Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya 26/12/2024

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 26/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Isiyaku Muhammed

  1. Sai da safenku

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye nan muka kawo ƙarshen labarai da rahotonnin abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai kuma gobe idan Allah ya kai mu, za mu sake dawowa domin ci gaba da kawo muku sabbin labarai.

    A madadin sauran abokan aiki, Abdullahi Bello Diginza ke cewa mu kwana lafiya.

  2. Isra'ila ta yi luguden hare-hare a muhimman wurare a Yemen

    Wasu hare-hare da Isra'ila ta kai sun faɗa kan wurare da dama a ƙasar Yemen, ciki har da filin jiragen sama na ƙasar da ke Sanaa, babban birnin ƙasar.

    Isra'ila ta ce ta kai harin ne a kan cibiyoyin mayaƙan Houthi sanadiyyar hare-haren jirage marasa matuƙa da suke ta kai mata a makonnin nan.

    Cikin inda aka harba makaman har da wani sansanin sojoji da ke kusa da filin jirgin na Sanaa, da cibiyoyin samar da lantarki biyu da kuma titunan tashar jiragen ruwa ta Hodeida.

    Isra'ila ta ce mayaƙan Houthi na amfani da waɗannan wurare domin shigo da makamai daga Iran, da kuma shigo da wasu jami'an na Iran.

    Lamarin ya faru ne a lokacin da shugaban Houthi, Abdul-Malik al-Houthi ke gabatar da jawabi a kusa da wurin.

  3. Faransa ta miƙa wani sansanin da sojojinta suka zauna a Chadi ga gwamnatin ƙasar

    Faransa ta miƙa wani sansanin da sojojinta suka zauna a Chadi ga gwamnatin ƙasar, yayin da daɗaɗɗiyar yarjejeniyar tsaro da ke tsakaninsu ta zo ƙarshe.

    Sansanin Faya - da ke arewacin Chadi - shi ne na farko da Faransa ta mayar wa gwamnatin Chadi yayin da sojinta ke janyewa daga ƙasar.

    Ƙasashen yankin Sahel da dama ne suka kori Faransa daga cikinsu bayan jerin juyin mulki da aka samu, inda suka karkata ƙoƙon neman taimakonsu ga Rasha, a fafutikar da suke yi ta yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

    A baya, Chadi ta kasance ƙasa mafi aminci ga Faransa a yankin Afirka.

  4. An zargi Rasha da kakkaɓo jirgin ƙasar Azerbaijan

    jirgi

    Asalin hoton, Reuters

    Masana da masu harkar rubuce-rubuce a ɓangaren sufurin jiragen sama sun zargi Rasha da kakkaɓo jirgin nan na kamfanin sufurin jiragen sama na ƙasar Azerbaijan, wanda ya yi hatsari ranar Laraba, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 38.

    Babu dai wata hujja da suka bayar, amma sun ce shingen kariya daga makamai na Rasha ne ya yi zaton cewa jirgin, jirgi ne maras matuƙi na ƙasar Ukraine.

    Wasu da suka shaida hatsarin sun bayyana cewa sun ji ƙarar fashewa, sannan kuma hotuna da aka ɗauka na tarkacen jirgin sun nuna wasu ramuka a jikin jirgin da ka iya zama wuraren da makami ya huda.

    A lokacin da ya yi magana da manema labarai, mai magana da yawun gwamnatin Rasha, Dmitry Peskov ya ce bai kamata a riƙa yin shaci-fadi ba.

  5. Fursunan da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai saboda satar zabuwa ya samu afuwa

    zabuwa

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwanmnan jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ya yi afuwa ga wani fursuna mai suna Segun Olowookere da aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai da rai saboda samunsa da laifin fashi da makami da satar zabbi.

    Cikin wani saƙo da gwanan ya wallafa a shafinsa na x, ranar Alhamis ya ce ya yafe wa Mista Olowookere tare da wanda ake tuhumarsu tare.

    Hukuncin da aka yanke wa Olowookere ya ɗauki hankali a shafukan sada zumunta, bayan da aka yi iƙirarin cewa an yanke musu hukuncin ne kan satar sabuwa, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels ya ruwaito.

    To sai dai ma'aikatar shari'ar jihar ta ce an gurfanar da mutanen biyu ne bisa zargin fashi da makami, ciki har da satar zabbi a 2010.

    Haka kuma gwamnan ya ce ya gwamnatinsa ta yafe wa fursunoni 51 bisa shawarar majalisar bayar da shawara kan yafe wa fursunoni.

  6. Jirgin ruwa ya lalata wayar da ke kai wa Estonia lantarki

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    Ƴansanda a ƙasar Finland sun ce ƙugiyar wani jirgin ruwa ta lalata wayar da ke kai ƙarfin lantarki ga ƙasar Estonia, kuma sun bayyana cewa wani jirgi ne daga jiragen ruwa da ke da alaƙa da Rasha.

