Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Abin da ƴan fansho ke cewa kan biyan haƙƙoƙinsu a Najeriya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da wata takardar lamuni ta naira biliyan dari bakwai da hamsin da takwas, domin sauke nauyin bashin da aka dade ana bi na kudaden fansho na ma'aikatan tarayya a duk fadin kasar, a karkashin shirin nan na fansho na hadakar kudi tsakanin ma'aikaci da wurin aikinsa.
Wannan dai shi ne karon farko da gwamnatin tarayyar Najeriya ta jibga makudan kudi ga asusun kare tsarin na fansho, a matsayin wani tanadi da zai tallafa wa kudaden fanshon na ma'aikata.
Amma kuma tun shekara ta 2014 rabon da gwamnati ta sa wa asusun kudade.
Bisa ga dukkan alamu, haƙata cimma ruwa, dangane da koke-koken da tsofaffin ma'aikatan tarayya ke ta yi, a kan dimbin basukan wasu hakkokinsu da suke bi shekara da shekaru.
Abdul'aziz Abdul'aziz shine mai magana da yawun shugaban Najeriya, ya kuma shaida wa BBC cewa shirin zai mayar da hankali musamman kan ma'aikatan da ke cikin tsohon tsari da suke yawan samun matsala wajen biyansu haƙƙoƙinsu.
"Shugaba Tinubu ya duba halin da wadanda suka bar aiki ke ciki, shiyasa ya amince da ba da wadannan maƙudan kuɗaɗe domin awarware matsalar d ata daɗe tana ciwa ƴan fansho tuwa a ƙwarya."
Abdul'aziz ya ce ba da jimawa gwamnati za ta fara biyan wadannan kudade, "Daman amincewar ce keda wahala, amman yanzu tunda an amince, ma'aikatar kudi za ta yi aiki tare da hukumar fansho, domin fitar da wadannan kudade domin fara biyansu."
Malam Muhammadu Mamman, jami'in hulda da jama'a na kungiyar masu karbar fansho na jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya, ya ce wannan abin farinciki ne ga daukacin 'yan fansho na tarayya.
Sai dai kuma suna fata a biya su hakkokin nasu a dunkule, kar a yi masu biyan bashi daddawar mutanen kauye, wato a biya wani bashin, amma kuma a dauki wani.
"Mun farinciki sosai, sai dai roƙon da muke da shi na yadda za a kasafta, tunda kudaden kashi-kashi ne suna da yawa,a biya mu a dunƙule domin suyi mana amfani.
Shi ma wannan kira ana fata an yi shi a gaban 'yan amin, domin kwalliyar wadannan kudaden da gwamnatin tarayya ta ware ta biya kudin sabulu.