Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 12/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Badamasi Abdulƙadir Muktar

  1. Habasha da Somalia sun cimma matsaya kan taƙaddamar Somaliland

    Ethiopia/Somalia

    Asalin hoton, Reuters

    Ƙasashen Habasha da Somaliya sun cimma matsaya don kawo ƙarshen takaddamar da ke tsakaninsu bayan wata tattaunawa da suka yi a Ankara babban birnin kasar Turkiyya.

    Shugaban Somaliya, Hassan Sheikh Mohamud ya ce ƙasarsa a shirye take ta yi aiki tare da Habasha.

    Ya ce ''Muna da damar haɗa hannu da juna don ci gaba tare da kuma biyan buƙatunmu''.

    Somaliya za ta ba da gudummawa wurin cimma hakan kuma a shirye muke mu yi aiki tare da shugabanni da kuma al'ummar Habasha.

    Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya yi maraba da yarjejeniyar mai cike da tarihi.

    Firaiministan Habasha, Abiy Ahmed da shugaban Somalia, Hassan Sheikh Mohamud, sun amince za su mutumta ƴancin kowanne ɓangare.

    Ƙasashen biyu maƙwabtan juna sun shiga taƙaddama ne tun a watan Janairu, lokacin da Habasha ta ƙulla yarjejeniyar alaƙa da Somaliland ta ruwa, yankin da Somalia ke yi wa kallon wani ɓangare na ƙasar ta.

  2. Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Mai Numfashi

    Bayanan bidiyo, Daga Bakin Mai Ita tare da Khadija Mai Numfashi

    Filin Daga Bakin Mai Ita na wannan makon ya karɓi baƙuncin Khadija Kabir Ahmad, wadda aka fi sani Khadija Mai Numfashi.

    Tauraruwar finafinai ce kuma haifaffiyar garin Kwanar Ɗangora ce da ke ƙaramar hukuma Ƙiru ta jihar Kano.

    Fim ɗinta na farko shi ne Ƙaddarata. Daga baya ta fito a shahararrun finafinai kamar Ɗan Gwamna, da kuma Bazato.

    An taɓa dakatar da ita daga shiga harkokin finafinai a 2023 sakamakon rawar da ta yi a Jamhuriyar Nijar, sai dai ta ce ta ɗauki alhakin abin da ya faru kuma komai ya wuce.

  3. Shugaban Koriya ta Kudu ya sha alwashin jajircewa kan dokar soji

    Yoon Suk Yeol

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban Koriya ta Kudu Yoon Suk Yeol yana ya ci gaba da kare matakin da ya ɗauka na kafa dokar soji a ƙasar a makon da ya gabata, yayin da ƴan majalisar dokoki na jami'iyyar adawa ke ƙoƙarin samun goyon bayan yunƙurin tsige shi a karo na biyu.

    Kafin jawabin Mista Yoon Shugaban jam'iyyarsa, Han Dong Hoon, ya bayyana a gidan talabijin yana mai cewa ta tabbata shugaban ba zai yi murabus ba, ya kuma yi kira ga ƴan jam’iyyar da su kada kuri’ar tsige shi daga mukaminsa ranar Asabar mai zuwa.

    A wani jawabi da ya yi ta talabijin a yau Alhamis, shugaba Yoon ya ce ya yunƙurin nasa matakin ne na kare dimokuraɗiyyar ƙasar daga durƙushewa.

    Yoon ya ce ba zai yi murabus ba, duk da yunƙurin tsige shi da majalisar dokoki ta ke yi karo na biyu a ranar Asabar.

    "Ina kan matsaya ta, ko an tsige ni ko ana bincike na, zan jajirce kan wannan yunƙuri har zuwa yadda hali ya yi''.

  4. Gwamnonin Najeriya sun yi taro a 'kan dokar haraji'

    NGF

    Asalin hoton, NGF

    Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta yi wani taro a cikin dare a hedikwatarta da ke birnin Abuja, inda rahotanni ke cewa sun tattauna abubuwa da dama ciki har da batun ƙudirin dokar haraji da ta janyo cece-ku-ce a ƙasar.

    Babu dai bayani daga gwamnonin a kan abin da taron nasu ya cimma wa, amma rahotanni daga jaridun ƙasar sun ce batun ƙudirin dokar harajin ne jigo a zaman gwamnonin na jiya Laraba da daddare.

    Gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki ne suka fi yawa a taron, inda aƙalla 15 suka halarta, sai gwamnoni biyu daga jam'iyyar Labour da kuma na APGA ɗaya.

