Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 26/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Shugaban Ghana ya amince ƴan Afirka su shiga ƙasar ba tare da biza ba

    Ghana

    Asalin hoton, Getty Images

    Shugaban ƙasar Ghana Nana Akufo-Addo, ya sanar da cewa dukan ƴan ƙasashen nahiyar Afika za su iya shiga ƙasarsa ba tare da takardar izinin ba wato biza.

    Da wannan sanarwa a yanzu Ghana ta bi sahun wasu ƙasashe irin su Rwanda da Seychelles da Gambia da kuma jumhuriyar Benin da suka sauƙaƙawa ƴan Afrika shiga ƙasarsu ba tare da biza ba.

    Shugaban ya ɗauki wannan matakin a daidai lokacin da yake ban-kwana da shugabancin ƙasar, bayan tsohon tsohon Shugaban Ƙasar John Mahama ya kayar da mataimakinsa shugaban na yanzu a zaɓen shugaban ƙasar.

  2. Assalamu alaikum

    Jama'a barkanmu da wannan safiya ta Alhamis daga wannan shafin da ke kawo muku labarai kai-tsaye daga sashen Hausa na BBC.

    Za kuma ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta domin karanta wasu labaran da kallon hotuna da bidiyo.

    Ku kasance tare da mu.