTN
Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta bayyana aniyarta ta yin garambawul ga dokar tsarin amfani da shafukan sada zumunta irin su Whatsapp da Facebook a ƙasar.
Ministan sadarwa na ƙasar ne ya bayyana hakan inda ya ce duk wani zaure na Whattsapp ko Facebook da ya ƙunshi adadin mutanen da suka wuce 50 zuwa 100 ya zamo tamkar ƙungiyar da ke buƙatar yin rajista a wajen hukuma don ci gaba da aikinsa.
Ministan ya ce zaurukan whattsap da Facebook na zama hanyoyin kasuwanci da kuma yaƙar gwamnatoci don haka suka fara nazari da wasu ƙasashen Afirka domin sake duba dokar aikin shafukan sada zumunta a ƙasashen.

Asalin hoton, OTHER
Ɗaliban jami'a na gwamnatin tarayya da ke Dutsinma na jihar Katsina huɗu ne ƴanbindiga suka sace a wata unguwar da ake kira da Paris Quarters da ke jihar, wadda take arewa maso yammacin ƙasar.
Mazaunin yankin ne suka tabbatar wa jaridar Daily Trust aukuwar lamarin, inda suka ce maharan sun isa unguwar ne da misalin ƙarfe 2:20 na daren Asabar, inda suka yi awon gaba da ɗaliban guda huɗu zuwa inda ba a tantance ba.
Mutanen yankin sun ce jami'an tsaron sun zo wajen bayan ƴanbindigar sun riga sun tafi da ɗaliban da suka sace.

Asalin hoton, Getty Images
Ma'aikatan agaji a yankin Darfur na ƙasar Sudan sun ce fararen hula shida ne suka mutu a lokacin da Dakarun RSF suka yi luguden wuta kan wani sansanin ƴan gudun hijira da wata kasuwa.
Wakilin BBC ya ce bama-baman RSF sun faɗa kan sansanin Abu Shouk da kuma kasuwar Naivasha da ke cunkushe da jama'a a garin El Fasher.
An dai daɗe da ayyana tsananin yunwa a Abu Shouk da wasu sansanoni biyu a yankin.
Sama da mutum miliyan goma sha biyu ne suka tsere daga gidajensu tun bayan ɓarkewar yaƙin Sudan kusan shekara biyu da suka gabata.

Asalin hoton, NLC
Ƙungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C.
Shafin intanet na tashar Channels ya ruwaito daga sanarwa da NLC ɗin ta fitar a ranar Lahadi bayan wani taro da ta yi a jihar Adamawa.
"NLC ba ta amince da yunƙurin hukumar lantarki ta Najeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarki kwastomomi daga layin B da A da sunan haɓaka samun lantarki, alhali kuma yunƙuri ne kawai na ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba," in ji sanarwar.
"A fili yake dai yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci ta hanyar ƙara kuɗin haraji da lantarki da sauransu a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya tsaya cak."
Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba za ta lamunci ƙarin kuɗin wutar ba, inda ta yi barazanar shirya zanga-zanga idan har aka ƙara kuɗin lantarkin.

Asalin hoton, ERICK-CHRISTIAN AHOUNOU
Ƙungiyar ECOWAS, ta ce tawagar da ta aika ƙasar Guinea-Bissau domin ta taimaka wajen warware taƙaddamar zaɓe ta bar ƙasar bayan da shugaban ƙasar ya yi barazanar korar tawagar.
Ƴan jam'iyyun hammaya na na siyasar ƙasar dai sun dage cewa ya kamata wa'adin Shugaba Umaro Sissoco Embalo ya ƙare a makon da ya gabata.
Sai dai ya dage kai da fata cewa ba za a yi zaɓe ba sai watan Nuwamban da ke tafe.

Asalin hoton, Godswill Akpabio
Ƙungiyar dattawan arewacin Najeriya, wato Arewa Consultative Forum ko kuma ACF a taƙaice ta nuna damuwarta kan zargin cin zarafi da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
A wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi wanda kakakin ƙungiyar, Muhammad-Baba ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce akwai buƙatar a gudanar da bincike mai kyau domin tantance sahihancin zargin, kamar yadda tashar Channels a shafinta na intanet.
"A yanzu dai yadda abubuwa suke shi ne zargin nan zai iya ɓata sunan Najeriya a idon duniya," in ji ƙungiyar, wadda ta nuna damuwa kan yadda a cewarta har zuwa yanzu, sanatocin arewa ne kaɗai suka fuskanci takunkumi kamar dakatarwa a majalisar ta 10.
"Wannan ya sa ACF ke fargabar ko dai abin ɓoye ne ya fara fitowa fili na yaƙi da yankin arewa. Wannan ya sa muke kira da a kawo ƙarshen wannan lamarin."
Ƙungiyar ta yi kira da sanatocin arewa su goyi bayan Natasha, sannan ta buƙaci a gudanar da bincike.

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Hisba ta jihar Kano ta sanar da kama wasu matasa waɗanda ba sa azumi, da waɗanda suka yi aski banza.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito mataimakin kwamanda-janar na hukumar, Mujahiddeen Abubakar, inda ya ce sun kama matasan ne a lokacin da suke sintiri a sassa daban-daban na Kano.
Haka kuma ya ce sun kama wasu matasa guda 60 da suka yi "askin banza" waɗanda a cewarsa ya saɓa da addinin musulunci da al'adun mutanen yankin.
A wani ɓangaren kuma, ya ce hukumar ta kama wani mai Adaidaita wanda suke zargi da haɗa fasinjoji maza da mata.