Satar mutane bakwai da suka ja hankalin ƴan Najeriya a 2024

    • Marubuci, Nabeela Mukhtar Uba
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 4

Sace-sacen al'umma na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan ƙalubalen da harkar tsaro ke fuskanta a Najeriya - ƙasa mafiya ƙarfin tattalin arziki da yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Ko a baya-bayan nan hukumar ƙididdiga ta Najeriya, NBS ta fitar da alƙaluman mutanen da aka sace a Najeriya a tsukin shekarar 2024 da suka kai sama da miliyan biyu inda yankin arewa maso yammacin ƙasar ya zama inda aka fi sace mutane da yawansu ya kai fiye da miliyan ɗaya sai kuma kudu maso gabashin ƙasar da yawan mutanen da aka sace a yankin suka kai sama da dubu 110.

Daga cikin irin sace-sacen da aka yi a 2024 da muke yi wa bankwana, BBC ta rairayo guda bakwai.

Ɗaliban Kuriga

A farkon watan Maris ne aka tashi da labarin sace ɗaliban makaranta 280 a garin Kuriga da ke ƙaramar hukumar Chikun a jihar Kaduna.

Sa dai a lokacin da hukumomi suka sanar da kuɓutar da yaran, sun ce sun yi nasarar ƙwato mutum 137 saɓanin adadin da mahukuntan makarantar suka sanar a lokacin da lamarin ya faru.

Sannan ɗaya daga cikin malaman makarantar da aka sace su tare da ɗaliban, ya rasu a hannun masu garkuwar.

Ɗaliban sun shafe kwana 17 a hannun masu garkuwa kafin hukumomi su kuɓutar da su ƴan kwanaki kafin cikar wa'adin biyan kuɗin fansa da masu garkuwar suka bayar.

Satar ɗaliban a lokacin ya sake tunowa da mutane batun ƴan matan Chibok da ƙungiyar Boko Haram ta sace a makarantarsu da ke jihar Borno cikin shekarar 2014.

Sarkin Gobir

Sace marigayi Sarkin Gobir na Gatawa Isa Bawa na ɗaya daga cikin sace-sacen da aka yi cikin 2024 da ya jefa al'umma cikin jimami.

Kwana uku bayan sace shi, ƴanbindigar sun fitar da wani bidiyo inda aka ga marigayin yana neman da a kai masa ɗauki domin kuɓutar da shi.

Sai dai bayan kwanaki 25 da kasancewa a hannun masu garkuwar ne kuma aka samu labarin mutuwarsa.

Duk da cewa ƴanbindiga sun kwashe shekaru suna kashe-kashe a yankin na arewacin Najeriya, amma ba kasafai ake samun irin haka ba.

Mutuwar Sarkin ta ƙara fito da matsalar taɓarɓarewar tsaro a Najeriya.

Mahaifiyar mawaƙi Rarara

A cikin watan Yuni ne ƴanbindiga suka yi garkuwa da Hajiya Hauwa'u Adamu, mahaifiyar fitaccen mawaƙin Hausa, Dauda Kahutu Rarara.

Katsina na daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ke fuskantar matsalar tsaro, inda ƴanbindiga ke kashewa tare da yin garkuwa da mutane.

Ƴansandaa, a lokacin sun ce sun kama mutum biyu bisa zargin hannu a sace mahaifiyar ta Rarara.

Sai dai bayan shafe mako uku a hannun ƴanbindigar ne Hajiya Hauwa'u ta samu kuɓuta.

Sace ƴanmata ƴangida ɗaya a Bwari

Sace ƴanmatan shi ne garkuwar farko da aka gani a 2024 inda ƴanbindiga, a ranar 2 ga watan Janairu, suka auka gidan su Nabeeha suka sace ta tare da mahaifinta da ƴan'uwanta mata biyar.

Bayanai sun nuna cewa daga bisani ƴan bindigar sun sako mahaifin, amma suka nemi a biya kuɗin fansa a kan ƴan matan shida.

Sai dai lamarin ya kai ga mutuwar Nabeeha, wadda ƴan bindigar suka kashe.

Batun sace ƴan matan da kisan Nabeeha, batu ne da ya ja hankali a Najeriya, musamman a dandalin sada zumunta.

Bayan kimanin makonni biyu da aukuwar lamarin ne hukumomin tsaro suka bayyana cewa sun samu ceto ragowar ƴanmatan bayan samamen da jami'an tsaro suka kai a kusa da dajin kajuru da ke Kaduna.

Ƴan rakiyar amarya a Katsina

A cikin watan Fabarairu ne kuma ƴanbindiga suka sace aƙalla mata 53 da suka kasance ƴan rakiyar amarya a jihar Katsina.

Bayanan ƴansanda sun nuna cewa masu garkuwar sun yi wa mutanen ƙofar rago yayin da suke hanyarsu ta dawowa daga wani biki a ƙaramar hukumar Sabuwa.

Mako ɗaya bayan sace su ne kuma ƴanbindigar suka fitar da wani bidiyo mai tsawon minti 2:20 da ya nuna ɗanbindiga sanye da kayan sojoji riƙe da bindiga.

Sun nuna matan sanye da hijabi a tsaye cikin surƙuƙin daji. Cikin matan, akwai guda biyu masu riƙe da jariri.

An kuma ga amaryar sanye da kakin soji da bindiga a wuyanta sai wani mutum wanda bisa jawaban ƴanbindigar ke nuna shi ne direban motar da wata mata dukkansu rataye da bindiga a wuya.

Gwamnatin Katsina dai a lokacin ta bayyana bidiyon a matsayin farfaganda da wani salo na nuna ikonsu da ƙalubalantar hukumomi kan yaƙarsu da ake yi.

Sojoji sun kuɓutar da su tare da miƙa su hannun gwamnatin jihar Katsina.

Sace mutum 50 a Maradun

A dai 2024 mai ƙarewa ce masu garkuwa suka sace sama da mutum 50 a ƙaramar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.

Bayanai sun ce maharan ɗauke da muggan makamai sun shiga garin cikin dare lamarin da ya sa wasu da suka farga suka tsere.

Wasu mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa maharan sun sace aƙalla mutum 50 zuwa 55, waɗanda mafi yawansu mata ne da ƙananan yara.

Har zuwa lokacin haɗa wannan maƙala babu labarin kuɓuto su daga hukumomin tsaro.

Ɗalibai masu karatun likita

A cikin watan Agusta ne aka wayi gari da labarin sace wasu ɗalibai masu karatun likita kimanin 20 a hanyarau ta zuwa wani taro.

An sace su ne a jihar Benue da ke yankin arewa ta tsakiya.

Sai dai bayan shafe yan kwanaki a hannun masu garkuwar ne kuma tawagar jami’an tsaro suka ceto su.