    Wayar ta daina aiki a ranar Laraba, inda kuma tuni ƴansanda suka kai samame kan jirgin wanda aka yi wa rajista da tsibirin Cook Island, wadda ƙasa ce ta yankin Pacific da kan bar jiragen wasu ƙasashen su yi amfani da tutarta.

    A cikin ƴan watannin da suka gabata, an ga yadda aka lalata wayoyin lantarki da dama a yankin Baltic.

    Ministan harkokin waje na Estonia ya ce abubuwan da aka shimfiɗa a ƙasan teku na cikin hatsari.

  7. Ɗan gwamnan Jigawa ya rasu kwana guda bayan rasuwar mahaifiyarsa

    Gwamnan jihar Jigawa

    Asalin hoton, Umar Namadi/X

    Bayanan hoto, Gwamna Umar Namadi

    Dan gidan gwamnan jihar Jigawa, Abdulwahab Umar Namadi, ya rasu kwana guda baya rasuwar mahaifiyar gwamnan.

    Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Hamisu Mohammed Gumel ya fitar, ya ce marigayin mai shekara 24 ya rasu ne ranar Alhamis da maraice, sakamakon wani mummunan hatsarin mota a kan hanyar Dutse zuwa Kafin Hausa.

    Marigayin na kan hanyarsa ne ta zuwa ta'aziyyar kakarsa - wadda ta rasu a ranar Laraba - lokacin da hatsarin motar ya rutsa da shi.

  8. MDD ta yi kira ga Isra'ila ta janye daga kudancin Lebanon

    MDD

    Asalin hoton, Reuters

    Rundunar wanzar da zaman lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya a Lebanon ta yi kira ga Isra'ila ta janye daga kudancin ƙasar a cikin lokaci.

    Rundunar ta ce ta damu ƙwarai da abin da ta bayyana da 'ci gaba da lalata unguwanni da gonaki da kuma hanyoyin da dakarun Isra'ila ke yi a yankin' duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta yi ƙoƙarin samarwa tsakanin Isra'ila da Hezbollah, wata ɗaya da ya gabata.

    Yarjejeniyar da aka cimma ta tanadi cewa dakarun Isra'ila da na Hezbollah za su janye zuwa ƙarshen watan Janairu.

    Sai dai dukkanin ɓangarorin biyu sun zargi juna da rashin martaba yarjejeniyar.

    Isra'ila ta ce tana duba buƙatar ta dakarun wanzar da zaman lafiyar suka gabatar.

  9. Sabuwar gwamnati a Syria ta ce tana kai hare-hare kan mayaƙa masu biyayya ga Assad

    Syria

    Asalin hoton, Getty Images

    Sabuwar gwamnati a Syria ta ce tana kai hare-hare kan mayaƙa masu biyayya ga tsohon shugaban ƙasar, Bashar al-Assad a lardin Ɗarɗous da ke yammacin ƙasar.

    Kafar yaɗa labaru ta gwamnatin Syria ta ce matakin ya kai ga abin da ta bayyana "kashe" da dama daga cikin waɗanda dakarun ƙasar suka yi artabu da su a jiya Laraba.

    Sojoji 14 ne na ƙungiyar HTS, wadda yanzu ke iko da mafi yawa na ƙasar aka kashe a artabun na jiya.

    Rikicin na Ɗarɗous, wanda yanki ne na mabiya aƙidar shi'ar alawi, waɗanda stiraru ne kuma daga cikinsu ne Bashar al-Assad ya fito, shi ne ƙalubale mafi girma na farko ga sabuwar gwamnatin, wadda ta ƙwace iko bayan korar tsohon shugaban ƙasar.

    Shugaban ya yi alƙawarin murƙushe duk wanda ya yi ƙoƙarin yin zagon-ƙasa ga tsaron ƙasar ta Syria.

  10. Boxing Day: Mece ce ranar kuma daga ina ta samo asali?

  11. Sokoto: Babu hujjar kashe mutanen da ba su ruwansu - Atiku

  12. An rufe wata kasuwa a Kano saboda tara ɓarayi da karuwai

    Shugaban ƙaramar hukumar, Aminu Salisu Kadawa ne ya tabbatar wa Daily Trust hakan, inda ya ce sun ɗauki matakin ne domin saita kasuwar.

    Ya ce an ba ƴankasuwar zuwa ranar 1 ga Janairu, inda ya ce duk wanda ya karya dokar, zai fuskanci hukunci.

    Ya ce, "ganin yadda kasuwar ta zama maɓoyar karuwai da ɓarayi da sauran harkokin baɗala, ya zama dole mu rufe kasuwar har sai mama ta gani."