    Ƙudirin dokar harajin wanda shugaban Najeriya Bola Tinubu ya gabatar wa majalisar dokokin ƙasar ya janyo suka da ƙorafi daga masu ruwa da tsaki, ciki har da gwamnonin ƙasar a ƙarƙashin majalisar ƙoli ta tattalin arziki, da gwamnoni da ƴan majalisa daga yankin arewa da ma ƙungiyoyi da dama.

    Gwamnonin Arewa 19 kuma sun bayyana rashin goyon bayan su ga wasu sassa na ƙudirin, tare da neman a gaggauta janye shi daga majalisar dokokin tarayya.

  5. Ɗana ya cancanci zama kwamishina - Oshiomhole

    Sanata Oshiomhole

    Asalin hoton, @OfficialAPCNg

    Sanata mai wakiltar mazaɓar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya ce ɗansa, Cyril, ya cancanta kuma yana da ƙwarewar da ta dace domin zama kwamishinan lafiya a jihar Edo.

    Sanata Oshiomhole, wanda tsohon gwamnan jihar ne yana tsokaci ne game da martanin da ya biyo bayan naɗin da gwamnan Edo Monday Okphebolo ya yi wa Cyril Oshiomhole a matsayin kwamishinan lafiya a cikin watan Nuwamba.

    Naɗin nasa dai ya janyo ƙorafi daga jama'a, masu ganin cewa kamar gwamnan ya saka wa Sanata Oshiomhole ne saboda gudunmuwarsa a zaɓen gwamnan.

    Amma a wata hira da gidan talabijin na Channels a Najeriya, Sanata Oshiomhole ya ce tun da daɗewa ɗan nasa ya cancanta riƙe muƙami a jihar, inda ya nemi takarar majalisar wakilai, amma mahaifin nasa ya hana shi saboda a lokacin shi ne gwamna.

    Ya yi bayanin cewa a yanzu lokaci ya yi da zai bari ɗan nasa ya shiga a dama da shi domin bayar da gudunmuwa wajen ciyar da jihar ta Edo gaba.

  6. Dakarun Isra’ila sun mamaye Bethlehem

    IDF

    Asalin hoton, Getty Images

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce dakarunta sun kewaye garin Bethlehem da ke gabar yamma da kogin Jordan da ta mamaye a yayin da suke neman wani ɗan bindiga da ya budewa wata motar bas wuta, inda ya kashe wani matashi dan shekara goma sha biyu.

    Sun ce akalla mutane hudu ne suka jikkata a harin, wanda aka kai a lokacin da motar ke kan hanyar zuwa birnin Kudus.

    A Gaza, likitoci sun ce Isra'ila ta kai wani hari ta sama a kudancin birnin Rafah, Kan wata tawagar falasdinawa da ke kokarin kare motocin agaji, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutane akalla 8 tare da jikkata wasu da dama.

    Isra'ila dai ba ta ce komai kan harin ba.

  7. MDD ta kaɗa ƙuri’ar tsagaita wuta a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Zauren Majalisar Dinkin Duniya ta kaɗa ƙuri'a da gagarumin rinjaye na neman tsagaita wuta ba tare da sharaɗi ba Gaza tare kuma da sakin dukkan mutanen da aka yi garkuwa da su cikin gaggawa.

    Ƙasashe 158 ne suka kaɗa ƙuri'ar amincewa yayin da Amurka da Isra'ila da wasu ƙasashe bakwai suka ƙi amincewa da ƙudurin.

    Da yake jawabi gabanin kaɗa kuri’ar, jakadan Falasdinawa a Majalisar Dinkin Duniya, Riyad Mansour, ya roƙi Majalisar da ta buƙaci a kawo ƙarshen faɗan da ake yi a Gaza.

    Ya yi bayanin cewa yana da muhimmanci sosai a dakatar da zubar da jini domin dawo da rayuwa a Gaza ta yadda za ta sake zama cibiyar Falasɗinawa

  8. Sabuwar gwamnatin Syria ta ce za ta rufe gidajen yarin Assad

    Syria

    Asalin hoton, Reuters

    Sabbin hukumomin mulki a Syria sun ce suna shirin rufe gidajen yarin hamɓararren shugaban ƙasar Bashar al-Assad tare da rusa rundunar jami'an tsaronsa.

    Dubbban mutane ne ake tunanin gwamnatin Assad ke tsare da su a gidajen yarin na Syria, ciki har da katafaren ginin nan na Sednaya, inda ake yawan samun rahotannin azabtarwa.

    Tun bayan da 'yantawayen ƙasar suka kifar da gwamnatin Assad suka yi ta buɗe gidajen yarin domin sakin fursunoni.

  9. Assalam alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Yau ma kamar kullum mun fito domin kawo muku labaran halin da duniya ke ciki, musamman Najeriya da makwabtanta.

    Kuna iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.