Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/02/2025

Wannan shafi ne d ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 14/02/2025

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Haruna Ibrahim Kakangi, Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Mu kwana lafiya

    Mun zo karshen rahotanni a wannan shafi na labarai kai-saye.

    Fatan kun ji daɗin kasancewa da mu daga sanyin safiya zuwa yanzu.

    Sai kuma gobe da safe idan Allah ya kai mu.

    Ahmad Bawage ke cewa asuba ta gari.

  2. WHO ta ce gomman majinyata sun tsere daga asibiti a Kongo

    Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce gomman majinyata da suke ɗauke da cutar ƙyandar biri sun tsere daga asibiti a Gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kongo sakamakon rikici.

    WHO ta ce akwai sama da mutum 140 da suke ɗauke da cutar waɗanda ake yi wa magani a killace a cibiyoyi da dama a birnin Goma.

    Yan tawayen M23 dai na ci gaba da dannawa zuwa birnin Bukavu yayin da rahotanni suka bayyana janyewar sojojin Kongo.

  3. Masu gabatar da ƙara bakwai sun ajiye aiki a Amurka

    Amurka

    Asalin hoton, Getty Images

    Masu gabatar da ƙara bakwai sun ajiye aiki a ma'aikatar shari'a ta Amurka.

    Sun ajiye aikin ne bayan ba su umarnin janye tuhumar cin hanci da ake yi wa magajin garin New York Eric Adams.

    Sanarwar ajiye aikin ta biyo ne bayan ma'aikatar shari'ar ta sanya wa lauyoyin wa’adin zaɓar wanda zai gabatar da kudirin watsi da tuhumar.

  4. 'Harin da Rasha ta kai Ukraine ya nuna ba ta son zaman lafiya'

    Babbar jami'ar harkokin waje a ƙungiyar Tarayyar Turai Kaja Kallas, ta ce harin da Rasha ta kai cibiyar makaman nukiliya ta Chernobyl a Ukraine cikin dare alama ce cewar Rasha ba ta son zaman lafiya.

    Ministan harkokin wajen Poland Radoslaw Sikorski ya ce akwai buƙatar a inganta tsaron Ukraine a Turai.

  5. An damƙe wani mutum kan zargin daɓa wa abokinsa wuƙa har lahira a Ribas

    Ƴan sanda

    Asalin hoton, AFP

    Rundunar ƴan sanda a jihar Ribas ta ce ta kama wani mutum mai suna Michael kan zarginsa da ɗaba wa abokinsa Uchenna wuƙa har lahira, bayan da ya zarge shi da sata masa waya.

    An ruwaito cewa lamarin ya faru ne a titin Egede da ke mile 2 a jihar ta Ribas a ranar Laraba.

    Uchenna dai ya gamu da ajalinsa ne lokacin da ya kai wa abokina ziyara - wanda aka ce sun daɗe suna abota, kamar yadda wani shaida ya faɗa wa Jaridar Punch a Najeriya.

    Ya ƙara da cewa lokacin da Uchenna ya isa wajen Michael, sun daɗe suna hira - inda daga bisani abokin ya nemi wayansa ya rasa.

    "Daga nan ne Michael ya fara zargin abokinsa Uchenna da cewa ya sata masa waya, amma Uchenna ya musanta, inda nan da suka shiga musayar yawu," in ji shaidan .

    Ya ce jim kaɗan kawai Michael ya ɗauki ya daɓa wa abokin nasa a ciki.

    Bayan an garzaya da shi asibiti ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa - yayin da ƴan sanda suka cafke wanda ake zargi da aikata laifin.

    Rundunar ƴan sandan jihar ta Ribas ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin zuwa yanzu.

  6. An ɗage taron mahaddata Qur'ani da aka shirya yi a Abuja

    Taron mahaddata Qur'ani

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan da BBC ta samu sun nuna cewa an ɗage taron mahaddata al-Qur'ani da ake yi wa laƙabi da Qur'anic Convention a Turance da ya rage ƙasa da mako biyu a gudanar a Abuja, babban birnin Najeriya.

    An dai saka ranar Asabar 22 ga watan Fabrairu na 2025 da ranar da za a yi taron da ake sa ran zai samu mahalarta waɗanda mahaddata Qur'ani ne sama da dubu 60 daga ciki da wajen Najeriya.

    Wani ɗan kwamitin tsara taron wanda bai so a ambaci sunansa ba ya shaida wa BBC cewa "tun daren jiya Alhamis aka ɗage yin wannan taro.

