Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2024

Wannan shafi da ke kawo muku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 29/12/2024

Taƙaitattu

Rahoto kai-tsaye

Abdullahi Bello Diginza da Ahmad Bawage

  1. Al'ummar Chadi za su gudanar da zaɓen majalisar dokoki

    Al'ummar ƙasar Chadi za su zaɓi 'yan majalisar dokoki a ƙasar a yau Lahadi, duk kuwa da zarge-zargen maguɗin zaɓen daga ɓagarori daban-daban.

    Shugaban mulkin soji, Mahamat Idriss Deby ya ce zaɓen wani ɓangare ne na kawo ƙarshen wa'adin shirin mika mulki na shekara uku da aka yi bayan rasuwar mahaifinsa -- tsohon shugaban ƙasar.

    'Yan adawa sun yi kira ga al'ummar ƙasar su ƙaurace wa zaɓen, bayan da suka yi zargin cewa Mista Deby na da niyyar yin amfani da zaɓen don ƙarfafa ikonsa.

    A nata ɓangare gwamnatin ƙasar ta ce 'yan adawa na ƙoƙarin daƙile tsarin dimokradiyya ne.

  2. Marabanku

    Masu binmu a wannan shafi, kamar kullum muna yi muku barka da hutun ƙarshen mako.

    Abdullahi Bello Diginza ke fatan kasancewa da ku, domin zagayawa da ku faɗin duniya don sanin halin da take ciki.

    Ku ci gaba da kasancewa da shafin namu