Faransa ta miƙa wa hukukomin Ivory Coast sansanin sojinta ɗaya tilo da ke ƙasar, a wani mataki na kawo ƙarshen ayyukan sojojinta a ƙasar na tsawon gomman shekaru.
Ministocin tsaron ƙasashen biyu ne suka sanya hannu kan takardun miƙa sansanin, jim kaɗan bayan ɗaga tutar Ivory Caost a filin farenti na sansanin.
Ministan tsaron Ivory Coast Tene Birahima Ouattara ya ce matakin wani sabon babi ne a ƙawancen da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Yayin da shi kuma takwaransa na Faransa, Sebastien Lecornu ya ce sauyi za a samu a wanzuwar Faransa a Ivory Coast, ba shuɗewa ba, inda ya bayyana bikin miƙa sansanin a matsayin wani mataki na tarihi.
Sansanin mai girman eka 570 da ke kusa da Abidjan, babban birnin ƙasar ya kasance wani muhimmin wuri a harkar tsaron ƙasar tun shekarar 1987, inda ya taimaka wajen daidaita ƙasar - wadda ke kan gaba a arzikin cocoa a duniya - bayan juye-juyen mulki da tashin hankalin da ya ɓarke a ƙasar bayan 2000.
An kuma sauya wa sansanin suna zuwa 'Thomas d'Aquin Ouattara'- sunan babban hafsan sojin ƙasar na farko - da aka sanya hotonsa a sansanin domin girmamawa a gare shi.
Faransa na sake fasalta alaƙar sojinta da ƙasashen Afirka bayan korar dakarunta daga ƙasashen Mali da Burkina Faso da kuma Nijar - inda sojojin da ke adawa da Faransa suka ƙwace mulki.
Kusan sojoji 1,000 ne Faransa ta girke a sansanin domin taimaka wa dakarun ƙasar wajen yaƙi da masu iƙirarin jihadi da ke ƙaddamar da hare-hare a wasu sassan ƙasashen yammacin Afirka.
To sai dai ana sa ran kimanin sojoji 100 za su ci gaba da zama domin bayar da horo da taimaka wa ayyukan wanzar da zaman lafiya.
Alaƙar soji tsakanin ƙasashen biyu ta faro ne tun shekarar 1961 lokacin da suka sanya hannu kan yarjejeniyar soji, bayan samun ƴancin kan ƙasar, yayin da alaƙar ƙasashen biyu ta soma tun zamanin mulkin mallaka.