Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/04/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Kakangi, Ahmad Bawage da Umar Mikail

  1. Saudiyya za ta biya wa Syria bashin da Bankin Duniya ke bin ta

    Syria

    Asalin hoton, Telegram

    Rahotanni na cewa Saudiyya na shirin biyan bashin da Bankin Duniya ke bin ƙasar Syria, a wani matakin farko na taimakon sabuwar gwamnatin Syria tsayawa da kafarta.

    Bankin duniya na bin Syria bashin dala miliyan 50, biyan bashin zai bai wa ƙasar damar samun tallafin don sake gina ƙasar, ciki har da gyara wutar lantarkin da yaƙi ya ɗaiɗai ta.

    A watan Janairun bana, Amurka ta ɗauke wa Syria takunkumin watanni shida - domin ba da damar kai agaji ƙasar, sai dai kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa wannan ba lallai ya yi tasiri ba.

  2. Yadda tsutsa ta lalata amfanin tumatir na miliyoyin naira a Najeriya

    Tumatir

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƙungiyar masu noman tumatir a Najeriya ta bayyana fargabar samun ƙaranci da tsadar tumatir, saboda barnar da wata tsusa ta yiwa dumbin gonakin da ake noma shi a sassan kasar.

    Dubban manoma ne al'amarin ya shafa wadanda suka zuba kudinsu wajen yin noman tumatir din amma hatsabibiyar tsutsar ta mamaye shi, inda kungiyar ta ce tuni suka fara ganin tasirin ta'adin da tsusar ta yiwa gonaki.

    Kungiyar manoman tumatir ta kokawa cewa tun farkon watan Maris din shekarar nan suka fara ganin bullar fitinanniyar tsutsar timatir din da ake kira Tuta Absaluta, inda ta yiwa dumbin gonaki mummunar barna a wasu jihohin arewacin Najeriya.

  3. Dubban mutane sun tsere daga Darfur bayan harin RSF

    Darfur

    Asalin hoton, Reuters

    Dubun-Dubatar farar hula ne suka tsere daga sansanin 'yan gudun hijira mafi girma a Sudan, bayan 'yan tawayen RSF sun karɓe iko da sansanin na ZamZam da ke yankin Darfur.

    Ƙungiyar da ke kula ƙaura ta duniya ta ce aƙalla mutane dubu 400 ne suka tsere daga sansanin, yayin da ƙungiyar likitocin ƙasa da ƙasa ta MSF ta ce yawancin mutanen sun yi tafiyar kilomita 70 a kafa, domin isa garin Tawila, inda yunwa da kishin ruwa suka galabaitar da su.

    Altayyib Idris Baraka, jami'in gwamnatin Sudan a yankin Darfur ya ce an kai munanan hare-haren ne sansanin ZamZam, inda RSF suka kwashe kwanaki uku suna kai ruwan wuta.

    Dama dai mazauna sansanonin Zamzam da Abou Shouk na fama da ƙarancin abinci.

  4. Buɗewa

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Talata.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran sassan duniya.

    Ahmad Bawage ne zai jagoranci kawo labaran a wannan lokaci.