Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/02/2025

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 20/02/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir da Abdullahi Bello Diginza

  1. Starmer ya goyi bayan Zelensky bayan Trump ya kira shi 'ɗan kama karya'

    Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya goyi bayan shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky a matsayin ''halastaccen zaɓaɓɓen shugaba'' bayan Donald Trump ya bayyana shi a matsayin ''ɗan kama karya''.

    A baya-bayan ne Donald Trump ya zargi Zelensky da rashin shirya manyan zaɓukan ƙasar, bayan ƙarewar wa'adinsa a ƙarshen watan Mayun 2024.

    Mista Starmer ya kira Shugaba Zelensky ta wayar tarho, inda ya ƙara jaddada goyon bayansa gare shi, sannan ya ce yana da ''ƙwaƙƙwarar hujjar'' dakatar da yin zaɓe a lokacin yaƙi.

    Firaministan na Birtaniya ya ce ƙasarsa ma ta taɓa ɗaukar irin wannan mataki a lokacin yaƙin duniya na biyu.

    Shi ma shugaban gwamnatin Jamus ya bayyana kalaman Trump da masu hadari waɗanda ba su dace ba.

    Matakan da shugaba Trump ke ɗauka kan rikicin Rasha da Ukraine na ci gaba da haifar da fargaba a ƙasashen Yamma.

  2. 'Shaguna 12 sun ƙone a gobarar kasuwar 'Fallujah Shopping Mall' da ke Yola'

    Jami'an hukumar kashe gobara da na NEMA sun samu nasara kashe wata gobara da ta tashi a kasuwar Fallujah Shopping Mall da ke birnin Yola ta jihar Adamawa.

    Cikin wata sanarwa da hukumar bayar da agajin gaggawa ta NEMA ta wallafa a shafinta na X, ta ce gobarar - wadda ta tashi cikin daren da ya gabata - ta janyo asarar dukiyoyi na miliyoyin kuɗi.

    NEMA ta ce jami'anta da na kashe gobara da na jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Adamawa, sun samu nasarar kai ɗauki domin kashe wutar.

    ''Babu labarin rasa rai, amma shaguna 12 sun ƙone ƙurmus, galibi na sayar da kayan wayoyin hannu, lamarin da ya haifar da asarar dukiya mai tarin yawa'', a cewar sanarwar.

    Kawo yanzu hukumomi sun ce suna ci gaba da bincike domin gano musabbanin gobarar.

    Gobara a kasuwannin Najeriya, wani abu ne da ya jima yana haifar da ɗimbin asarar dukiyoyi, inda a lokuta da dama hukumomi ke cewa za su gudanar da bincike domin ɗaukar matakai.

  3. Jirgin ƙasa ya kashe giwaye shida a Sri Lanka

    Wani jirgin ƙasan fasinja ya sauka daga kan layi bayan da ya kaɗe wasu giwaye a kusa da gandun dajin Habarana da ke tsakiyar Sri Lanka.

    Lamarin ya faru ne da safiyar yau Alhamis a daidai lokacin da dabbobin ke kiwo a kan digar jirgin.

    Ba a dai samu labarin jikkatar fasinjoji ba, amma giwaye shida sun mutu yayin da biyu suka jikkata a hatsarin da ya auku a gabashin Colombo, babban birnin ƙasar.

    Ba sabon abu ba ne jirgin ƙasa ya bi ta kan giwaye a Sri Lanka, inda irin wannan hatsari ya fi yawa a duniya.

    A shekarar da ta gabata fiye da mutum 170, da giwaye kusan 500 aka kashe a irin wannan hatsarin.

    Giwayen ƙasar, waɗanda ke fuskantar barazanar wuraren kiwo sakamakon sare dazuka na ƙara kusantar inda mutane ke al'amuransu domin yin kiwo.

    Hukumomi sun buƙaci direbobin jiragen ƙasa su riƙa amfani da ƙarar sautin ankararwar jiragen, wato ham domin ankarar da giwayen da ke kan titin jirgin.

  4. Za mu hana motocin dakon man fetur ɗaukar lita 60,000 - Gwamnatin Najeriya

    Hukumar kula da harkokin sarrafawa da tacewa da sufurin man fetur a Najeriya, NMDPRA ta bayyana haramta wa tankokin dakon man fetur ɗaukar lita 60,000 daga ranar 1 ga watan Maris mai zuwa domin rage yawaitar haɗurran tankokin dakon man mai a kan titunan ƙasar.