    Sai dai kuma majiyar ba ta tabbatar wa da BBC haƙiƙanin dalilin da ya sa aka ɗage taro ba da kuma yaushe ne sabon lokacin da za a yi taron a nan gaba.

  7. Shugaban ƙungiyar Afenifere Ayo Adebanjo ya rasu

    Ayo Adebanjo

    Shugaban tsagin ƙungiyar Yarabawa ta Afenifere Chief Ayo Adebanjo ya rasu, yana da shekara 96.

    Adebanjo ya rasu ne a gidansa da ke Lekki, a jihar Legas.

    Iyalansa ne suka tabbatar da rasuwarsa a wata sanarwa da suka fitar yau Juma'a, 14 ga Fabrairun, 2025.

    Ɗan kishin ƙasar ya rasu ya bar matarsa mai shekara 94, Christy Ayo-Adebanjo da yara da kuma jikoki.

    "Za mu ci gaba da tunawa da irin gwagwarmaya da ya yi wajen faɗa a kan gaskiya da adalci. Ya tsaya da kuma jajircewa wajen ganin Najeriya ta samu cigaba," kamar yadda sanarwar iyalansa ta bayyana.

    An haifi Adebanjo ranar 10 ga Afrilun 1928 a wnai ƙauye kusa da Ijebu Ode da ke jihar Ogun.

    Ya kasance mai kishin ƙasa, ɗan siyasa kuma lauya a tsawon rayuwarsa.

  8. Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da filin jirgin sama a Kongo

    Kongo

    Asalin hoton, Reuters

    Ƴan tawayen M23 sun ƙwace iko da wani filin jirgin sama a garin Bukavu yayin da suke ci gaba da dannawa zuwa gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo.

    Rahotanni sun ce sun kuma ƙwato wasu garurua guda biyu.

    Dannawar da M23 ɗin ke yi na zuwa ne duk da kiran tsagaita wuta da kuma komawar tattaunawar samar da zaman lafiya da ƙasashe ke yi.

    Ɗaruruwan mutane aka ɗaiɗaita a makonnin baya-bayan nan sakamakon rikicin ƴan tawayen.

    A watan da ya gabata, M23 da ke samun goyon bayan Rwanda, suka ƙwace iko birnin Goma mai albarkatun ƙasa.

  9. 'Rasha za ta fuskanci takunkumi idan ba ta kawo karshen yaƙin Ukraine ba'

    JD Vance

    Asalin hoton, Reuters

    Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya gargadi Rasha cewar za ta iya fuskantar takunkumin tattalin arziƙi idan ta ƙi amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya da Ukraine.

    Jim kaɗan bayan isar sa birnin Munich don halartar taron tsaro, Mista Vance ya ce akwai yiwuwar amfani da ƙarfin soji.

    Shugabannin ƙasashen Turai da dama sun zargi Amurka da amfani da rarrashi wajen shawo kan Rasha.

    "Wani abu da shugaban Amurka da ni muka tabbatar shi ne Turai ƙawace mai muhimmanci ga Amurka, muhimmancin rawar da Jamus mai ƙarfin tattalin arziki za ta taka na daga acikin bututuwan da zamu duba," in ji mista Vance.

    A wani abu mai kama da martani ga ministan tsaron Jamus Boris Pistorius, ya ce nan gaba Turai na da ikon ɗaukar matakin soji ba tare da sahalewar Amurka ba.

  10. A guji barin Ukraine cikin tattaunawar kawo karshen yaƙi - Zelensky

    Shugaba Volodymyr Zelensky ya yi gargaɗin a guji barin Ukraine a baya cikin tattaunawar yadda za a kawo ƙarshen yaki a ƙasar.

    Da ya ke jawabi a taron Munich, ya nemi Turai ta goyi bayan ukraine don ta kare kanta.

    "Ina tunanin yana shirin yadda zai yaƙi ƙasashen ƙungiyar tsaro ta NATO a baɗi, to amma zamu hana shi," i ji Zelensky.

    A ranar Laraba Donald Trump ya yi wata doguwar tattaunawa da shugaban Rasha Vladmir Putin ta wayar tarho inda suka taɓo batun cimma zaman lafiya kai tsaye.