    Sai dai Kadawa ya ce za su sanar da ranar da za a sake buɗe kasuwar.

  13. Finafinan Kannywood biyar da suka yi tashe a 2024

    Garwashi

    Asalin hoton, Umar UK

    A Kannywood, ana ta samun sauye-sauye, musamman a ɓangaren shirya fim da kasuwancinsa, inda daga CD aka koma sinima, yanzu aka koma YouTube, sannan ake ta hanƙoron shiga manhajojin duniya ka'in da na'in.

    A wannan shekarar, kamar kowace shekara, masu shirya finafinan Kannywood sun taka muhimmiyar rawa wajen tsarawa da fitar da finafinai masu kyau, waɗanda suka ƙayatar da masu kallo.

    Tun bayan komawa ɗora finafinai a YouTube, yanzu za a iya cewa harkokin Kannywood sun fara komawa yadda suke a baya, bayan a baya masana'antar ta fara durƙusawa.

  14. Ƴan arewacin Najeriya shida da soshiyal midiya ta yi wa rana a 2024

    Ƙarin bayani - https://bbc.com.im/hausa/articles/c9q7ne0w2e4o%3C/a%3E%3C/p%3E%3C/div%3E%3C/div%3E%3C/article%3E%3C/li%3E%3Cli class="css-xxlek1">

    Talauci bai san bambancin addini ko ƙabila - Ndume

  15. Lakurawa muka kai wa hari a Sokoto ba mutanen gari ba- Sojoji

    Soji

    Asalin hoton, DEFENCE HQ/X

    Dakarun haɗin gwiwa na jami'an tsaron Najeriya da suke aiki na musamman na Fansan Yamma sun mayar da martani kan harin da sojoji suka kai, wanda ya yi ajalin mutane a ƙaramar hukumar Silame ta jihar Sokoto.

    A jiya Laraba ne wasu hare-haren da sojojin Najeriya suka kai a wasu ƙauyuka da ke jihar Sokoto suka yi sanadiyyar mutuwar aƙalla mutum 10 da raunata wasu da dama.

    A wata sanarwa da kakakin aikin sojin, Laftanar kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, kan zargin sojoji da kai wa farareb hula, ya ce sun kai hare-haren ne bayan samun bayanan sirri.

    "Sojoji ba sa ƙaddamar da hare-hare yi sai an tattara bayanan sirri, musamman hari kan ƴanta'adda irin su Lakurawa, saboda dole a tabbatar harin ya kai gare su.

    "Ya kamata mutane su riƙa tantance bayanai domin gudun yaɗa labaran ƙarya tare da jefa tsoro a zuƙatan mutane. Akwai yiwuwar ƴanta'addan za su yi na amfani da yaɗa labaran ƙarya domin kawo tsaiko ga aikin sojin."

    Ya ƙara da cewa, "yankunan Gidan Sama da Rumtuwa da aka kai hare-haren, yankuna ne da aka gano akwai ƴan Lakurawa."

  16. A ƙara haƙuri da Tinubu – Ganduje

    Ganduje

    Asalin hoton, SALIHU TANKO YAKASAI

    Shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga ƴan Najeriya su ƙara haƙuri da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu duk da yanayin da ƙasar ke ciki na wahalar rayuwa.

    Ganduje ya bayyana haka ne a saƙonsa na Kirsimeti da sakataren watsa labaransa, Edwin Olofu, ya fitar, inda ya ce ƴan Najeriya za su dara domin tattalin arzikin ƙasar zai inganta a 2025, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

    Ganduje ya ce, "Ƴan Najeriya su ƙara haƙuri da gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu musamman game da matakan da ya ɗauka na inganta tattalin arziki waɗanda suka jawo wa ƴan ƙasar rashin jin daɗi.

    "Tuni an fara ganin sakamakon gyare-gyaren. Zuwa bikin Kirsimetin baɗi, tattalin arzikin ƙasar ya gyaru. Ɓangaren tsaro ma an fara ganin sakamako mai kyau domin an rage harkokin ƴanbindiga."

  17. Isra'ila ta kashe ƴanjarida biyar a Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, Reuters

    Bayanan hoto, Hoton wani gini da aka ruguza a Gaza

    Isra'ila ta kashe wasu ƴan jarida biyar a wani hari da ta kai kan motarsu a yau Alhamis, a ƙofar wani asibiti a Gaza, kamar yadda hukumomin lafiya a Zirin suka bayyana.

    Daga cikin ƴanjaridan da aka kashe, akwai wanda yake tsimayin haihuwar matarsa.

    Sai dai a ɓangaren rundunar sojin Isra'ila, ta musanta kashe ƴanjaridar, inda ta ce sojojinta sun ce waɗanda suka kashe ƴan ƙungiyar ta'adda ne.