Najeriya ta kai hari, Nigeria 0-1 South Africa
Kyaftin Najeriya, Wilfred Ndidi, ya ɗaɗata ƙwallo daga wajen yadi na 18, amma gola Romwen Williams ya cafke ta.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku rahotonni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a duniyar wasanni na ranar 6 ga watan Yuni, 2024.
Umar Mikail
Kyaftin Najeriya, Wilfred Ndidi, ya ɗaɗata ƙwallo daga wajen yadi na 18, amma gola Romwen Williams ya cafke ta.
Ɗan wasan gaba na Afirka ta Kudu, Zwane ya kusa ƙara wa Najeriya ba don Nwabali ya fito ya tare shi ba. Da kyar Bassey ya fitar da ƙwallon zuwa bugun kwana.
An bai wa Modiba na Afirka ta Kudu katin gargaɗi.
Zwane ya yi kwance-kwance, ya yayyaga 'yan bayan Najeriya kuma ya jefa ƙwallon a ragar Nwabali ba tare da wata matsala ba.
Ƙwallo ce mai ƙayatarwa domin sai da ya bayar da mutum biyu kafin ya shauɗa ta raga, kuma duk da Nwabali ya kai mata cafka hakan bai sauya komai ba.
Najeriya za ta buga bugun tazara mai haɗari bayan an kayar da Lookman
Themba Zwane na Afirka ta Kudu ya ɗaɗa ƙwallo mai haɗari daga bugun tazara kuma ta bigi tirken sama ta yi waje.
Wasan ya fara zafi da gaske
An bai wa Osayi Samuel katin gargaɗi saboda ƙeta.
Osayi Samuel ya kayar da ɗan wasan Afirka ta Kudu a kusa da da'irar yadi na 18 na Najeriya.
Ɗan wasan Afirka ta Kudu, Rayners ya yi satar gida - amma ba don haka ba da tuni labari ya sha bamban.
Ademola Lookman na Najeriya ya ɗaɗa ƙwallo daga ɓangaren hagu, amma ta yi faɗi zuwa waje.
Ɗan wasan Afirka ta Kudu ya yi satar gida
Gola
Williams
'Yan baya
Mudau, Ngezana, Mvala, Modiba, Mokuena
'Yan tsakiya
Sithole, Zwane, Tau
'Yan gaba
Mokwana, Rayners
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta fitar da jerin 'yan wasan da za ta fara fuskantar Afirks ta Kudu da su. Su ne:
Gola
Nwabali
'Yan Baya
Tanimu, Ajayi, Bassey, Samuel
'Yan tsakiya
Ndidi, Iwobi, Bashiru
'Yan gaba
Lookman, Iheanacho, Onuachu
'Yan benci:
Moffi, Boniface, Onyeka, Abdullahi, Chukwueze, Awaziem, Olawoyin, Ismaila, Onyedika.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta kammala atasayen tunkarar Afirka ta Kudu a wasan neman shiga Kofin Duniya na 2026 a safiyar yau.
Nan gaba kaɗan za a take wasan fallen farko a garin Uyo na Najeriya, kafin ta ziyarci Afirka ta Kudu a 2025.
'Yan wasan tawagar Bafana Bafana ta Afirka ta Kudu sun yi atasayensu na ƙarshe a safiyar yau kafin karawar da za su yi da Najeriya.
Awa biyu da rabi kawai suka rage kafin fafatawar da za a yi a filin wasa na Godswill Akpabio da ke birnin Uyo na jihar Akwa Ibom.
Ɗan wasan gaba na Leicester City Jamie Vardy ya saka hannu kan yarjejeniyar ƙarin shekara ɗaya da ƙungiyar mai buga gasar Premier League.
Vardy ya fara taka wa Leicester leda tun 2012 kuma ya ci ƙwallo 190 cikin wasa 464.
Ɗan wasan mai shekara 37 ya lashe kofin Premier da ƙungiyar a kakar 2015-16.
"Na daɗe ina faɗa cewa shekaru lamba ce kawai," a cewar kyaftin ɗin na Leicester.
"Ina jin ƙafafuwana lafiya ƙalau shi ya sa na yanke shawarar cigaba har sai sun ce: 'Shikenan, an gama'. Na san irin wannan ranar na zuwa amma dai ba yanzu ba."
Tsohon ɗan wasan Ingilan ya kuma lashe kofin FA, da Community Shield, da kofin Championship biyu a Leicester, wanda ya bai wa ƙungiyar damar haurowa gasar Premier League a kaka mai zuwa.
Tawagar The Pharaohs ta Masar ta doke Burkina Faso a wasan neman gurbin gasar Kofin Duniya ta 2026 a daren jiya.
Ɗan wasan gaba Trezeguet ne ya ci wa Masar ƙwallayen biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci, inda Lassina Traore ya farke wa Burkina ƙwallo ɗaya jim kaɗan bayan dawowa daga hutun.
Da wannan sakamako, Masar ta ci gaba da zama a mataki na ɗaya da maki 9, sai Guinea-Bissau ta biyu da maki biyar, da kuma Burkina a mataki na uku da maki huɗu.
Ranar Litinin Masar ɗin za ta shawo ta da Guinea-Bissau a wasa na biyu na wannan zagayen.
Ghana ta doke Mali 2-1 a wasan neman shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da suka buga ranar Alhamis da dare.
Kamory Doumbia ne ya fara ci wa Mali ƙwallo ana dab da tafiya hutun rabin lokaci, kafin Ernest Nuamah ya farke ta minti 13 da dawowa daga hutun.
Sai bayan minti huɗu da cikar lokaci tauraron ɗan wasa Jordan Ayew ya ci wa Ghana ƙwallon nasarar, abin da ya sa magoya baya ɓarkewa da sowar murna.
Sakamakon ya mayar da Ghana ta biyu a saman teburi da maki shida, yayin da Mali ke biye mata da maki huɗu. Sai kuma Comoros ta ɗaya mai maki shida kafin ta buga wasanta da Madagascar a yammacin yau.
Sai a ranar Litinin Ghana za ta karɓi baƙuncin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a wasa na gaba a birnin Kumasi.