Yaƙin Iran da sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi na kawo muku muhimman abubuwan da ke faruwa dangane da yaƙin Iran da kuma sauran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya na 20/04/2026

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman MINJIBIR

  1. Firaiministan canada ya kudiri niyyar farfaɗo da alaƙarsa da Amurka

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Firaministan Canada, ya ce dangantakar tattalin arziƙi tsakanin ƙasarsa da Amurka ta yi tsami, kuma dole ne a tashi tsaye don farfaɗo da ita.

    A cikin wani jawabi ta bidiyo, Mark Carney ya ce harajin shigo da kaya da gwamnatin Turump ta ƙaƙaba sun yi matukar illa ga ma’aikata a masana’antun mota da na ƙarafa a ƙasar.

    Mark Caney, ya ce Canada na ƙoƙarin faɗaɗa hanyoyin saka jari da kuma ƙulla yarjejeniyoyin kasuwanci da sauran ƙasashen duniya.

    Dangantakar shugabannin biyu ta yi tsami tun bayan da Mista Carney ya zama firaminista a bara, kuma ƴan Canada da dama sun fusata da barazanar da Mista Trump ya yi ta mayar da ƙasarsu jiha ta 51 ta Amurka.

  2. Ƴansandan Louisiana sun ce mutumin da ya harbe yara 8 mahaifinsu ne

    ‘Yan sanda a jihar Louisiana a Amurka sun ce mutumin nan da ya harbe yara takwas ranar Lahadi shi ne mahaifin dukkansu ba wai daya daga cikin mutanen da aka harbe ba.

    An kuma raunata mata biyu a hare-haren da suka faru a birnin Shreve-port. Ƙaramin cikin wadanda aka kashe din shine dan shekara ɗaya kacal a duniya.

    Ƴan sanda sun kashe mahaifin da aka bayyana sunansa da Shamar Elkins, bayan sun bi sawunsa lokacin da ya yi ƙoƙarin tserewa a cikin wata mota da ya sata.

    Wannan shi ne hari mafi muni daga hare-haren bindiga dadi masu yawa da aka kai kasar cikin shekaru biyu.

  3. Pakistan na shirin karɓar baƙuncin Amurkawa da Iraniyawa domin tattaunawa

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Pakistan na shirin karɓar baƙuncin zagaye na biyu na tattaunawar zaman lafiya tsakanin Iran din da Amurka a wannan mako, sai dai har yanzu babu tabbaci ko Iran za ta halarta.

    Kafofin watsa labarai na gwamnati sun ce wakilan Tehran ba su da niyyar shiga tattaunawar, muddin Washington na ci gaba da toshe tashoshin jiragen ruwan ƙasar.

    Har yanzu dai manyan shugabannin Iran ba su ce ko kanzil ba, game da lamarin tukuna.

    Fadar White House ta ce tawagarta za ta kasance ƙarƙashin jagorancin mataimakin shugaban ƙasar JD Vance.

    Shugaba Donald Trump ya yi barazanar lalata tashoshin wutar lantarki da gadojin Iran idan ba a cimma yarjejeniya ba.

  4. Iran ta sha alwashin ɗaukar fansar tare jirginta da Amurka ta yi

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    Iran ta yi alƙawarin ɗaukar fansa bayan Amurka ta ƙwace wani jirgin dakon kayanta a Tekun gabas ta tsakiya.

    Sojojin Amurka sun ce sun budewa jirgin wuta, lamarin da ya lalata injinsa, bayan ya yi ƙoƙarin wucewa ta shingen da Amurkar ta kafa.

    Wakiliyar BBC ta ce shugaba Trump ya ce sojin ruwan Amurkar sun gargadi matuka jirgin da su dakata, amma suka yi kunnen kashi.

    Wani kakakin sojojin Iran ya bayyana kwace jirgin a matsayin fashin teku, kuma saba yarjejeniyar zaman lafiyar da ke aiki.

  5. Buɗewa

    Masu bibiyarmu barka da warhaka da fatan an yi wayi garin ranar Litinin lafiya wadda ake yi wa take da ko nasara na tsoron ki. Yau ma kamar kullum mun dawo muku da shafin namu na kai tsaye inda muke kawo muku muhimman labarai dangane da al'amuran yau da kullum.

    Da fatan za ku ci gaba da kasancewa da shafin da ma sauran shafukan sada zumunta na BBC Hausa.