Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a sauran sassan duniya, Asabar 11/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Daga Abdullahi Bello Diginza

  1. Wakilan Lebanon da Isra'ila za su gana da a Amurka

    Wakilai daga Lebanon da Isra’ila za su gana a birnin Washington a ranar Talata, ƙarƙashin shiga tsakanin Amurka, wata guda bayan sake ɓarkewar rikici mai muni tsakanin Isra’ila da Hezbollah.

    Ɓangaren Isra’ila ya ce a shirye yake ya tattauna abin da ya kira shawarwarin zaman lafiya da gwamnatin Lebanon.

    Sai dai ya ce ba zai tattauna yiwuwar tsagaita wuta da ƙungiyar Hezbollah ba, tare da cewa zai nemi a kwance ɗamarar ƙungiyar.

    Isra’ila na cewa hare-haren da take kaiwa a ƴan makonnin nan na shafar wuraren da Hezbollah ke da ƙarfi ne kawai, to sai dai hare-haren sama da ta kai sun kashe kusan mutane 2,000, ciki har da yara da mata da dama, da kuma likitoci da ƴan jarida da malamai.

    Asibitoci sun cika maƙil sakamakon yawan waɗanda suka jikkata.

    Fiye da mutum miliyan guda ne hare-haren suka raba da matsugunansu.

  2. Wakilan Iran sun isa Pakistan domin tattaunawar kawo ƙarshen yaƙin ƙasar

    Mataimakin shugaban Amurka

    Asalin hoton, pool

    Wata tawaga daga Iran ta isa birnin Islamabad na Pakistan domin tattaunawa da Amurka da nufin kawo ƙarshen rikicin da aka shafe sama da makonni shida ana gwabzawa.

    Shugaban majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, wanda ke jagorantar tawagar, ya ce a shirye Tehran take ta ƙulla yarjejeniya idan Amurka ta amince da haƙƙoƙinta.

    A baya ya ce ba za a yi wata tattaunawa ba har sai an tsagaita wuta a Lebanon.

    Idan har tattaunawar ta gudana, to kuwa zai kasance an kafa tarihi, domin za ta zamo tattaunawa mafi girma tsakanin ƙasashen biyu tun bayan juyin juya halin Musulunci na 1979.

    A gefe guda, shugaban Amurka Donald Trump ya ce ya yi wa mataimakinsa, J. D. Vance, fatan alheri yayin da zai halarci tattaunawar.

    Ya kuma ce za a buɗe mashigar Hormuz “ko da Iran ta amince ko ba ta amince ba.”

  3. Assalamu alaikum

    Masu bin shafin BBC Hausa kai-tsaye barkanmu da safiyar wannan rana ta Asabar.

    Abdullahi Bello ke fatan sake kasancewa da ku domin kawo muku irin wainar da ake toyawa game da tattaunar kawo ƙarshen yaƙin Iran da sauran batutuwa.

    Ku biyo mu a shafukanmu na sada zumunta domin tafka muhawara kan labaran da muke wallafawa.