  11. Jami'ar UNIZIK ta kori ɗalibar da ta ci kwalar malami kan bidiyon TikTok

    Jami'ar UNIZIK

    Asalin hoton, Nnamdi Azikiwe University

    Hukumomin Jami'ar Nnamdi Azikiwe da ke, Awka a jihar Anambra ta kori ɗalibar nan, Goddy-Mbakwe Chimamaka Precious, saboda cakuma tare da cin kwalar wani malamin jami'ar.

    A cikin wani bidiyo da ya karaɗe shafukan sada zumunta an ga ɗalibar ta far wa malamin jami'ar, Dr Chukwudi Okoye, bayan ya ratsa ta cikin bidiyon da take ɗauka a wani lungu da ke harabar jami'ar.

    Cikin takardar korar da jami'ar ta fitar mai ɗauke da kwanan watan 13 ga watan Fabrairu, wadda magatakardar jami'ar, Victor I. Modebelu ya sanya wa hannu, ta ce an ɗauki matakin ne bayan shawarar kwamitin bincike da jami'ar ta kafa.

    ''Kwamitin ya samu ɗalibar da laifin saɓa wa dokokin ladabtarwa na jami'ar, musamman sashe na 4 na dokar ladabtarwa ta (SDR)'', in ji takardar korar, kamar yadda Jaridar Punch ta ruwaito.

    Bidiyon cakumar malamin ya ja hankalin mutane da dama a shafukan sada zumunta, inda aka yi ta kiraye-kirayen ɗaukar mataki.

    Jami'ar ta buƙaci ɗalibar ta gaggauta ficewa daga harabar makarantar tare da mayar wa jami'ar duk wasu abubuwan da ke hannun ɗalibar.

  12. Birtaniya ta ce za ta ci gaba da mara wa Ukraine baya

    Firaministan Birtaniya

    Asalin hoton, Reuters

    Firaministan Birtaniya, Sir Keir Starmer ya tabbatar wa shugaban ƙasar Ukraine, Volodymyr Zelenskyy cewa Birtaniya za ta ci gaba da bai wa Ukraine abin da ya kira da ''cikakken goyon baya'' tare da taimaka mata wajen cimma muradinta na zama mamba a ƙasashen ƙungiyar tsaro ta Nato.

    Mista Starmer bai fito ƙarara ya soki sabuwar manufar Amurka kan Ukraine ɗin ba, amma ya dage cewa duk wata tattaunawa kan makomar Ukraine na buƙatar sanya Ukraine ɗin a ciki.

    A jiya ne dai shugaban Amurka, Donald Trumo ya ce zai tattauna da takwaransa na Rasha Volodymyr Putin, don duba yadda za a kawo ƙarshen yaƙin Ukraine.

    Matakin dai bai wa wasu ƙasashen Turai daɗi ba, waɗanda ke ganin ya kamata a sanya Ukraine ɗin cikin tattauanwar.

  13. Harin gurneti ya raunata mutum huɗu a Afghanistan

    Motar ɗaukar marasa lafiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'ai a Afghanistan sun ce aƙalla mutum huɗu sun jikkata bayan harin gurneti a wani masallaci a lardin Samangan da ke arewacin ƙasar.

    Hukumomin ƙasar sun ce lamarin ya faru ne a lokacin sallar Juma'a a birnin Aybak.

    Ƴansanda sun kama mutum biyu da suke zargi da hannu a lamarin.

    Lamarin na zuwa ne a kwana guda bayan wani ɗan ƙunar baƙin wake ya kashe mutum guda tare da raunata wasu uku a cikin harabar ma'aikatar raya birane da ke birnin Kabul.

  14. Haɗarin babbar mota ya yi ajalin mutum 16 a Kano

    Motoa

    Asalin hoton, FRSC

    Wani hatsarin babbar mota da ya auku a birnin Kano ya yi ajalin mutum 16.

    Cikin wata sanarwar da jami'in hulɗa da jama'a na hukumar kiyaye aukuwar hadurra ta jihar Kano, Abdullahi Labaran ya fitar, ya ce hatsarin ya auku ne ranar Alhamis da daddare a kan babbar gadar Muhammadu Buhari da ke unguwar Hotoro.

    Abdullahi Labaran ya ce lamarin ya faru sakamakon gudu da direban motar ke yi, lamarin da ya sa ta ƙwace masa a daidai gadar.

    Ya ƙara da cewa hatsarin ya rutsa da mutum 71 da motar ke ɗauke da su yayin da mutum 52 suka samu raunuka, mutum 16 kuma suka mutu.

    Tuni aka kai waɗanda suka jikkata asibin Murtala da ke birnin na Kano domin ba su kulawar da ta dace.

    Hatsarin manyan motoci a kan titunan ƙasar na ƙara haifar da fargaba, inda a lokuta da dama idan motocin suka faɗi ake rasa rayuka da asarar dukiyoyi.

    Ko a farkon makon nan ma wata babbar mota ɗauke da dabbobi da faɗi a jihar Neja, da ke arewa ta tsakiyar ƙasar.

  15. Hamas ta bayyana sunayen Isra'ilawa uku da za ta saki gobe Asabar

    Alexander Troufanov da Yair Horn da kuma Sagui Dekel-Chen duk suna cikin mutanen da mayaƙan Hamas suka kwasa daga Isra'ila a ranar da suka kai samame

    Asalin hoton, Hostages and Missing Families Forum

    Bayanan hoto, Alexander Troufanov da Yair Horn da kuma Sagui Dekel-Chen duk suna cikin mutanen da mayaƙan Hamas suka kwasa daga Isra'ila a ranar da suka kai samame

    Hamas ta saki sunayen mutum uku da take garkuwa da su waɗanda za ta saki gobe Asabar domin yin musaya da Falasɗinawan da Isra'ila ke riƙe da su a wani ɓangare na ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin ɓangarorin biyu.

    Hakan na zuwa ne bayan kwanakin da aka kwashe ana fargabar wargajewar yarjejeniyar.

    Isra'ilawan da za a sakin su ne: Alexander Troufanov - ɗan Isra'ila mazaunin Rasha, da Yair Horn - ɗan Isra'ila mazaunin Argentina, da kuma Sagui Dekel-Chen - ɗan Isra'ila mazaunin Amurka.

    Isra'ila ta bayyana cewa za ta ci gaba da ruwan wuta a kan Gaza idan ba a saki mutanen a kan lokaci ba.

    Taƙaddama ta kaure ne bayan da Hamas ta yi barazanar dakatar da sakin mutanen na Isra'ila bayan zargin Isra'ilar da karya ƙa'idojin yarjejeniyar tsagaita wuta.

    Tun bayan fara aiki da yarjejeniyar tsagaita wutar a ranar 19 ga watan Janairu, Hamas ta saki Isra'ilawa 16, da ƴan ƙasar Thailand biyar yayin da ita kuma Isra'ila ta saki Falasɗinawa 566 da take riƙe da su a gidajen yarinta.

    Ana sa ran Hamas za ta saki ƴan Isra'ila 33 da take garkuwa da su a matakin farko na yarjejeniyar tsagaita wutar, yayin da ita kuma Isra'ila za ta saki Falasɗinawa 1,900.

    Yaƙi ya turnuƙe a Gaza ne tun bayan da Hamas ta kai wani hari kan Isra'ila a ranar 7 ga watan Oktoban 2023, inda mayaƙanta suka kashe kimanin mutum 1,200 tare da yin garkuwa da wasu mutum 251.

    Tun bayan wancan lokacin, ma'aikatar lafiya ta Hamas ta ce an kashe sama da mutum 48,230 sanadiyyar luguden wuta da Isra'ila ta riƙa yi a Gaza.

  16. Magoya bayan Arsenal na kokawa kan raunukan ƴan wasan gaban ƙungiyar

    Ƴan wasan Arsenal

    Asalin hoton, Getty Images

    Magoya bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal sun fara bayyana damuwarsu kan raunukan da ƴan wasan gaban ƙungiyar ke fama da su.

    A baya-bayan nan be dai ƙungiyar ta sanar da raunin ɗan wasanta, Kai Havertz - wanda zai yi jinya har ƙarshen kaka.

    Lamarin na zuwa ne a daidai lokacin da Bukayo Saka da Gabriel Jesus, da Gabriel Martinelli ke ci gaba da jinya.

    Wani da da magoya bayan Arsenal ke kallo a matsayin wat mummunar ƙaddara da ta auka wa ƙungiyar.

    Alhaji Yaman mai Arsenal a Najeriya ya ce a yanzu haka kungiyar na cikin garari sakamakon jinyar da ƴanwasan ke yi.

    ''Abin taƙaicin shekararmu fiye da 20 ba mu ɗauki kofin Premier ba, amma kuma gashi banan ma da muke fatan hakan, fatan namu na neman gamuwa da cikas'', a cewarsa.

