Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 15/01/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Alhamis, 15 ga watan Janairun 2026.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida, Haruna Kakangi da Ahmad Bawage

  1. Shugabar riƙon-ƙwaryar Venezuela ta tattauna da Trump kan alaƙar ƙasashen biyu

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugabar rikon-kwarya ta Venezuela Delcy Rodriguez, ta yi wata tattaunawa mai tsawo da armashi, ta waya da Shugaban Amurka, Donald Trump, inda suka tattauna kan alakar kasashensu biyu.

    Bayan tattaunawar ta waya, Trump, ya ce a yanzu an samu fahimtar juna sosai tsakanin Amurka da Venezuela - suna ɗasawa, har ma ya bayyana shugabar a matsayin mai ban mamaki.

    Wannan tattaunawar ita ce ganawa ta farko da aka sani tsakanin su tun bayan hamɓarar da tsohon shugaban ƙasar, Nicolás Maduro.

    Rodríguez ta karɓi ragamar mulkin Venezuela a matsayin shugabar rikon-kwarya ne bayan da Amurka ta kame tsohon shugaban ƙasar Maduro a farkon watan Janairu ta kai shi kasarta, ta gurfanar da shi gaban sharia kan zargin safarar miyagun kwayoyi lamarin da ya janyo sabon yanayin siyasa a Caracas.

  2. Iran ta ce ba ta da shirin kashe masu zanga-zanga

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya ce gwamnatin ƙasarsa ba ta da wani shiri na aiwatar da hukuncin kisa kan mutanen da aka kama bisa zargin shiga zanga-zanga.

    Araghchi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da kafar yaɗa labarai ta Fox News, inda ya kuma yi gargaɗi ga Shugaban Amurka, Donald Trump, da kada ya sake aikata abin da ya kira kuskuren da aka yi a bara, lokacin da Amurka ta kai hare-haren sama kan wasu muhimman tashoshin nukiliyar Iran a watan Yuni.

    Trump dai ya yi barazanar ɗaukar tsauraran matakai idan har Iran ta aiwatar da hukuncin kisa kan masu zanga-zanga. Sai dai daga baya ya ce an tabbatar masa cewa Iran ta dakatar da kisan masu zanga-zangar.

    Sai dai har yanzu tambayar har yanzu ita ce: ko Trump yana jan lokaci ne, ko kuwa yana ƙoƙarin shammatar Iran—kuma mene ne ainihin lissafinsa a wannan lokaci?

    A halin da ake ciki, a ranar Laraba, Amurka da Birtaniya sun janye wasu daga cikin sojojinsu daga wani muhimmin sansani a ƙasar Qatar, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a kan yiyuwar Amurka ta sake kai hari a yankin.

  3. 'Babu sauran kulawa da gwamnati ke bai wa iyalin Tafawa Balewa'

    ...

    Asalin hoton, Getty Images

    Yayin da ake cika shekara 60 da juyin mulkin soji na farko a Najeriya, BBC ta kai ziyara inda aka binne gawar mutum mafi girman muƙami da aka kashe a lokacin juyin mulkin.

    Abubakar Tafawa Ɓalewa shi ne Firaiministan Najeriya na wancan lokaci, kuma yana cikin waɗanda sojojin suka hallaka a shekarar 1966, baya ga Firimiyan jihar Arewa da na Yamma da kuma manyan sojoji da masu riƙe da muƙaman gwamnati.

    Shi ne juyin mulkin da ya kawo ƙarshen jamhuriya ta farko a Najeriya, wadda ta ƙunshi fitattun mutane da suka yi fafutikar samun ƴancin kan ƙasar.

    An binne marigayin ne a garin Bauchi da ke jiharsa ta asali a arewa maso gabashin Najeriya.

    Cikin iyalan Tafawa Ɓalewa da BBC ta zanta da su, akwa jikan marigayin, Abubakar (Billy) Tafawa Ɓalewa wanda ya nuna takaici kan halin da kabarin kakan nasa ke ciki da kuma kuma iyalansa.

  4. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Alhamis.

    Kamar kullum, yau ma za mu kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida da Abdullahi Bello Diginza ke fatan sake kasancewa da ku a daidai wannan lokaci.

    Za ku iya leƙawa shafukan sada zumuntanmu na intanet, da facebook da X da kuma whatsapp domin karanta sauran labarai da kallon bidiyo da tafka muhawara.