    Babban daraktar hukumar, mai lura rarrabawa da wuraren adana man, Ogbugo Ukoha ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da menama labarai bayan taron masu ruwa da tsaki na hukumar.

    Ya ce ɗaukar matakin ya zama wajibi la'akari da ƙaruwar haduran tankokin mai a kan titunan ƙasar, da a wasu lokuta ke zuwa mummunar asarar rayuka.

    Ya ce taron masu ruwa da tsakin - wanda ya samu halarta hukumomin tsaro da masu kula da sufuri kamar hukumar DSS da ta hukumar kiyaye aukuwar hadura da ƙungiyoyin NARTO da NUPENG da SON da DAPPMAN da MEMAN da NMDPRA - ya ɗauki matakin cewa ba za a bar duk tankar da ke ɗauke da litar mai fiye da 60,000 ta hau kan titi ba.

    A baya- bayan nan dai hatsuran tankokin man fetur a ƙasar ya haifar da asarar rayuka masu yawa.

  5. Labarai da dumi-dumi, Hamas ta miƙa wa Red Cross gawarwakin Isra'ilawan da take garkuwa da su

    Ƙungiyar Hamas ta kammala miƙa gawarwaki huɗu na Isra'ilawan da take garkuwa da su a Gaza.

    Mayaƙan Hamas ɗin ne suka ɗauko gawarwakin ɗaya-bayan-ɗaya daga kan dandamali inda ta gabatar da su, zuwa cikin motocin ƙungiyar Red Cross.

    Motocin Red Cross huɗu ne dai suka yi layi a wurin, domin daukar gawarwakin.

    Mutane da dama ne suka taru domin kallon miƙa gawarwakin, yayin da mayaan Hamas ke tsaye a wurin riƙa da makamai.

  6. An ajiye gawarwakin Isra'ilawan a kan dandamali gabanin miƙa su ga Red Cross

    Hotunan da ke fitowa daga Gaza na nuna gawarwakin Isra'ilawa a kan dandamalin da Hamas ta shirya a Khan Younis da ke kudancin Gaza domin miƙa su ga Red Cross.

    Tuni dai motocin Red Cross suka isa wurin domin ɗaukar gawarwakin domin mayar da su Isra'ila.

    Hamas dai ta ce uku daga cikin gawarwakin na iyalan Bibas ne, yayin da guda ya kasance mai gwagwarmayar tabbatar da zaman lafiya.

  7. Labarai da dumi-dumi, Motocin Red Cross sun isa Khan Younis don ɗaukar gawarwakin Isra'ilawa

    Motocin ƙungiyar agaji ta Red Cross sun isa birnin Khan Younis domin ɗaukar gawargwakin Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su.

    Tuni dai mayaƙan Hamas suka fara taruwa a wurin da aka shirya miƙa gawarwakin.

  8. Hamas na shirin miƙa gawarwakin Isra'ilawa huɗu ga Red Cross

    Falasinawa na ci gaba da taruwa a kudancin Gaza yayin da Hamas ke shirin mia wa Red Cross gawarwakin Isra'ilawa huɗu da suka mutu a lokacin da take garkuwa da su.

    Ƙungiyar Hamas ta ce gawarwakin na iyalan Bibas ne da suka haɗa da uwa mai suna Shiri Bibas da ƙananan yaranta biyu, Kfir mai wata tara da kuma Ariel mai shekara huɗu

    Na huɗun shi ne Oded Lifshitz,, ɗan gwagwarmayar tabbatar da zaman lafiya.

    To sai dai ISra'ila ta ce ba za ta tabbatar da mutanen ba, har sai ta gudanar da gwajin ƙwayoyin halitta a kan gawarwakin.

    Ana sa ra sankin wasu Isra'ilawa masu rai a ranar Asabar mai zuwa.

  9. Marabanku

    Masun bin shafin BBC Hausa kai-tsaye, barkanmu da safiyar wannan rana da Alhamis.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kun wayi gari lafiya, tare da fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokaci, domin kawo muku halin da wasu sassan duniya ke ciki.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa