Gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya sun ce za su kafa rundunar tsaron haɗin gwiwa

Asalin hoton, Babajide Sanwo-Olu/X
Gwamnonin yankin kudu maso yammacin Najeriya sun amince da kafa wata rundunar tsaron haɗin gwiwa da za ta riƙa sanya idanu kan matsalolin tsaro a yankin.
Cikin wata sanarwar bayan da taro da ƙungiyar gwamnonin yankin ta fitar, bayan wani taro da ta gudanar a fadar gwamnatin jihar Legas, ta ce matakin ya zama wajibi, sakamakon rahotonin ɓullar ƙungiyar ISWAP da wasu ƙungiyoyin ƴanbindiga a yankin.
Cikin watan Janairu ne gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya ce ƴanbindigar da ake fattaka daga wasu yankunan arewacin ƙasar na kwarara zuwa wasu sassan jiharsa.
Lamarin da ya sa masu ruwa da tsaki na yankin - ciki har da ƙungiyar cigaban Yarabawa ta Afenifere - suka riƙa kiraye-kirayen ɗaukar matakan daƙile hakan.
Ƙungiyar gwamnonin yankin ta ce ɓullar ƴanbindigar a yankin babbar barazana ce ga zaman lafiya da tsaron ilahirin yankin kudu maso yammacin ƙasar.
Gwamnonin sun kuma ce sabuwar rundunar za ta yi aiki rundunar ƴansanda da sauran jami'an tsaro domin tabbatar da tsaron yankin.
Shugaban ƙungiyar, wanda shi ne gwamnan jihar Legas ya ce za a samar wa sabuwar rundunar cikakkun kayan aiki na zamani ciki har da jirage marasa matuƙa.
Taron ya samu halartar duka gwamnonin yankin kudu maso yammacin ƙasar.






