Sabuwar gwamnati a Syria ta ce
tana kai hare-hare kan mayaƙa masu
biyayya ga tsohon shugaban ƙasar,
Bashar al-Assad a lardin Ɗarɗous da ke yammacin ƙasar.
Kafar yaɗa labaru ta gwamnatin Syria ta ce
matakin ya kai ga abin da ta bayyana "kashe" da dama daga cikin waɗanda dakarun ƙasar suka yi artabu da su a jiya
Laraba.
Sojoji 14 ne na ƙungiyar HTS, wadda yanzu ke iko da
mafi yawa na ƙasar
aka kashe a artabun na jiya.
Rikicin na Ɗarɗous, wanda yanki ne na mabiya aƙidar shi'ar alawi, waɗanda stiraru ne kuma daga cikinsu ne
Bashar al-Assad ya fito, shi ne ƙalubale mafi girma na farko ga sabuwar gwamnatin,
wadda ta ƙwace
iko bayan korar tsohon shugaban ƙasar.
Shugaban ya yi alƙawarin murƙushe duk wanda ya yi ƙoƙarin yin zagon-ƙasa ga tsaron ƙasar ta Syria.