Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Usman Minjibir, Umar Mikail, Aisha Babangida da Umaymah Sani Abdulmumin

Assalamu Alaikum

Ma'abota BBC Hausa barkanmu da hantsin Litinin.

Sannunmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotonnin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙwabtansu.

Umar Mikail da Aisha Babangida ne ke tare da ku a wannan safiya bisa kulawar Usman Minjibir.