Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Nigeria 1-1 South Africa: Wasan neman shiga Kofin Duniya

Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Babu wata matsala tsakanina da Lukman, in ji Victor Boniface

    Ɗan wasan gaba na Najeriya Victor Boniface ya ce babu wata matsala tsakaninsa da abokin wasansa Ademola Lukman bayan Atalanta ta doke Bayer Leverkusen a wasan ƙarshe na gasar zakarun Turai ta Europa League.

    Lukman ne ya ci wa Atalanta ƙwallayen uku rigis da ta doke Leverkusen a wasan da suka buga a watan Yuni, wanda shi ne karon farko da duka 'yan wasan na Najeriya suka buga wasan ƙarshe a gasar zakarun Turai.

    Sai dai bayan da Boniface ya gaza buga wa Najeriya wasa a gasar Kofin Ƙasashen Afirka ta 2023 saboda rauni, yanzu 'yan wasan biyu sun haɗu a sanasanin Super Eagles ɗin domin buga wasan neman shiga Kofin Duniya na 2026.

    "Ɗan Najeriya ne shi, ni ma ɗan Najeriya ne. Ɗan'uwana ne shi, ya je ne don ya yi nasara ni ma na je don na yi nasara, ba abin da ya dame ni," kamar yadda Boniface ya shaida wa BBC.

    "Amma dai a ƙarshe su ne suka yi nasara kuma ina taya shi murna."

    Anjima a yau Najeriya za ta buga wasan farko cikin biyu tare da Afirka ta Kudu a birnin Uyo na jihar Akwa Ibom, inda za ta buga na biyun da Benin a Ivory Coast ranar Litinin.

  2. Chelsea ta ɗauki Adarabioyo daga Fulham

    Chelsea ta ɗauki ɗan wasan baya na Fulham Tosin Adarabioyo kyauta bisa yarjejeniyar shekara huɗu.

    Adarabioyo mai shekara 26 zai koma Stamford Bridge ne idan kwantaraginsa ya ƙare a ƙarshen watan nan, kuma an fahimci cewa yana so ya koma can ne don ya buga gasar zakarun Turai ta Europa Conference League.

    Tsohon ɗalibi a Manchester City, Adarabioyo ya ƙi amincewa da sabon tayin da Fulham ta yi masa a watan Afrilu, inda zai zama ɗan wasan mafi yawan albashi a ƙungiyar.

    "Chelsea babban kulob ne kuma wannan lokaci ne mai muhimmanci a gare ni. An haife ni mil uku kacal daga Stamford Bridge kuma a nan na fara buga ƙwallon ƙwararru," in ji Adarabioyo.

    "Ina cikin farin ciki sosai kuma na ƙagu na fara taimaka wa kulob ɗin cimma abin da muka sa a gaba."

    Chelsea na fatan zuwan ɗan wasan zai taimaka wajen hanzarta tafiyar Trevoh Chalobah, wanda Man United ke nema.

    Thiago Silva mai shekara 39 ma zai bar Chelsea zuwa Fluminense ta Brazil kafin sabuwar kaka.

  3. Assalamu Alaikum, Barkanmu da Juma'a

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye na wasanni.

    Ku biyo ni Umar Mikail don sanin yadda take kasancewa a duniyar wasannin.