  17. Isra'ila na jiran sunayen mutanenta da Hamas za ta saki gobe

    za a saki sunayen

    Asalin hoton, Getty Images

    Isra'ila na sa ran Hamas ta bayyana sunayen ƴan ƙasarta uku da ƙungiyar za ta saki ranar Asabar cikin waɗanda take garkuwa da su

    Tun da farko ƙungiyar ta ce za ta ɗage sakin Isra'ilawan, bayan da ta yi iƙirarin cewa Isra'ila ta saɓa wa sharuɗan yarjejeniyar.

    To sai dai bayan shiga tsakani da aka yi a Masar, tare da barazanar komawa yaƙi da Isra'ila ta yi, idan ba a ci gaba da aiwatar da yarjejeniyar ba, Hamas ta amince ta ci gaba da sakin Isra'ilawan da take garkuwa da su.

    Ƙungiyar agaji ta Red Cross - wadda ke shiga tsakani a musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas - ta ce ta damu da halin lafiyar Isr'ilawan da Hamas ke garkuwa da su

  18. Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kafa rundunar 'tsaron layukan wutar lantarki'

    Lantarki

    Asalin hoton, TCN

    Gwamnatin Najeriya ta ce za ta kafa wata runduna ta musamman domin kare layuka da cibiyoyin samar da wutar lantarkin ƙasar daga ɓat-gari masu sace kayyakin wutar.

    Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka ranar Juma'a a wata hira da gidan talbijin na Channels da ke ƙasar.

    Mista Tunji-Ojo ya ce sun ɗauki mataki tare da takwaransa na wutar lantarki, domin saman da abin da ya kira ''dakarun tsaron lantarki'' na ƙasa.

    Ya ƙara da cewa za a samar da dakarun ne daga rundunar tsaron fararen hula ta Civil Defence, kuma za a ɗora musu alhakin dakatar da lalata abubuwan lantarkin, lamarin da ke haifar da katsewar wutar a wasu lokuta a faɗin ƙasar.

    A baya-bayan nan dai ƙasar na yawan fama da katsewar lantarkin, sakamakon abin da hukumomin ƙasar suka ce sace wasu wayoyin da ɓata-gari suke yi ne ke haifarwa.

    Ministan cikin gidan ya ce lokaci yayi da ya kamata a ɗauki matakin bai ɗaya domin magance matsalar.

  19. Ku San Malamanku tare da Farfesa Yahuza Abdullahi Muhammad

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyo

    A wannan makon za mu kawo muku Sheikh Farfesa Yahuza Abdullahi Muhammad a filinmu na Ku San Malamanku wanda malami ne a birnin Maiduguri.

    Farfesa Yahuza ya halarci makarantar harshen larabci da addinin Musulunci a unguwar Agege da ke jihar Legas.

    Malamin ya samu gurbin ƙaro karatu a ƙasar Syria inda daga baya ya koma ƙasar Libya domin samun shaidar karatun digiri.

    Ya koyar a sashen koyar da Larabci na Jami'ar Maiduguri a jihar Borno, inda kuma har yanzu a can yake koyarwa.

    Shehun malamin ya yi karatun zaure da na zamani inda ya samu ilimi a wurin malamai da dama.

    Farfesa ya ƙware a fannin harshen Larabci da fassara da kuma ilimin rabon gado.

  20. Amurka da Rasha sun yi musayar fursunoni tsakaninsu

    Wasu fursunonin da aka yi musaya

    Asalin hoton, Getty Images

    Amurka ta saki wani ɗan Rasha da aka samu da laifin zambar kuɗaɗe, a wani ɓangare na musayar fursunoni tsakanin ƙasashen biyu.

    Alexander Vinnik na gudanar da wani kamfanin musayar kuɗaɗen kirifto, wanda masu shigar da ƙara a Amurka suka ce na ɗaya daga cikin manyan masu taimaka wa masu laifi a faɗin duniya wajen turawa da kuma ajiye kuɗaɗe.

    A shekarar 2017 ne hukumomin Amurka suka kama shi kan zarge-zarge 21 masu alaƙa da zamba, inda a watan Mayun shekarar da ta gabata ya amsa laifukan da ke tuhumarsa da su, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 20.

    An mayar da shi Rasha, inda ita ma ta saki wani Ba'amurke mai suna Marc Fogel - da aka samu da laifin mallakar wata tabar wiwi ta magani da likita ne kawai ke rubuta wa mutum ita.

    Fadar White House ta yaba da matakin musayar fursunonin, inda ta ce hakan ya nuna alaƙar kyautatuwar diplomasiyya tsakanin manyan ƙasashen biyu.