Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo mu ku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 30/01/2025

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Ahmad Bawage da Aisha Aliyu Jaafar

  1. NLC za ta yi zanga-zanga don adawa da ƙarin kuɗin kiran waya

    NLC

    Asalin hoton, NLC

    Ƙungiyar ƙwadago ta NLC a Najeriya ta ce za ta gudanar da gagarumar zanga-zanga ranar Talata 4 ga watan Febrairun 2025, domin adawa da ƙarin kuɗin kiran waya da kashi 50 wanda Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC ta amince da shi.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta hannun shugabanta Joe Ajaero, ya ce sun ɗauki matakin ne a wani taron gaggawa da suka gudanar ranar Laraba.

    NLC ta ce zanga-zangar za ta zama gargaɗi ga hukumomi kan yunkurin kakabawa mutane ƙarin kuɗin kiran waya a ƙasa kuma da albashi mafi ƙanƙanta bai wuce naira 70,000 ba, ga kuma ƙarin farashin mai da na abinci da lantarki da kuma ƙaruwar hauhawarar farashi.

    Ƙungiyar ta buƙaci rassanta na jihohi da su fara shirya mambobinsu domin shiga zanga-zangar ta ƙasa baki-ɗaya, inda ya yi kira ga ƙungiyoyin fararen hula da su ma su fito.

    Ta kuma yi kira ga ma'aikata da kuma ɗaukacin ƴan Najeriya da su tsaya kai da fata wajen yin watsi da wannan tsari da kuma waɗanda ba su alheri gare su.

    Ƙungiyar ƙwadagon ta kira yi gwamnatin tarayya da NCC da hukumar majalisar tarayya da su zauna don tattaunawa da masu ruwa tsaki domin sake duba wannan ƙari a daidai lokacin da ƴan ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

  2. Za mu kaddamar da gagarumin farmaki kan ƴan tawaye - Shugaban Kongo

    Kongo

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Jamhuriyar Dimukradiyyar Kongo ya sha alwashin mayar da ƙarfin ikon gwamnatinsa a gabashin ƙasar inda ƴan tawayen M23 da Rwanda ke mara wa baya suka karɓe ikon birnin Goma.

    A jawabin da ya yi wa ƴan ƙasa, Felix Tshisekedi, ya ce zai ƙaddamar da gagarumin hari kan abin da ya kira ƴan ta'adda.

    Ya kuma ce ƙasashen waje sun gagara taka musu birki.

    An yi ta tattaunawar wayar tarho daga Amurka da Majalisar Ɗinkin Duniya kan Alla-wadai da karɓe ikon birnin Goma, da kiraye-kirayen ƙasashen waje kan ƴan tawayen su janye.

    Amma da alama M23 da Rwanda ke mara wa baya ta yi biris da hakan.

    Rahotanni na cewa ƴan tawayen M23 na ci gaba da dannawa ɓangaren kudancin Congo, tare da karɓe yankuna da dama.

  3. Musayar fursunoni: Hamas ta saki Agam Berger

    Hamas ta saki Agam Berger - An yi garkuwa da ƴar shekara 20 ɗin ne bayan kaddamar da hari da ƙungiyar ta kai cikin Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoban 2023.

    Zuwa yanzu an miƙa ta hannun jami'an Isra'ila inda ta nufi kudancin ƙasar domin sake haɗuwa da iyalanta.

    An sake Agam ne a safiyar yau a birnin Jabalia da ke arewacin Gaza.

    Agam

    Asalin hoton, Reuters

    Agam

    Asalin hoton, Reuters

  4. Labarai da dumi-dumi, An gano aƙalla gawawwaki 19 a hatsarin jirgin sama a Amurka

    Hukumomi sun ce an gano aƙalla gawawwaki 19 a hatsarin jirgin fasinja da ya afku a Amurka, kamar yadda wani jami'i da ke cikin masu bincike ya shaida wa gidan talabijin na CBS.

  5. Za a yi musayar fursunoni karo na uku tsakanin Isra'ila da Hamas

    Arbel Yehud da Agam Berger da Gadi Moses

    Asalin hoton, Hostages and Missing Families Forum

    A yau Alhamis ake sa ran za a yi musayar fursunoni a karo na uku tsakanin Isra'ila da Hamas, inda ake sa ran Hamas za ta sako ƙarin Isra'ilawa uku da suke tsare da su.

    Ana sa ran wasu ƴan asalin Thailand 5 na daga cikin waɗanda za su shaki iskar ƴanci.

    Isra'ila dai za ta miƙa Falasdinawa 110, cikinsu akwai mata 30 da kuma yara.

    An samu tsaikon ci gaba da musayar fursunonin ne, bayan fusatar da Isra'ila ta yi, kan ƙin sanya Arbel Yahud cikin waɗanda Hamas za ta saka, lamarin da ya janyo Isra'ila daukar matakin wucin gadi na hana Falasdinawa da ke komawa arewacin Gaza bayan shafe watanni sama da 15 suna gudun hijira.

    A lokacin an yi ta raɗe-raɗin watakil an kashe Yahud, to amma bayan Isra'ila ta samu tabbacin ta na raye, sai ta buɗewa dubun dubatar Falasdinawa da sukai dafifi a bakin iyaka wucewa domin komawa gida.

    A ɓangare guda kuma ana sa ran sakin karin Isra'ilawa uku a jibi Asabar.

  6. Ana can ana aikin ceto bayan hatsarin jirgin fasinja a Amurka

    Hatsari

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani jirgin sama ya yi hatsari tare da faɗa wa kogin Potomac a Washington DC, bayan taho mu gama da ya yi a sama da jirgin soji mai saukar ungulu.

    Jirgin ya taso ne daga Kansas, yana tunkarar filin jirgin sama na Reagan a lokacin da ya yi hatsarin. Fasinjoji 64 ne dai ke cikin jirgin, yayin da sojoji uku ne cikin mai saukar ungulu.

    Jami'ai sun ce karamin jirgin fasinjojin mallakin kamfanin Eagle na kokarin sauka a filin jirgin sama na Reagan, a lokacin da helikoftan sojojin ya yi taho mu gama da shi, nan take wuta ta kama.

    Jaridar Washington Post ta ruwaito wani jami'in yankin na cewa ma'aikatan ceto sun fara zakulo gawawwaki da suka fada kogin.

  7. Assalamu alaikum

    Masu bibiyar mu barkan mu da safiyar Alhamis.

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye na BBC Hausa.

    Ku kasance da mu domin samun labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da kuma sauran sassan duniya.